Ahlulbait (a.s) Cikin Alkur'ani Mai Girma

Alkur'ani mai girma shi ne tushen dukkan tunani, shi ne mabubbugar shari'a da ka'idoji. Duk abin da Alkur'-ani ya zo da shi wahayi ne abin saukarwa, kuma magana ce tsarkakkiya daga Allah, yana furuci da tsarin rayuwa yana kuma ayyana dokokin rayuwar. Duk wani musulmi ya san cewa abin da Alkur'ani ya zo da shi shi ne shari'a da sakon da zai bi a rayuwarsa, sannan kuma an wajabta masa aiki da shi da yin tafiya bisa shiriyarsa. Abin lura kuma shi ne Alkur'anin nan ya yi magana a kanAhlulbaiti (a.s) da yanayi da tsari kamar haka:

  1. Amfani da sunansu na isdilahi wanda shi Alkur'-anin ya sanya musu. Wani lokaci yakan ambace su da Ahlulbaiti kamar yadda ya zo cikin Ayar Tsarkakewa, wani lokaci kuma yana ambatonsu da al-Kurba kamar yadda ya zo cikin ayat al-Muwadda (ayar kauna). Ayoyi masu yawa sun sauka da wadannan ma'anoni sannan Sunna ta yi bayaninsu ga al'umma a lokacin da ayoyin suke sauka daga bisani kuma masu fassara da masu ruwaya suka nakalto bayanin cikin littattafansu manya da kanana.
  2. Kiyaye da kuma rubuta dukkan ababen da suka kebanta ga Ahlulbaiti (a.s) bugu da kari kan saukan ayoyi da dama da suke ambaton falalar Ahlulbaiti (a.s), matsayinsu, yabo da fuskantar da al'umma zuwa gare su; wani zubin a ambaci darajojin a hade, kamar yadda ya zo cikin Ayar Mubahala (Surar Ali Imrana, 3: 61) da Ayar Ciyarwa cikin Surar Dahri da sauransu. Wani zubin kuwa

a rarrabe kamar yadda ya zo cikin Ayar Wilaya (Surar Ma'ida, 5: 55).

Bari mu bijiro da sashen wadannan ayoyi - suna kuwa da yawa - wadanda suka yi magana a kan Ahlulbaiti (a.s), domin bayani a kan falalarsu da matsayinsu, gami da kuma sharhi:

Ta Farko:Ayar Tsarkakewa

"...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa". (Surar Ahzabi, 33:33)

Hakika tafsirai da ruwayoyi sun hadu a kan cewa abin da ake nufi da Ahlulbaiti shi ne mutanen gidan Annabi (s.a.w.a) wadanda kuma su ne, Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.). Bayani ya zo cikin littafin Durrul Mansur na Imam As-Suyudi cewa: (Al-Dabarani ya fitar da hadisi daga Ummu Salma cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce da Nana Fadimatu cewa: "Taho min da mijinki da 'ya'yansa biyu", sai ta taho da su sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya lullube su da wani mayafi, sa'an nan ya sanya hannunsa bisansu ya ce:

"Ya Allah! Wadannan su ne Ahlulbaitin Muhammadu (a wani lafazin zuriyar Muhammadu) to Ka sanya tsirarKa da albarkarKa wa zuriyar Muhammadu kamar yadda Ka sanya wa zuriyar Ibrahima, lalle Kai ne Abin godiya, Mai girma".

Sai Ummu Salma ta ce: "Sai na daga mayafin domin in shiga in kasance tare da su, sai Annabi (s.a.w.a) ya janye shi daga hannuna ya ce: "Lallai ke kina tare da wani alheri "[1].

An ruwaito hadisi daga Ummu Salma, matar Annabi (s.a.w.a) cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance a dakinta bisa wurin kwanciyarsa yana rufe da wani mayafi sakar Khaibara, sai Fadima ta zo da wata tukunya da abinci a cikinta. Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ki kira mijinki da 'ya'yansa Hasan da Husaini". Sai ta kira su. Yayin da suke cin abincin sai aya ta sauko wa Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa:

"Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkake-ku tsarkakewa"

Sai Annabi (s.a.w.a) ya kama gefen ragowar sashen mayafinsa ya rufe su da shi, sannan ya fitar da hannunsa daga mayafin ya nuna sama ya ce:

"Ya Allah! Wadannan su ne mutanen gidana, make-bantana, to Ka tafiyar da kazamta daga gare su kuma Ka tsarkake su, tsarkakewa".

Ya fadi hakan har sau uku. Ummu Salma ta ce: "sai na shigar da kaina cikin mayafin na ce: "Ina tare da ku Ya Manzon Allah? Sai ya ce: "ke kina tare da wani alheri", ya fadi hakan har sau biyu[2].

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ci gaba da bayyana wa al'ummarsa ma'anar wannan aya mai girma, yana tsarkake fahimtarta ga wannan aya domin al'umma ta haskaka da ita ta kuma rayu a kanshiryuwarta. An ruwaito shi yana cewa:

"Wannan aya ta sauka ne a kan mutane biyar: Ni kaina, Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini."Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa [3]"

Kamar yadda kuma aka ruwaito daga Ummul Muminina A'isha, tafsirin ayar da bayanin mutanen da ake nufi a ciki, kamar haka: (Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fito wata safiya yana sanye da wani mayafi mai zane, wanda aka yi da bakin gashi, sai Hasan dan Ali ya zo, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya shigar da shi (cikin mayafin), sannan sai Husaini ya zo, ya shigar da shi, sannan Ali ya zo ya shigar da shi, sa'an nan sai ya ce:

"Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa[4] ".

A wata ruwayar kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana wucewa ta kofar Fadima (a.s.) yayin da ya fito sallar asuba yana cewa:

"Salla! Ya mutanen babban gida (Ahlulbaiti), salla! "Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa "[5].

Hakan nan Alkur'ani yake magana a kanAhlulbaiti (a.s) yana iyakance mutanen da suke ciki, tsarkaka manisanta daga dukkan dauda da sabo da zunubi da kuma son zuciya. Saboda haka halayen su abin koyi ne haka nan su kansu. Alkur'ani bai sanar mana da su irin wannan sanarwa ba, sai domin ya jaddada matsayi da mukaminsu ga al'umma, ya kuma ja hankulanmu zuwa ga koyi da su da komawa gare su domin fahimtar shari'a da karbar hukumce-hukumcenta daga wurinsu. Ta wannan hanyar, Alkur'ani ya ayyana mana mizani na aikace (wato ayyukan Ahlulbaiti) da ma'aunin da za mu koma gare shi yayin da ra'ayoyi suka sassaba, aka kuma sami bambancin fahimta da I'itikadi (wato abin da mutum ya yarda da shi).

Wannan kuwa a sarari yake idan muka duba yadda Alkur'ani ya jaddada cikin ayoyi da yawa ya kuma bijiro da Ahlulbaiti (a.s) a matsayin ja-gorori ga al'umman musulmi bayan Manzon Allah (s.a.w.a.).

