Tambayoyi dangane da Alkur'ani

dai-dai da fatawar ayatullahi sistani

1-Shin ya halatta mutum ya yi imani da dukkan kira'o'i bakwai?

Amsa:Babu laifi ya halatta.

2- shin wajibi ne mace ta boye gashinta yayin karatun kur'ani?

Amsa:Ba dole ba ne.

3-Shin alwalla wajibe ce yayin karatun kur'ani?

Amsa: Ba wajibi ba ce, idan ba za'a taba rubutun kur'ani ba.

4-mene ne hukunci amfani da kayan sa maye?

Amsa: bai halitta ba ayi amfani da kayan sa maye .

5-Shin ya halitta a saida Alkur'ani?

Amsa: Ya halitta a saida wa musulmi, koda yake abin da ya fi shi ne, idan za' a yi ciniki sai a yi ciniki a kan bango da takardun kur'anin, ba rubutun kur'anin ba.

6-Shin wajibi ne mutum ya yi sujjada yayin da ya ji an karanta ayar sujjada a cikin rediyo ko talabijin?

Amsa:Ba wajibi ba ne. sai dai idan ya kasance ana yin karatun ne a lokacin, ba kaset ba ne.

7- Me ake fada, yayin sujjadar karatun Alkur'ani maigirma?

Amsa:Ba dole ba ne a fadi wani abu, Amma an so ka fadi wannan addu'ar:

( لا إله إلا الله حقاً حقاً لا إله إلا الله إيماناً وتصديقاً لا إله إلا الله عبوديةً ورقاً سجدتُ لك يا رب تعبداً ورقاً لا مستنكفاً ولا مستكبراً بل أنا عبد ذليل ضعيف خائف مستجير )                                       

8-Shin ya halitta mutum ya sumbaci kur'ani?

Amsa:Ya halitta babu wani dalili da ya hana hakan.

9- Mene ne hukuncin wanda bai sauke kur'ani ba a cikin watan ramadan, duk da cewa ya yi niyyar sauke shi zuwa karshen watan?

Amsa: Ba bu wani abu a kansa.

10-Shin gaskiya ne bai halitta ba mutum ya manta abin da ya hardace daga Alku'ani, kuma wajibi ne ya koma ya hardace abin da ya manta din?

Amsa:Ba harumun ba ne.

11- wace dabba ce a ka ambata da sunaye daban-daban a cikin kur;ani, so nawa ne aka ambace ta kuma cikin wadan ne surori ne?

Amsa: Naka-64 Hud.Jamal-40 a'araf  Al;ba'ir 65-yusuf.

12-mene ne matakin da musulmi zai dauka yayin da yaga wanda ba musulmi ba ya mallaki kur'ani?

Amsa:Ba wajibi ba ne ya dauki wani mataki.

13-Mene ne hukuncin kyautar kur'ani ga wanda ba musulmi ba(tarjama)?

Amsa: Babu laifi matukar ba zai wulakanta shi ba.

14-Shin ya inganta mutum ya karanta kur'ani da niyyar ladar ga wani wanda yake so, alhalin yana raye?

Amsa: Ya halitta hakan.           

15-Shin ya halitta sauke kur'ani ga mamaci ta hanyar kaset?

Amsa: Ya halitta babu laifi.

16- Shin dole ne mutum ya yi wata salla ko sadaka yayin da kur'ani ya fadi a hannunsa ba da gangan ba?

Amsa: Ba wajibi ba ne, Amma ya kamata ya kiyaye hakan, don kada ya zama wulakantarwa ga kur'anin.

17-Me ya sa aka jeranta kur'ni kamar yadda yake a yanzu, ba kamar yadda aka saukar da shi ba(wato sura ta  farko sannan ta biyu kamar dai haka..)?

Amsa:Abin da yake ingantacce shi ne, an tattara kur'ni kamar yadda yake yanzu tun lokacin Manzo maitsira, saboda haka babu matsala a kan hakan.

18-me ya sa ba'a ambaci sunan Imam Ali da sauran A'imma (a.s) ba, a cikin Alkur'ani?

Amsa:Allah ya san hikimar hakan. Amma wata kila saboda a jarraba mutane, kuma don kiyaye alfarmar alkur'anin daga makiya,don kada su janza wani abu daga garesa, kamar yadda aka yi wa hadisan manzo.

19-Shin kur'anin da ke hannummu, shi ne aka saukar wa manzo ba tare da wani canji ba?

Amsa:Haka ne, wannan kur'ani da yake a hannun musulmi shi ne aka  saukar wa manzo ba tare da wani canji ba.

20-Shin ya inganta mutum ya fahimci ma'anar aya daga wasu ayoyi, kuma mene ne hukuncin tafsirrin kur'ani da kur'ani?

Amsa: Ya Inganta a wasu wurare, amma bai wadatar ba, dole ne a koma zuwa ga ingantattun hadisai wajen fahimatar ma'anar ayoyin alkur'ani.

21-akwai ruwayoyi da dama da suke nuni da cewa akwai kari ko ragi a cikin Alkur'ani.mene ne ingancinsu kuma mene ne ra,ayinku akan hakan?

Amsa:Babu wani dalili da yake nuni akan rishin matsalar wadannan ruwayoyi, dangane da danganensu da kuma abin da suke nuni akansa.sannan kuma akwai dalilai daga ruwayoyi wadan da suka yi karo da wadannan ruwayoyin  suna nuni akan rashin ingancin hakan. Wato wadanda suke nuni da rishin kari ko ragi daga Alkur'ani mai girma,saboda haka wannan magana ta saba wa shi kansa Alkur'ani da kuma ingantattun ruwayoyi.

22-wadan ne surori ne ake sujjjada ta wajibi a cikinsu?

Amsa: Sajda, fusilat, Najm da Alak.