Matsayin hardace kur'ani

  Duk wanda ya kasance mai imani yana karanta kur'ani kuma ya hardace sa. To za a ba shi dinari dari biyu daga baitul-mali ko wace shekara idan kuma bai same cikakku ba anan duniya to  zai amshe a lahira inda yake ya fi bukatarsu.Imam Ali (a.s)

Muhimmancinsa:

Muhimmnci da wasiyar manzo a kowane lokaci akan kur'ani maigirma wannan ne ya sa al'ummar musulmi suka sa kur'sni a gaba domin ya jagoranci rayuwarsu musamman muminai a cikinsu na wannan lokaci wanda bas u da wani littafi sa kur'ani don haka suka dukufa wajen karatu,harda, koyo da koyar da shi a cikn rayuwarsu. Karatu da harder kur'ani ya kasance wata ibafa maigirma a wajen musulmai har ya zuwa yanzu da aka samu hanyar buga kur'ani ta yadda ba za'a manta shi ba, sabanin zamanin da bayan kasancewarsa ibada kuma hanya ce ta kiyaye shi kur'anin.

Don hak har ya zuwa yanzu zaka ga mahardacin kurni ana gimama sa girmamaw ata musamman a cikin musulmi.

 A ckin kur'ani dongane da harda a wuri daya ne ya yi Magana kanhkan.in da yake cewa: (æ ÇÐßÑä ãÇíÊáì Ýì ÈíæÊßä ãä ÂíÇÊ Çááøå æ ÇáÍßãÉ Çä Çááøå ßÇä ...)   wato ku hardace hikima da ayoyin kur'ani da ake karantawa a gidajenku Allah ya mai rahama ne kuma masani akan komi.

 A cikn wannan aya da yard a ta zo kafinta an yi wa matan matan manzo bayanin ayyukansu, wanda aikinsu na karshe da ake bayani shi ne wannan kur'ani da ake karantawa a cikin dakunansu to lallai su yi kokari su hardace shi.

Amma anan wannan umurni bai kebanci matan manzo ba kawaitunda kur'ani ya shafi dukkan alumma' sai dai kawai wani wuri akan yi mgana ne da wasu mutane na musamman wajen bayanin wani abu. Amma ba ya nufin cewa su kadai ake nufi ba. Saboda haka dukkan musulmi a wajen riko da kur'ani da hardarsa duk suna ciki.

Amma hadisai akan harda:

Amma hadisan da suka yi magana akan muhimmancin hardar kur'ani da falalarsa suna da yawan gaske wanda Ai'mma a.s suna nuna cewa ma mutum ba zai taka wani mataki ba sai ta hanyar hardace kur'ani maigirma.Bayanansu su ne kamar haka:

1-zama da kur'ani:

Imam sadik a.s yana cewa:"mahardacin kur'ani kuma mai aiki da shi zai kasance tare da mala'iku masu ka wo wahayi."

2- Imam Sadik a.s yana ewa:"mafi daukakar al'ummata sune mahardata kur'ani da masu salla a cikin dare.

3-Tsari daga zbar Allah:Imam Ali a.s yana cewa ku karanta kura'ani ku hardace shi Allah bay a azbatar da zuciyar da ta hardace kur'ani.

4-Rayar da zuciya:wanda yak e babu komai acikin zuciyar daga kur'ani ti kamar rusasshen gida yake.wato kamar yadda rusasshen gida yake ba ya da wani matsayi a idanun mutane to haka zuciyar da babu kur'ani a ciknta a wajen ubangiji.saboda haka kamar yadda jiki yake bukatar abinci don ya rayu hak ma zuciya tana rayuwa ne da kur'ani.

5-Don samun rahamar Ubangiji:manzo s.a.a.w yana cewa:"duk wanda ya hardace kue'ani sannan ya yi tsammani Allah ba zai yi masa rahama ba, to ya yi izgila da ayoyin Allah T.A."

6- Rubanya lada:Imam Sadik a.s yana cewa: "Duk wanda ya hardace kur'ani da wahala saboda raunin kwakwalarsa to Allah madaukki zai rubanya masa lada."

7 -Amsar ceto: Manzo s.a.a.w yan cewa:"Duk wanda ya hardace kurani za shiga lajanna kuma zai ceci danginsa guda goma."

8- Aljanna mafi daukaka:Manzo s.a.a.w Yana cewa:" yawan adadin  darajar Aljanna yawan  adadin ayoyi kur'ani ne, saboda haka lokaci da mahardacin kur'ani zai shiga Aljanna za ce masa, ka karanta kur'ani duk lkacin da ya karanta aya daya sai darajarsa  ta  yi sama, sai a ce babu wata daraja a cikin Aljanna saman darajar mahardacin kur'ani.

9-Ladar Annabawa:Manzo yana cewa:  " Mafi giman alumma bayan annabawa sai malamai sannan sai mahardata kur'ani. Zasu bar duniya kamar yadda Annawa suke barinta za a tayar da su ranar kiyama tare da Annabawa kuma zasu tsallaka siradi tare da su , sannan zasu karbi ladar Annabawa.

10-Sadakin aure:sahal bin Sa'ad yana cewa wata rana wata mata tazo wajen manzo. Ta ce ta bayar da kanta ga Allah da manzonsa wato manzo ya ba anda ya ga dama. Sai wani sahabi ya ce yana so, amma ba ya da sadaki. Sai manzo ya tambaye sa, ya san wani abu daga kur'ani sai ya ce, e ya hardace sura kaza da kaza.sai manzo ya ce to ya je ya koyar da ita wadannan surorin a matsayin sadakinta.

 Wannan shi ne kdan daga abin da ya shafi hardar kur'ani maigirma. Da fatan Allah ya ba mu ikon hardace kur'ani da kuma aiki da shi, amin.