Dogewar da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi, wata da watanni bisa tsayuwa a bakin kofar Aliyu da Fadima (a.s.) yana kiransu da asuba zuwa salla, yana kiransu da Ahlulbaiti ba kome ba ne face sanar da al'umma mutanen da ake nufi da Ahlulbaiti, kana kuma yana fassara wa musulmi ayar tsarkakewa, yana sanar da su matsayin Ahlulbaiti (a.s) tare da jan hankulansu zuwa gare su da kuma wajabta musu kaunarsu da yi musu biyayya da jibinta al'amari gare su.

Dabarani ya ruwaito daga Abu Hamra' cewa:

"Na ga Manzon Allah (s.a.w.a.) yana zuwa kofar Aliyu da Fadima tsawon wata shida yana cewa: "Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa[6] ".

Fakhru al-Razi ya ambata a cikin tafsirinsa, Tafsir al Kabir, cewa bayan saukar ayar: "Kuma ka umurci iyalanka da salla, kuma ka yi hakuri a kanta", (Surar Daha, 20: 132), Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kan je (kofar) Aliyu da Fadima kowace safiya yana mai cewa: (lokacin) salla (ya yi), ya aikata hakan har na tsawon watanni.

Sannan kuma ya kawo hadisin Hammad bn Salma, daga Aliyu bn Zaid daga Anas cewa: "Annabi (s.a.w.a) ya kasance yana wucewa ta dakin Fadima koyaushe ya fito zuwa ga salla har na tsawon wata shida, yana mai cewa:

"Salla! Ahlulbaiti! "Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa[7] ". A cikin wannan akwai bayani da kuma nuni zuwa ga muhimmancin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya riki Ahlulbaiti (a.s) da shi, da kuma karfafawarsa wa musulmi cewa su (Aliyu, Fadima da 'ya'yansu) su ne mutanen gidansa (Ahlulbaiti), wadanda Allah Ya tafiyar da dukkan dauda ga barinsu, Ya kuma tsarkake su tsarkakewa. Wannan muhimmancin an nuna shi ne bayan Allah Ya yi magana da ManzonSa cewa: "...kuma ka umurci iyalanka da salla, kuma ka yi hakuri a kanta".

Sannan a sarari yake cewa daga abin da ayar:

"Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa",

take nuni da shi da kuma amfani da lafazin maza ba lafazin mata ba da aka yi, wato ()da kuma(), akwai nuni zuwa ga wadanda ake nufi, su ne wadannan mutane biyar din. Bayani ya zo a cikin Tafsirai cewa da Allah Yana nufin matan Annabi (s.a.w.) ne da Yayi amfani da kalmar() da ta () da magana irin wacce ake yi wa mata.

A baya mun riga da mun ga Hadisin Mayafi lokacin da aka saukar da wannan aya ta tsarkakewa yayin da Ummu Salama taso shiga cikin wannan mayafi amma Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce mata ke dai kina a matsayinka, kuma kina a kanalheri.

Hakan yana nuna mana rashin shigar matayen Annabi (s.a.w.a) cikin wannan aya ta tsarkakewa, kana kuma babu daya daga cikinsu da ta yi ikirarin saukar wannan aya a kansu, duk kuwa da cewa ayar ta falaloli da kuma matsayi mai girma ce.

Wannan ayar ta fitar da wata hanya wacce abin da take nuni da shi da abin da ta tattara suna da yalwar gaske. Tana jan hankulanmu zuwa ga batutuwa na asasi a


rayuwar Musulunci domin kada mu sami rikitarwar fahimta balle ma manufofin Littafin Allah na gaskiya su tawaya. Allah Ya yi nufin gina al'umma bisa ginshikin tsarki da nisantar dauda da abin kunya sai Ya sanya Ahlulbaiti (a.s) a matsayin wani tushe abin dogara da kuma haske mai haskakawa. Lalle babu wani mutum da Alkur'ani mai girma ya siffanta shi da wannan siffa daga cikin musulmi, babu kuma wanda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya siffanta shi da wannan siffar (siffar tsarki maras iyaka) face Ahlulbaiti (a.s).

Ta Biyu: Ayar Soyayya

"Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta. Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, za Mu kara masa kyau a cikinsa, lallae Allah Mai gafara ne, Mai godiya". (Surar Shura, 42:23)

Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya bayyana ko wane ne ake nufi da wannan aya mai albarka, kuma ko su waye kaunarsu da biyayya gare su da rayuwa bisa tafarkinsu ya wajabta ga musulmi. Malaman tafsiri da hadisi da tarihi sun ruwaito cewa "Makusantar Annabi" wadanda ake nufi a wannan ayar su ne Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.).

Zamakhshari ya fada a cikin tafsirinsa al-Kashshaf cewa: "An ruwaito cewa mushrikai sun taru a wurin taronsu sai sashinsu ya ce wa sashi: "shin kuna ganin Muhammadu zai nemi wani lada a kan abin da yake kira gare shi? Sai aya ta sauka cewa: "Ka ce: "Ba ni tambaya


ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta[8] ".

Sai Zamakhshari ya ce: "Kuma an ruwaito cewa yayin da wannan aya ta sauka sahabbai sun tambayi Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya Manzon Allah su waye danginka wadanda sonsu ya wajabta a kanmu". Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu".

A cikin Musnad na Imam Ahmad bin Hambal - da isnadinsa ambatacce -, daga Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas (r.a.) ya ce: "Yayin da zance Allah Ta'ala cewa: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta", ya sauka, sai mutane suka tambayi Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya Rasulallah! Su waye danginka wadanda sonsu ya wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'yayansu biyu[9]".

Fakhrurrazi ya tabbatar da wannan zancen cikin Tafsirul Kabir bayan ya ambaci maganar Zamakhshari dangane da Alu Muhammad (dangin Muhammadu). Ga abin da yake cewa:

"Ni ina cewa dangin Muhammadu su ne wadanda al'amuransu suke tare da na shi (Annabi), to kuma duk wadanda kusancinsu yafi kusa da shi da kuma cika, to su ne aalu (dangin Annabi). Babu shakka cewa Fadima da Ali da Hasan da Husaini suna da mafi tsananin alaka da Manzon Allah (s.a.w.a.), wannan kuwa an nakalto ta hanyoyi daban. A saboda haka ya wajaba su kasance su ne Aalu".

Har ila yau an sassaba a kanma'anar aalu, wasu sun ce su ne danginsa, wasu kuma sun ce su ne al'ummarsa. To idan mun dauke shi da ma'anar dangi, to su din dai su ne aalu din, idan kuma muka dauke shi da ma'anar al'umma[10]wadanda suka karbi kiransa to nan ma dai su ne aalu din. Don haka a bisa dukkan yanayi dai su aalu din ne dai.

To amma shigar waninsu cikin kalmar aal, a nan kan an samu sabani kan hakan. Marubucin al-Kashshaf ya ruwaito cewa yayin da wannan aya ta sauka, mutane sun ce: "Ya Manzon Allah su waye danginka wadanda kaunarsu ta wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu, Fadima da 'ya'yansu biyu", sai ya tabbatar da cewa wadannan hudun su ne dangin Annabi (s.a.w.a), to idan kuwa hakan ya tabbata to ya wajaba su zama abin kebancewa da karin girmamawa. Ana iya tabbatar da hakan ta fuskoki kamar haka:

  1. Fadin Allah (S.W.T) cewa: "face dai soyayya ga makusanta", kuma fuskar kafa hujja da ayar ya gabata.
  2. Babu shakka cewa Annabi (s.a.w.a) ya kasance yana kaunar Fadima. An ruwaito shi yana cewa:

"Fadima yanki ne daga gare ni, abin da yake cutar da ita yana cutar da ni ".

