Sakamakon hardar kur'ani

Hardace kur'ani yana da tasiri kamar yadda  karatunsa yake da tasiri maigirma.

Wadansu daga cikin wadannan tasirai ko sakamako kuwa wadan da saboda hardace ayoyi suke samuwa su ne kamar haka:

1-Ladar lahira:

Kamar yadda dai muka fada a wajen bayanin matsayin hardace kur.ani cewa mahardata kur'ani suna da matsayi madaukaki a cikin gidan Aljanna, sannan kuma ladarsu nunkin baninki ce.

2-Shiriyar Mutum:

Harda da riko da Alkur'ani suna daga cikin wasiyyoyin Imaman tsira, saboda haka a dabi'ance hardar kur'ani tana sanya danfaruwa zuwa ga Allah madaukaki sarki.

Saboda Mahardata kur'ani ko dan saboda tabbatar da abin da suka hardace, kullum zaka ga suna mai-maita abin kowace rana. Imaman tsira sun yi wasiyya ga mahardata kan cewa lallai su rika mai-maita abin da suka hardace, kamar yadda mai rakumi yakan daure guyawun rakuminsa ta yadda zai natsu ba sai ya  rika zuwa ba koda yaushe yana zagaya sa ba.To haka nan kur'ani idan ba'a  mai-maita shi to lallai abin da aka hardace kuwa zai tafi.

Saboda haka mahardacin kur'ani yakan danfaru da kur'anin yakan samar da duk abin da zai tabbatar da shi.Imam Ali a.s yana cewa:"Ba  wanda ya kasance  zai zauna da kur'ani kuma  ya saurari kur'ani, face sai ya  sadu da karuwa ko raguwa; zai karu da shiriya kuma zai ragu da bata(wato zai samu kariya daga bata).

Hardar kur'ani yakan kawo natsuwa a cikin zuciya kuma yakan kawo canji na musamman ga mutum.Mutane da yawa sakamakon saurarensu da karatun kur'ani ya sa suka canza yanayin rayuwarsu zuwa kamala da cin nasara.

3- Samar da natsuwar zuciya:

Ambaton Allah yakan kawo natsuwa ta musamman a cikin zuciyar  Dan Adam. Allah madaukaki a wani wuri cikin kur'ani yana cewa:"Ka sani zikirin Allah yana sa natsuwar zuciya." Karatun kur'ani da hardarsa yakan sanya mutum cikin wata natsuwa ta musamman kuma yakan kiyaye shi daga rashin natsuwa da kwanciyar hankali.kuma idan muka lura zamu iya ganin gaskiyar wannan Magana.makaranta kur'ani da mahardata, sun tabbatar da haka cewa lallai karatun kur'ani musamman da asuba yakan kawo wa mutum wata natsuwa ta musamman, kuma yakan zama garkuwa ga mutum daga shiga cikin wani mawuyacin hali na tashin hankali da rashin natsuwa.

Manzo mai tsira a wani wuri yana cewa:" kur'ani kamar kwalbar almiske ce wadda aka dade bakinta. Idan aka buda duk zata bice wuri da kamsi, idan kuwa aka barta a kulle babu wanda zai fa'idantu da kamshin da ke cikinta." To kur'ani ma kamar haka yake. Idan aka karanta sa yakan samar da natsuwa a wuri, amma idan aka bar shi a cikin zuciya to mutane ba zasu samu wannan kamshi da albarkarsa ba. Don haka karatun Alkur'ani ba wai kawai mai karantasa yake amfana ba.Karatunsa yana saukar da albarka da natsuwa ga dukkan al'umma baki daya.

4-Tsira daga kadaici:

Littafi shi ne mafi dacewar abokin zama, kur'ani shi ne mafi kyawo mafi can-canta abokin zama.A kan haka ne Imam Sajjad a.s. yake cewa:"Da a ce dukkan mutane duniya zasu mutu amma za,a barni da Alkur'ani, to da ba zan yi kadaici ba.

5-Don fahimtar Alkur'ani:

Abu mafi tasiri wajen hardar kur'ani shi ne kara fahimtar alkur'ani.Mahardaci saboda saninsa da ayoyin kur'ani da kuma alakarsu da juna ya kansa ya fahimci ma'anar Alkur'ani fiye da waninsa.Alkurani yana da ma'anoni na zahiri da na badini, wanda yasan alakar da ke akwai tsakanin ayoyin kur'ani yakan fahimci zurfin ma'anarsa cikin sauri, sabanin wanda ba shi da wannan masaniyar.Misali wanda yake so ya yi bincike a kan ma'anar wata kalmar kur'ani cikin sauri zai iya fahimtar ma'narta sakamakon saninsa da sauran ayoyin kur'ani wadanda suke  kama da alaka da ita.