Kamar yadda ingantaccen hadisi ya tabbatar cewa Annabi Muhammadu (s.a.w.a) ya kasance yana kaunar Aliyu, Hasan da Husaini (a.s.). To idan wannan ya tabbata, lallai kaunarsu ta zama wajibi a kan dukkan al'umma domin fadin Allah (S.W.T.) cewa:

"Ka ce: Idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, Allah Ya so ku...". (Surar Ali Imrana, 3:31)

"...ku bi shi, don ku shiryu". (Surar A'arafi, 7: 158)

Da kuma fadinSa cewa:

"...to, wadanda suke sabawa umurninSa, su kiyayi abkuwar wata fitina....". (Surar Nur, 24: 63)

"Lalle abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah...." (Surar Ahzabi, 33: 21)

  1. Addu'a ga dangin Manzo tana da wani matsayi mai girma, domin haka ne aka sanya wannan addu'ar ta zama cikamakin tahiya a cikin salla, wato: "Ya Allah! Ka yi tsira ga Muhammadu da Alayen Muhammadu, kuma Ka yi jin kai ga Muhammadu da Alayen Muhammadu".

Ba a samun wannan girmamawa ga wani wanda ba su dangin ba. To duk wannan yana nuni da cewa kaunar alayen Muhammadu wajiba ce.

Imam Shafi'i yana cewa:

Ya kai mahayi tsaya a wannan kwari na Mina,

   Ka kira mazaunin al-Nahidhi.

Da daddare yayin da alhazai suka wuce zuwa Mina,

          Tamkar kogin Furatu mai yalwa da yawan ruwa.

Idan Rafdhu[11] shi ne son Zuriyar Muhammadu,

     To mutane da aljannu su shaida ni Rafidhi ne[12] .

Ibn Munzir da ibn Abi Hatam da ibn Mardawihi da Dabarani cikin Mu'ujamul Kabir daga Ibn Abbas sun ce: "Yayin da ayar: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta", ta sauka sai mutane suka ce: "Ya Manzon Allah su wane ne makusantanka wadanda kaunarsu ta wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu [13]".

A cikin Mu'ujam din dai ya inganta daga Imam Hasan dan Ali (a.s.) cewa wata rana yayin da yake huduba wa mutane ya ce:

"Ni ina daga cikin Ahlulbaitin da Allah Ya farlanta kaunarsu a kan kowane musulmi, inda Ya ce: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta".

(Ibn Abi Hatam ya fitar daga Ibn Abbas cewa: (lokacin da aka karanta wannan aya): (. ) "kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau) (Surar Shura, 42: 23), sai ya ce: "(hakan) shi ne kaunar Ahlulbaiti[14] ".

Alkur'ani mai girma ya tabbatar da tsarkin Ahlulbaiti (a.s) da ayar tsarkakewa kuma ya fahimtar da al'umma matsayinsu da rawar da suka taka dangane da daukaka sakon Musulunci a cikin rayuwar al'umma. Da wannan ne kuma suka cancanci soyayya da riko zuciya daya wanda Alkur'ani ya yi umurni da shi a wannan ayar.

Abin da Alkur'ani yake nufi da wannan soyayya ba wai bege da doki da soyayya ta zuci kawai ba ne, domin babu wata fa'ida ga soyayya da kaunar da take cikin rai da zuciya, amma ba ta da wata bayyana a waje (a fili). Lallai tabbatar kauna da soyayya ga makusantan Manzon Allah (s.a.w.a.) yana samuwa wajen koyi da su da kuma rayuwa bisa turbarsu da lizimtar mazhabarsu da abin da ya fito daga gare su, da kuma daukar matsayinsu a al'umma matsayin shugaba kuma ja-gora.

Yayin da Alkur'ani yake sanya wannan ayar a bisa harshen Manzon Allah (s.a.w.a.) kuma Yake umurtansa da cewa ya sanar da al'ummarsa da mutane bai daya cewa ba ya nufin samun wani lada ko sakayya daga gare su domin isar da sako da jure wahalhalun kira zuwa ga Allah da kuma shiryar da su, face soyayya ga makusantansa (s.a.w.a) da tsarkake zuciya gare su da rayuwa bisa tafarkinsu, abin da kurum Alkur'ani yake nufi shi ne kiyaye tafarkin al'umma da tsare hanyarta ta akida da shari'a, domin al'umma ta fuskanci Ahlulbaiti bayan da Alkur'ani ya fuskantar da ita zuwa gare su.

Ba don lamuncewar da ake samu daga Ahlulbaiti (a.s) ba, da kuma ikon ja-gorancin al'umma a kan hanyar shiriya da lamunce hakan ba, da Alkur'ani bai saukar da soyayyar ba, kuma da ba a umurci Manzon Allah (s.a.w.a.) da ya sanya hakkinsa (ladansa) a kan al'umma shi ne kaunar Ahlulbaiti (a.s) ba.

Wannan tarin bayanai da muka kawo na maganganun malaman tafsiri da hadisi sun nakalto mana fassarar da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi wa wannan aya mai albarka, da sanya kaunar Ahlulbaiti (a.s) cikin zukata kuma ya sanya kaunar ta hakika ce mai tabbata cikin zuciyar ko wane musulmi, tana bayyana a cikin halayensa, tunaninsa da kuma begensa. Soyayyar nan tana kuma ayyana matsayarsa a kanAhlulbaiti (a.s) da makiyansu da masoyansu da kuma bin tafarki da kuma abin da ya tabbata daga gare su na hadisi, fikihu, tafsiri, tunani, akida, shari'a da kuma tsarin aiki na jagoranci da siyasa.

Wannan lambar girma da daukaka tana da manufa da abin da take nuni da shi a kebance, wanda ya kamata musulmi su kiyaye shi kuma su riski zurfinsa.

Ta Uku: Ayar Mubahala

"To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirayi 'ya'yanmu da 'ya'yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku, sa'an nan kuma mu kankantar da kai,

sa'an nan kuma mu sanya la'anar Allah a kan makaryata". (Surar Ali Imrana, 3: 61)

Wani abu mai madauwamin tarihi wanda malaman tarihi da tafsiri sun ruwaito shi ya auku, wanda kuma yake nunawa al'umma irin girma da daukakan Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a.), su ne kuwa: Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.) a wajen Allah (S.W.T.) da kuma matsayinsu a cikin wannan al'umma.

Wannan abin kuwa kamar yadda su malaman tafsiri da tarihin suka kawo shi ne cewa wata tawaga[15] ta kiristocin Najran ta zo domin ta yi jayayya da Manzon Allah (s.a.w.a.) don a gane waye yake kan gaskiya. Nan take sai Allah Ya umurce shi cikin wannan aya mai albarka da ya kira Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.) ya fita da su zuwa wani kwazazzabo, ya kuma kira Kiristocin da 'ya'yansu da matansu su fito sannan a yi addu'ar Allah Ya saukar da azaba kanmakaryata.

Zamakhshari a cikin Al-Kashshaf yana cewa:

"Yayin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kiraye su zuwa ga Mubahala[16] , sai suka ce: sai mun koma mun yi nazari. Da suka kebanta sai suka ce wa shugabansu; "Ya Abdul Masih! Me ka ke gani? Sai ya ce: "Wallahi, Ya ku jama'ar Nasara, kun sani cewa Muhammadu Annabi ne wanda aka aiko shi kuma hakika ya zo muku da bayani mai rarrabewa game da al'amarin sahibinku. Wallahi babu wata al'umma da ta taba yin mubahala da wani Annabi face babbansu ya halaka, karaminsu kuma ya gagara girma, to idan ko kun aikata hakan to lallai za mu halaka. Idan kun zabi riko da adddininku da zama bisa abin da kuke kansa to ku yi bankwana da mutumin na ku koma garinku.

Ko da gari ya waye sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fito yana mai sammako, yana rungume da Husaini (a.s.) yana rike da hannun Imam Hasan (a.s.), Fadima (a.s.) kuwa tana biye da shi sannan shi kuma Aliyu (a.s.) yana bayanta, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce musu: "Idan na yi addu'a ku ce amin".

Ko da Kiristocin nan suka hango Manzon Allah (s.a.w.a.) yana zuwa da tasa tawagar, sai wannan Fadan da ke cikinsu ya ce musu: "Ya jama'ar Nasara! Wallahi ni ina ganin wasu fuskokin da idan Allah Ya so gusar da wani tsauni daga muhallinsa domin alhurmansu sai Ya yi. Don haka (ina shawartarku) da kada ku yi Mubahala da su don za ku halaka ya zamo babu wani kiristan da zai wanzu a bayan kasa har tashin kiyama".

To daga nan sai suka ce wa Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya Abal Kasim! Mun yi shawara ba za mu yi mubahala da kai ba, mu bar ka a kan addininka, mu kuma mu tabbata a bisa addininmu".

Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce musu:

"Idan kun ki yarda da mubahala, to ku musulunta duk hakkin da musulmai ke da shi kuma kuna da shi, duk kuwa abin da yake kansu yana kanku". Amma sai suka ki, don haka sai ya ce musu: "To ni zan yake ku".

Sai suka ce : "Ba mu da karfin yaki da Larabawa, amma za mu yi sulhu da kai cewa ba za ka kai mana hari ba, ba za ka tsoratamu ba, ba za ka fitar da mu daga addininmu ba. Mu kuma za mu kawo riguna dubu biyu duk shekara, dubu daya cikin watan Safar dubu dayan kuwa cikin watan Rajab, da kuma sulken karfe guda talatin". Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi sulhu da su akan hakan, sa'an nan ya ce:

"Na rantse da Wanda raina yake HannunSa, hakika

halaka ta yi reto kan mutanen Najran, da sun yi mubahala (da mu) da an shafe su an mai da su birrai da aladu, da kuma kwazazzabon nan ya kama da wuta a kansu da kuma Allah Ya tuge Najran da mutanenta har tsuntsayen da ke bisa bishiyoyi, kuma da ba za a shekara ba face Nasara sun hallaka dukkansu".

Sannan Zamakhshari ya ci gaba da bayani kan tafsirin Ayar Mubahala da matsayin Ahlulbaiti (a.s) bayan da ya ba da shaidar matsayinsu mai girma da hadisin Ummul Muminina A'isha, ya ce:

"(Annabi) Ya gabatar da su (Ahlulbaiti) a kankansa ne wajen ambato domin ya yi mana tambihi a kan taushin matsayinsu da kusancinsu (ga Allah), don ya nuna cewa su abin gabatarwa ne a kan kai kuma abin fansa da su. Wannan kuwa shi ne mafi karfin dalili a kanfalalar Ashabul Kisa'i[17].

Tafsirul Kashshaf na Zamakhshari yayin tafsirin Surar Ali Imrana aya ta 61, haka nan kuma ya zo cikin Tafsirin Tha'alabi daga Mujahid da Kalbi[18].

Wannan yanayi (na fitowa domin Mubahala) yana nuna mana fitowar rundunar imani ne tana fuskantar rundunar shirka, sannan kuma wadanda suka fito (a sashin imani) su ne 'yan kangaba wajen karbar shiriya, su ne magabatan al'umma kuma mafi tsarkin cikinsu, rayuka ne wadanda Allah Ya tafiyar da dauda ga barinsu kuma Ya tsarkake su matukar tsarkakewa. Ba a mayar masu da addu'a, ba a kuma karyata wata maganarsu. Daga nan za mu fahimci cewa dukkan abin da ya zo mana daga Ahlulbaiti (a.s) yana gudana ne bisa wannan matsaya (ta tsarki da fifiko) sawa'un wani tunani ne ko shari'a ko ruwaya ko tafsiri ko shiryarwa da fuskantarwa. Domin su ne magaskanta cikin maganarsu da harkar rayuwarsu da kuma tafarkinsu.

Da Ahlulbaiti (a.s) ne Alkur'ani ya kalubalanci abokan gaba Musulunci, ya sanya masu jayayya da su su ne makaryata abubuwan bijirowar tsinuwa da azaba; "sa'an nan kuma mu sanya la'anar Allah a kan makaryata".

Shakka babu da ba don an lamunce mana tabbatuwa da kuma gaskiya cikin abin da yake fitowa daga gare su ba, da Allah bai ba su wannan daukaka ba kuma da Alkur'ani bai yi furuci da wannan ba.

Fakhrurrazi ya kawo cikin tafsirinsa Alkabir kwaton-kwacin abin da Zamakhshari ya ruwaito, inda tafsirinsu suka dace da juna a wannan matsayin. Sannan ya yi karin bayani a kanzancen Zamakhshari da cewa:

"Ka sani cewa wannan ruwaya daidai take da abin da aka daidaita a kan ingancinsa tsakanin ma'abuta tafsiri da hadisi[19]".

Allama Tabataba'i ya ce wadanda ake nufi a wannan aya kuma wadanda Allah Ya yi nufin (amfani da su wajen) tsinewa abokan gabarsu, su ne Manzon Allah (s.a.w.a.), Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.). Ga abin da Allama Tabataba'in ya ce:

"Malaman hadisi sun hadu a kanruwaito wannan ruwaya da samun karbuwarta, kuma ma'abuta manyan littattafai kamar su Muslim a cikin Sahihinsa da Tirmidhi a nasa Sahihin, sun tabbatar da wannan ruwaya, sannan malaman tarihi sun karfafa ta. Kana kuma malaman tafsiri sun hadu a kankawo wannan ruwaya cikin tafsiransu ba tare da wata suka ba, ba kuma kokwanto. Haka nan kuma akwai malaman hadisi da tarihi kamar su Dabari da Abul Fida da Ibn Kathir da Suyudi da sauransu".