Saboda haka sanin alaka tsakanin ayoyi yana da muhimmancin gaske wajen sanin hakikanin ma'anar aya. Wannan yakan yi sauki ga mutum idan ya hardace dukkan alkur'anin. Saboda haka harda wata abu ce mai muhimmanci ga al'ummar musulmi.

6-karfafa kwakwalwa:

harda Alkur'ani tana daya daga cikin abin da ke sa kwalwar mutum ta kara karfi wajen hardace wani abu da kuma saurin fahimta.

Saboda haka muna iya cewa daya daga cikin tasirin hardar kur'ani shi ne karfafa kwakwalwar mutum.Don haka ne zaka ga wanda ya hardace kur'ani yakan yi saurin fahimtar abubuwa fiye da wanda ba haka yake ba, kuma a dauka dama fahimtarsu daya take kafin hardar.

Hikimar da ke cikin hardace kur'ani:

Wata kila wani ya yi tambaya kamar haka cewa idan munce lokacin da aka fara saukar da Alkur'ani babu wata hanya da za'a iya kiyaye shi daga canzawa sai kawai ta hanyar hardace shi, amma yanzu da zamani ya zo wanda ana iya buga kur'ani to yanzu babu wata lalura ga hardace Alkur'ani, kawai wani nau'i ne na  wahalarwa kawai.

Anan muna iya ba da amsa ga mai wannan tambaya da cewa ai ba kawai don kiyaye kur'ani ake hardace shi ba. Wannan daya daga cikin dalilan harda ne, don haka don yanzu akwai hanyoyi daban-daban da za'a iya kiyaye sa ai ba zai hana hardace kur'anin ba, tunda akwai sauran dalilan da suka sa ake hardace shi. A sama mun fadi wasu dalilai da dama, a nan ma kuma zamu kara da wasu kamar haka:

1-Don kada a canza wani abu daga gare shi:

kamar yadda muka fada baya cikin bayani tarihin hardar kur'ani mun ce akan rubuta kur'ni ne kan fatar dabbobi da ganyan itatuwa da sauransu don kiyaye shi.saboda haka akwai yiwuwar makiya su sa hannu wajen canza wasu abubuwa daga cikinsa. Amma idan ya kasance ba ita kadai ce hanya ba to kaga kenan babu yadda za'a yi a canza kur'ani maigirma ta hanyar canza rubutu, domin akwai sa cikin zuciya wanda ba za'a canza shi ba kuma da wuri za'a iya gane cewa lallai nan an yi ragi ko an yi kari a cikin rubutunsa.

2-Aiki da kur'ani:

da ya daga cikin hikimar hardace kur'ani shi ne aiki da kur'anin. A lokacin da mutum ya hardace kur'ani kuma yasan abin da yake cewa to zaka ga kowane lokaci yakan zaman masa kamar fitila ajen haska masa inda ya kamata ya bi ko kuma ina ne bai kamata ba. Sabanin wanda bai san wani abu ba daga kur'ani ko kuma ya sani amma ba ya tare da shi a cikin zuciya.kamar yadda sahabban manzo suke cewa a lokacin da kur'ani yake sauka idan muka hardace aya goma,ba mu  kara koyon wasu sai mun ga  cewa muna aiki da su, sannan sai mu kara koyon wasu suma haka.

3-Hardar kur'ani ibada ce:

Ban da fa'idojin da muka fada a sama na hardar kur'ani, ruwayoyi da dama sun zo akan bayanin cewa hardar kur'ani ba don kawai kiyaye alku'nin ba, Allah madaukaki ya sanya  sharda a matsayin aikin ibada.Imam Sadik a.s. yana cewa:"Ya Allah ka sanya hardar kur'ani abin so a garemu."Domin duk abin da kake so shi ne zaka ba da muhimmanci akansa.saboda haka kasancewar harda  wani abu ne mai muhimmnci Imam yake rokon Allah da sanya  harda  abin soyuwa a gareshi don ba ba ta  muhimmanci.

Dukkan abin da muka fada a sama dongane da hardar kur'ani na falala da daukaka duk suna samuwa ne  ta hanyar aiki da kur'anin kawai. Saboda haka harda kamar hanya ce  don yin aiki da shi Alkur'ani ba wai kawai don kwalliya ko neman suna ba, idan ya kasan ce da wannan ma'anar ne to lallai ba shi da amfani ko kadan. Allah madaukaki ya ba mu dama da ikon hardace kur'ani tare da aiki da shi albarkacin manzo tsira da iyalansa(a.s.)

  Wassalamu alaikum warahmatullah.