A cikin wannan aya mai albarka, Allah da ManzonSa Sun yi amfani da Ahlulbaiti (a.s) wajen yin Mubahala da abokan gaban Allah, to hakan kuwa yana sanar da al'umma matsayi da daukakan da suke da shi. Hakika ba don wannan kebantacciyar daukaka da suke da ita a wajen Allah ba, da kuma tsarki na musamman ma ba, da Manzon Allah (s.a.w.a.) bai kira wadannan taurari tsarkaka domin yin barazana ga makiya Allah da saukar da azaba da kuma lamunce amsa addu'arsu ba.

A cikin ayar akwai ma'anoni masu zurfi na harshen da aka yi amfani da shi cikin maganar wadanda lallai ne a yi la'akari da su, hakan kuwa shi ne danganta wadannan Taurari (Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini) da Annabi (s.a.w.a.), wato cewan da aka yi "'ya'yanmu" da "matanmu" da "kanmu".

Ba don faruwar wannan lamari da fitar da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi da wadannan Taurari tare da shi ba, da mai yiyuwa zukata su koma ga matan Annabi (s.a.w.a) wajen kalmar "matanmu", wajen kalmar "'ya'yanmu" kuwa zuwa ga Fadima da sauran 'ya'yan Ma'aiki (s.a.w.a.), sannan wajen kalmar "kanmu" kuwa zuwa ga zatin Annabi (s.a.w.a) mai tsarki shi kadai.

Amma fita da wadannan mutanen hudu da Annabi ya yi tare da shi koma bayan wasunsu, ya fassara mana cewa mafificiyar macen wannan al'umma kuma abin koyi gare ta ita ce Nana Fadima (a.s.), zababbun 'ya'yan musulmi kuwa su ne Hasan da Husaini (a.s.), don kuwa Alkur'ani ya dangantasu ga Annabi (s.a.w.a.) sai suka zama 'ya'yansa, kamar yadda aya ta nuna. Kana kuma Alkur'ani ya dauki Aliyu (a.s.) tamkar ran Manzo (s.a.w.a).

Ta Hudu: Ayar Salati

"Lalle, Allah da Mala'ikunSa suna salati ga Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi". (Surar Ahzab, 33:56)

A cikin ayoyin da suka gabata, Alkur'ani mai girma ya yi magana a kan tsarkin Ahlulbaiti (a.s) da kaunarsu da kuma cewa su ne mutanen gidan Manzon Allah (s.a.w.a.). Masu fassara kuma sun iyakance wadannan mutane da sunayensu cewa su ne Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.).

To wannan ayar kuwa ta kawo umurni ne na wajibcin yin salati ga Annabi (s.a.w.a) da alayensa madaukaka da kuma kebancesu, koma bayan wasunsu da kuma girmama mukaminsu da karamarsu domin al'umma ta san matsayinsu wajen sakon Musulunci a cikin rayuwar al'umma.

Fakhrurrazi ya kawo cikin Tafsirinsa abin da aka ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a.) kantafsirin wannan aya mai albarka, inda ya ce:

"An tambayi Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya ya za mu yi salati a gare ka Ya Manzon Allah? Sai ya ce:

"Ku ce: Ya Allah Ka yi tsira ga Muhammadu da Alayen Muhammadu, kamar yadda Ka yi tsira ga Ibrahim da Alayen Ibrahim, Ka yi albarka ga Muhammadu da Alayen Muhammadu, kamar yadda Ka yi albarka ga Ibrahim da Alayen Ibrahim, lallai Kai Abin godiya ne, Mai girma".

Kafin ya kawo wannan nassin, sai da ya bijiro da

tafsirin ayar sannan ya ce:

"Wannan dalili ne kanmazhabar Shafi'i domin umurnin na wajibci ne[20] saboda haka salati ga Annabi yana wajabta. Kuma salatin ba ya wajaba in ba a tahiya ba, saboda haka yana wajaba ne a cikin tahiya[21] ".

Fakhrurrazi ya karkare da cewa: "Idan Allah da Mala'ikunSa sun yi wa Manzon Allah (s.a.w.a.) salati, to wata bukata kuma yake da shi ga salatinmu?

To muna iya cewa yi masa salati ba wai don yana bukatuwa ga salatin ba ne, don kuwa idan ba haka ba ne, to ai babu bukatar salatin Mala'iku bayan salatin Allah a gare shi. Amma ba kome ba ne yasa muke masa salati face bayyana girmamawarmu gare shi, da tausayawarSa gare mu domin Ya saka mana domin salatin. Don haka ne Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wanda ya yi mini salati sau guda, Allah Zai masa goma").

A ciki Durrul Mansur na Imam Suyudi, Abdurrazak da Ibn Abi Shaiba da Ahmad da Abd bn Humaid da Bukhari da Muslim da Abu Dauda da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ibn Mardawihi, daga Ka'ab bn Ujrah, ya ce wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, mun san yadda ake maka sallama, to ya ya ake maka salati? Sai ya ce: "Ka ce: Ya Allah Ka yi tsira a kan Muhammadu da Alayen Muhammadu kamar yadda Ka yi tsira kanIbrahim da Alayen Ibrahim, lallai Kai ne Abin godiya, Mai girma".

Malamin ya kawo hadisai goma sha takwas ban da wannan hadisin dukkan su suna nuni ga tarayyar Alayen Manzon Allah (s.a.w.a.) da shi cikin salati. Ma'abuta littattafan hadisi sun ruwaito su daga sahabbai daban-daban. Ga wasu daga cikinsu: Ibn Abbas da Dalha da Abu Sa'id al-Khudri da Abu Huraira da Abu Mas'ud al-Ansari da Buraida da Ibn Mas'ud da Ka'ab bn Umrah da Ali (a.s.).

Sannan kuma a cikinsa Imam Ahmad da Tirmizi sun fitar da hadisi daga Hasan bn Ali (a.s.) cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a gurinsa bai mini salati ba [22]".

Kamar haka ne malaman fikihu suka ruwaito wajibcin salati ga Annabi Muhammadu da Alayensa (a.s.) cikin tahiyar salla[23] da wajibcin kawo ambaton Alayen Muhammadu cikin salla.

Duk wanda ya sa ido a kan wannan aya zai fahimci cewa manufar shar'anta salatin da lizimtar da shi shi ne girmama Alayen Manzon Allah (s.a.w.a.), wadanda Allah Ya tafiyar da dauda daga gare su kuma Ya tsarkake su matukar tsarkakewa, domin al'umma ta yi koyi da su, ta bi tafarkinsu, kuma ta fake a gare su lokacin fitinu da sassabawa.

To wadannan da salla ba ta inganta sai gami da an masu salati, su ne Shuwagabannin al'umma, su ne a ka yi nuni da su kuma aka lamunce a yi koyi da su. Ba don tabbata da lamuncewar tsayuwarsu da kubutar abin da ya fito daga gare su ba, da Allah bai umurci musulmi a dukkan zamunna da su rataya da su da yi musu salati cikin kowace salla ba.

Hakika cikin wannan maimaitawa - maimaita salati ga Annabi da Alayensa, da kuma farlanta hakan a kowace salla - akwai jaddadawa da jan hankulan musulmi cikin kowace salla saboda muhimmanci Ahlulbaiti (a.s) da matsayinsu, da kuma koyi da su da rayuwa bisa tafarki da hanyarsu.

Ta Biyar: Surar Insan

"Hakika mutane na gari suna sha daga wani kofin (giya) da mahadinta ya kasance mai kamshin kafur ne.

(Shi kafur din) wani marmaro ne da bayin Allah suke sha daga gare shi suna bubbugo shi bubbugowa ta hakika. (Don ko) suna cika alkawari na bakance suna kuma tsoron ranar da sharrinta ya kasance mai tartsatsi ne. Suna kuma ciyar da abinci tare da kuma suna son sa; ga miskini da maraya da kuma ribatacce a yaki. (Suna cewa): "Mu kawai muna ciyar da ku ne saboda Allah, ba ma nufin sakamako ko godiya daga wurinku. Hakika mu muna jin tsoron rana mai sa daure fuska matsananciya daga Ubangijinmu". Sai Allah Ya kare su (daga) sharrin wannan ranar Ya kuma hada su da haske da kuma farin ciki. Ya kuma saka musu da Aljanna da alhariri saboda hakurin da suka yi. Suna masu kishingida a cikinta a kan gadaje ba sa samun zafin rana ko sanyi a cikinta. Inuwowinta suna kusa da su, an kuma yiwo kasa-kasa da 'ya'yan itacenta kasa sosai. Ana kuma kai-ka-wo da korai na azurfa da kofuna wadanda suka kasance na karau. Karau din na azurfa ne, sun auna su, aunawa daidai da bukata. Ana kuma shayar da su wata giya a cikinta wadda mahadinta ya kasnce mai kanshin zanjabilu ne (watau citta mai yatsu). (Shi zanjabilu) wani marmaro ne a cikinta da ake kiran sa Salsabilu. Samarin hadimai dawwamammu da ba sa tsufa kuma suna kai-ka-wo tsakaninsu, idan ka gan su sai ka yi tsammanin su wani lu'u-lu'u ne wanda aka baza. Idan kuma ka yi kallo a canza ka ga ni'ima da kuma mulki kasaitacce. A samansu akwai tufafi sakar alhariri koraye da kuma abawarsa, aka kuma yi musu ado da warawarai na azurfa, Ubangijinsu kuma Ya shayar da su abin sha mai tsafta. Hakika wannan ya kasance sakamako ne a gare ku, kuma aikinku ya kasance abin godewa.

A cikin wadannan ayoyi masu albarka, Alkur'ani ya yi zancen Ahlulbaiti (a.s) ya kuma sanya su su ne koluluwar masu gabatar da wani bisa kansu wajen ciyarwa da kuma takawa. Alku'ani ya sanya su misali da ja-gora ga dan'Adam, domin sauran mutane su yi koyi da su da kuma rayuwa bisa tafarkinsu.

Abin da ya faru har ya sa aka saukar da wadannan ayoyi dominsa yana nuni ne da matsayin Ahlulbaiti (a.s) da kaiwarsu matuka wajen aikatawa da lizimtar shari'a da kuma fuskantar Allah cikakkiya. Kuma su ne mutanen kirkin da aka yi musu albishir da aljanna, to duk wanda ya yi koyi da su, ya yi tafiya a kan tafarkinsu, to za a tashe shi tare da su. Zamakhshari ya kawo bayani kan wannan aya cikin tafsirinsa. Ga abin da ya ce:

(Daga Ibn Abbas (r.a.): Wata rana Hasan da Husaini (a.s.) sun yi rashin lafiya, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) tare da wasu mutane suka ziyarce su don gai da su, sai ya ce wa Imam Ali (a.s.): Ya Abal Hasan, da dai ka yi bakance kan rashin lafiyar 'ya'yanka. Sai Aliyu da Fadima da baiwarsu Fiddha suka ce idan suka sami sauki daga wannan ciwo nasu, za su yi azumin kwanaki uku. Sai kuwa suka warke, alhalin kuwa a wannan gida mai albarka babu wani abu na daga abinci. Sai Aliyu (a.s.) ya yi bashin sa'i uku na Sha'ir daga wani Bayahude mai suna Sham'un Alkhaibari, daga nan sai Fadima ta nika sa'i guda ta yi gurasa biyar, adadin mutanen gidan. Sai ta sanya gurasar a gabansu domin su yi buda baki, bayan lokacin shan ruwa ya yi. Sun shirya za su ci kenan sai ga wani almajiri ya tsaya a kofa ya ce: Assalamu Alaikum, mutanen gidan Muhammadu (s.a.w.a), ni miskini ne daga miskinan musulmi, ku ciyar da ni, Allah Ya ciyar da ku daga abincin aljanna. Sai suka fifita shi (wajen cin abincin) wato suka dauka suka ba shi, su kuwa suka kwana ba su dandani kome ba, sai ruwa, sannan kuma

suka wayi gari da azumi a bakinsu. Da suka kai maraice, suka sake shirya abincin buda baki, sai ga wani maraya ya tsaya a kofa ya yi bara, nan take suka dauki abincin suka ba shi, suka kwana haka. A rana ta uku ma suka ci gaba da azumi, shi ma da lokacin buda baki ya yi suka shirya dan abin da ya sawwaka, a nan ma sai ga wani kamamme ya zo shi ma yana neman abin da zai ci. Sai suka dauki abin da suka tanada suka ba shi.

Da suka wayi gari sai Aliyu (r.a.) ya kamahannun Hasan da Husaini suka nufi gurin Manzon Allah (s.a.w.a.). Yayin da Annabi (s.a.w.a) ya gansusuna karkarwa kamar 'ya'yan tsaki saboda tsananin yunwa, sai ya ce: "Babu abin da zai bakanta mini rai fiye da halin da na ganku a ciki". Sai ya tashi ya tafi tare da su sai ya ga Fadima (a.s.) tana wurin sallarta alhali bayanta ya mannu da cikinta, idanunta sun fada. Ganinta cikin irin wannan hali ya bakanta wa Manzon Allah (s.a.w.a.) rai, sai ga Jibrilu (a.s.) ya sauko ya ce: "Karbi ya Muhammadu, Allah Na tayaka murna batun Ahlulbaitinka", sai ya karanta masa wannan surar[24] .

Ta Shida:

Hakika ayoyin Alkur'ani masu yawa sun sauka da batun Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s.) wanda aka yi tarbiyyarsa cikin gidan Manzon Allah (s.a.w.a.) tun yana karami[25] . Ya tashi karkashin kiyayewarsa (s.a.w.a) don haka ya kwaikwayi halayensa. Ya yi imani da shi, gaskanta shi da kuma binsa tun yana dan shekara goma. Sannan kuma Imam Ali (a.s.) ya kasance mai daukar tutar Manzon Allah (s.a.w.a.) kuma shi ne jarumin sojansa wanda ya kere kowa a dukkan yake-yakensa, da suka hada da Badar, Uhud, Hunain, Ahzab, Khaibar, Zatu Silasil da dai sauransu. A saboda irin jaruntar da ya nuna a irin wadannan yakuna, ya sa Manzon Allah (s.a.w.a.) da kansa ya jinjina masa da bayyanar da wasu kalmomi dawwamammu da suka kasance ado ga littatta-fan tarihi sannan kuma abin koyi na koli cikin sadaukar-wa da kuma jihadi.

Idan muka yi bincike kanasbabun Nuzul (dalilan saukar ayoyi), za mu samu cewa abin da ya sauka dangane da Amirul Muminina, Aliyu bn Abi Talib (a.s.) - ban da abin da muka ambata na Ahlulbaiti (a.s) - suna bayani ne:

  1. Kan jaruntar Aliyu (a.s.) gwarzontaka da kuma sadaukarwarsa a kan tafarkin Allah.
  2. Kan hakurinsa bisa cutarwa da izgili.
  3. Kan gudun duniya, takawa ilimi da kuma kaunarsa ga muminai.

Bari mu ambatowasu misalai kamar haka:

Ayar Wilayah:

إِنَّمَا وَلِيُّكُمُ اللّهُ وَرَسُولُهُ وَالَّذِينَ آمَنُواْ الَّذِينَ يُقِيمُونَ الصَّلوةَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَوةَ وَهُمْ رَاكِعُونَ وَمَن يَتَوَلَّ اللّهَ وَرَسُولَهُ وَالَّذِينَ آمَنُواْ فَإِنَّ حِزْبَ اللّهِ هُمُ الْغَالِبُونَ

"Abin sani kawai, majibincinku Allah ne da ManzonSa da wadanda suka yi imani, wadanda suke tsayar da salla, kuma suna bayar da zakka alhali suna masu ruku'i. Kuma wanda ya jibinci Allah da ManzonSa da wadanda suka yi imani, to, kungiyar Allah su ne masu rinjaye". (Surar Ma'ida, 5: 55-56)

Zamakhshari cikin tafsirinsa ya bayyana cewa:

"Wannan aya ta sauka ne dangane da Aliyu (Allah Ya karrama fuskarsa) lokacin da wani ya roke shi alhali

yana cikin ruku'in salla, sai ya sake masa zobensa wanda yake loko-loko a dan kuriyarsa, wanda cire shi baya bukatar aiki mai yawa da ka iya bata salla. Idan ka ce ta ya ya za a ce da Ali ake alhali lafazin na jam'i ne? sai in ce maka: An zo da shi akan lafazin jam'i ne ko da yake dalilin saukar ayar a kan mutum guda ne domin a kwadaitar da mutane wajen yin tamkar aikinsa, sai su sami tamkar ladansa. Domin kuma tambihi cewa halayen muminai wajibi ne su kasance da wannan koluwa wajen kwadayin aikin alheri da bibiyar lamarin mabukata ta yadda idan wani abin da ba ya son jinkiri ya lizimce su suna cikin salla, ba sa jinkirta shi sai an idar da sallar[26] ".

Al-Wahidi ya ambata cewa al-Kalbi ya fadi cikin dalilin saukar wannan aya, cewa:

"Lalle karshen wannan aya a kanAliyu dan Abi Talib (r.a.) take domin ya ba da zobensa ga wani mai bara alhali yana cikin ruku'un salla[27]".

Littattafan tafsiri da hadisi masu yawa sun ambato cewa wannan aya mai albarka ta sauka ne dangane da Imam Ali (a.s.). Akwai cikakken bayani kan hakan cikin wadannan littattafa ga mai karin bayani[28] .

Ayar Tabligh (Isar da Sako):

يَا أَيُّهَا الرَّسُولُ بَلِّغْ مَا أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ وَإِن لَّمْ تَفْعَلْ فَمَا بَلَّغْتَ رِسَالَتَهُ وَاللّهُ يَعْصِمُكَ مِنَ النَّاسِ إِنَّ اللّهَ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الْكَافِرِينَ

"Ya kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar maka daga Ubagijinka. Kuma idan baka aikata ba, to, ba ka iyar da sakonSa ba kenan, kuma Allah Zai tsare ka daga mutane....[29] " (Surar Ma'ida: 5:67)

An saukar da wannan aya ne a wani kwari da ake ce ma Ghadir Khum. Ga bayanin akan abin da ya faru:

An ruwaito cewa, yayin da Manzon Allah (s.a.w.a.) yake dawowa daga Hajjin Ban Kwana[30] sai wannan aya (da muke magana a kanta) ta sauka a gare shi a rana ta goma sha takwas ga watan Zul Hajji[31].

To sai ya yada zango a Ghadir Khum daga Juhfa[32] , inda a nan ne kuma hanyoyi suka rarrabu zuwa birnin Madina, Masar da kuma Sham. Sai ya tsaya a nan har wadanda suke bayansa suka iso, wadanda suke gaba kuwa suka komo inda yake[33] . Akwai wasu itatuwan kaya a rarrabe, sai aka hana Sahabbai sauka a karkashinsu. Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya sa aka sare wadannan itatuwa na kaya[34] , sai ya sa aka yi kiran salla[35] , ya sallaci azahar tare da jama'a cikin garjin rana[36] . Daga nan sai ya mike ya gudanar da huduba bayan ya yi godiya ga Allah da kuma tsarkake Shi da kuma yin wa'azi ga al'umma, sai ya ce:

"Hakika an kusa a kira ni kuma in amsa, ni kuma abin tambaya ne ku ma abin tambaya ne, to me za ku ce?

Sai suka amsa: "Za mu ba da shaidar cewa kai ka isar da sako, ka yi nasiha, to Allah Ya saka maka da alheri".

Sai Annabi (s.a.w.a) ya ce: "Shin ba kwa shaidar cewa babu abin bauta da gaskiya face Allah ba, kuma Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, da cewa aljanna gaskiya ce, wuta ma gaskiya ce"?

Sai suka ce: "Haka ne, mun shaida hakan".

Sai ya ce: "Ya Allah Ka shaida", sai ya ci gaba da cewa: "Shin ba kwa ji".

Sai suka ce: "Na'am" (watau suna ji).

Sai ya ce: "Ya ku mutane! Ni mai gabata ne ku kuma masu iske ni ne a bakin tabki, fadinsa tamkar tafiyar tsakanin garin Basra da San'a'[37] ne, akwai kofuna na azurfa, yawansu kamr adadin taurari, ni kuma mai tamabayarku ne batun abubuwa biyu masu nauyi (Sakalaini), to ku kula da yadda za ku kasance game da su a bayana".

Sai wani ya yi kira ya ce: "Mene ne wadannan nauyaya biyu, Ya Manzon Allah?

Sai ya ce masa: "Littafin Allah, gefe yana hannun Allah, gefe kuma yana hannunku, to ku yi riko da shi, ba za ku bata ba, ba za ku canjba ba, da kuma iyalina, mutanen gidana. Hakika Mai Tausayawa, Masani, Ya sanar da ni cewa su biyun ba za su rabu da juna ba har sai sun iske ni a bakin tafki. Na roka musu wannan wajen Ubagijina, saboda haka kada ku gabace su sai ku halaka, kada ku takaita (ga barinsu), sai ku halaka, kada ku sanar da su domin sun fi ku sani[38] .

Sannan sai ya ce: "ashe ba ni ne nafi cancanta ga kowane mumini a kan kansa ba"?

Sai suka ce: "Haka ne, Ya Manzon Allah[39] ".

Daga nan sai ya kama hannun Aliyu bn Abi Talib (a.s.) ya daga sama har mutane suka ga farin hammatarsa[40] , ya ce:

Ya ku mutane! Allah Shi ne Majibincina, ni kuma ni ne majibincinku[41] . To duk wanda na ke majibincinsa, wannan Aliyun majibincinsa ne. Ya Allah! Ka jibinci wanda ya jibince shi, Ka yi gaba da wanda ya yi gaba da shi[42] , Ka taimaki wanda ya taimake shi, Ka wulakanta wanda ya wulakanta shi[43] , Ka so mai son sa, Ka ki wanda ya ki shi[44] ".

Sannan sai ya ce: "Ya Allah Ka shaida[45] ".

Ba su (Manzon Allah da Aliyu) rabu ba har sai da Allah Ya saukar da wannan aya:

"A yau Na kammala muku addininku, kuma na cika muku ni'imaTa a kanku, kuma Na yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku". (Surar Ma'ida, 5:3)

Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:

"Allahu Akbar! Bisa kammalar addini da cikar ni'ima da yardar Ubangiji da Manzancina da walittakan Aliyu[46] ".

Akwai ayoyi masu yawa, wadanda wannan karamin littafi ba zai iya tattaro su ba, da suke magana a kan matsayin Ahlulbaiti (a.s) da karamar su da girman mutanen ciki, wadanda wasu daga cikinsu sun kebanta ne ga Uban wannan itace mai tsarki, wato Imam Ali (a.s.). mai karatu zai iya samun wadannan ayoyi cikin littattafan tafsiri, hadisi, tarihi da kuma masu bayani kanfalalolin wadannan taurari da kuma wadanda suka yi magana kan Asbabun Nuzul na wadannan ayoyi. To amma bari mu kawo kadan daga cikin irin wadannan ayoyi, su ne kuwa:

(1). Fadin Allah Madaukakin Sarki:

وَيَقُولُ الَّذِينَ كَفَرُواْ لَوْلآ أُنزِلَ عَلَيْهِ آيَةٌ مِّن رَّبِّهِ إِنَّمَا أَنتَ مُنذِرٌ وَلِكُلِّ قَوْمٍ هَادٍ

"Abin sani kawai kai mai gargadi ne kuma a cikin kowadanne mutane akwai mai shiryarwa". (Surar Ra'ad, 13:7)

Hadisi ya zo cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya sanya hannunsa bisa kirjinsa, ya ce:

"Ni mai gargadi ne, ko wadanne mutane kuma suna da mai shiryarwa", sai ya yi nuni da hannunsa zuwa Ali (a.s.), sai ya ce kai ne mai shiriyarwan, Ya Aliyu, da kai masu shiryuwa za su shiryu a bayana[47] ".

(2). Fadar Allah Madaukakin Sarki:

قَالُوا إِنَّا تَطَيَّرْنَا بِكُمْ لَئِن لَّمْ تَنتَهُوا لَنَرْجُمَنَّكُمْ وَلَيَمَسَّنَّكُم مِّنَّا عَذَابٌ أَلِيمٌ

"Shin wanda ya zama mumini yana kamar wanda ya zama fasiki? Ba za su yi daidai ba". (Surar Sajada, 36: 18)

Wannan mumini kuwa shi ne Aliyu (a.s.), fasikin kuma shi ne Walid bn Ukba[48].

(3). Fadar Allah Madaukakin Sarki:

أَفَمَن كَانَ عَلَى بَيِّنَةٍ مِّن رَّبِّهِ وَيَتْلُوهُ شَاهِدٌ مِّنْهُ

"Shin wanda ya kasance a kanhujja bayyananna daga Ubangijinsa, kuma shaida na binsa daga gare shi...." (Surar Hudu, 11:17)

Manzon Allah (s.a.w.a.) shi ne yake bisa hujja bayyananna a al'amarinsa, shaidan kuwa shi ne Imam Ali (a.s.)[49] .

(4). Fadar Allah Madaukakin Sarki:

فإنَّ اللهَ هُوَ مَوْلاهُ وجِبْريلُ وصَالحُ المؤمِنين

"....to lalle Allah Shi ne Mataimakinsa da Jibrilu da Salihin muminai...." (Surar Tahrim, 66: 4)

Salihin muminai a nan shi ne Aliyu bn Abi Dalib (a.s.)[50] .

(5). Fadar Allah Madaukakin Sarki:

وتَعِيَها أُذُنٌ واعِيَةٌ

"...kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye". (Surar Alhakkatu, 69: 12)

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya karanta wannan aya, sai ya juya ga Ali (a.s.), ya ce: "Na roki Allah da ya sanya shi shi ne kunnenka".

Sai Ali (a.s.) ya ce: "Babu wani abu da na ji daga Manzon Allah (s.a.w.a.) na manta shi[51] ".

Al-Wahidi ya nakalto cikin Asbabun Nuzul daga maruwaita daga Buraida, cewa:

"Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce wa Aliyu (a.s.) cewa: "Allah Ya umurce ni da in kusato da kai, kada kuma in nisantar da kai, cewa kuma in ilmantar da kai, don ka kiyaye, kuma Allah Ya yi alkawarin Zai sa ka kiyaye din. Sai aya ta sauka: "Kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye".

(6). FadinSa Madaukakin Sarki cewa:

إنَّ الَّذينَ آمَنوا وعَمِلوا الصَّالِحَاتِ سَيَجْعَلُ لمُمُ الرَّحْمنُ وُدًّا

"Hakika wadanda suka ba da gaskiya suka kuma yi aiki na nagari, to (Allah) Mai rahama Zai sanya soyayya a tsakaninsu". (Surar Maryam, 19: 96)

Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce wa Aliyu (a.s.) cewa:

"Ya Aliyu ka ce: "Ya Allah Ka sanya mini wani alkawari, kuma Ka sanya mini soyayya cikin zukatan muminai". Sai Allah Ya saukar da wannan ayar dangane da Aliyu (a.s.)[52] .

(7). Fadar Allah Ta'ala cewa:

إنَّ الَّذينَ آمَنوا وعَمِلوا الصَّالِحَاتِ أُولئكَ هُمْ خَيْرُ البَرِيَّة

"Lalle ne wadanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan kwarai, wadannan su ne mafifita alherin halitta"(Surar Bayyina, 98:7)

Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: "Ya Aliyu, mafifita alherin halitta (a cikin wannan aya) su ne, kai da 'yan shi'arka[53] ".

(8). Fadar Allah Madaukakin Sarki cewa:

أَجَعَلْتُمْ سِقَايَةَ الْحَاجِّ وَعِمَارَةَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ كَمَنْ آمَنَ بِاللّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ

"Yanzu kwa mayar da shayar da alhazai da raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya ba da gaskiya da Allah da ranar lahira kuma ya yi jihadi domin Allah?...." (Surar Tauba, 9: 19)

Lalle wadannan su ne Abbas da Dalha, wanda ya yi imani kuwa shi ne Aliyu (a.s.).

Akwai wasu ayoyi da dama a kanwannan lamari da muke magana a kansa, amma za mu takaita saboda takaitawa.