Tarihin Hardar kur'ani

Manzon Allah (s.aa.w) ya zama Annabi yan dan sheka ra atba'in da haihuwa, sannan an saukar da kur'ani a cikin shekara  ashrin da uku ne aka saukar da kur'ani akan abubuwa daban-daban.

Sahabbansa s.a.a.w tare da umurninsa sun kasance suna kiyaye wannan kur'ani mai girma  a cikin takardu wadan da aka yi su da fatar dabbobi, da kuma kasusuwa na allon kafadar dabbobi, ganyan itatuwa da dai sauransu.

 Duk da haka sun kasance sun kasance suna hardace sa saboda neman albarkarsa. Don haka ne ma wannan hanyar wato harda ita ce hanya ta farko wajen kiyaye shi kur'ani kafin a zo ga rubutunsa. Wannan kuwa ya faru ne sakamakon kasancewar wancen zamani rubutun Kufa ne kawai ake amfani da shi, kuma rubutu ne mai wahalar karantawa, ga shi kuma mafi yawan mutane a wannan lokaci ba su iya rubutu da karatu ba.saboda haka ta wannan hanyrce kawai wato harda zasu iya nuna kauna da shaukinsu akan kur'ani. Don hak ne suka dukufa kan wannan aiki mai girman gaske.

Dalili kuwa akan hakan shi ne lokacin da manzo mai tsira yana a kogon Hira  lokacin da Jabra'il ya zo ma sa da wahayi in da yake ce ma sa ka karanta, sai manzo ya ba shi amsa da cewa ban iya  karatu ba. Wannan sheda ne akan cewa mutanen wannan yanki a lokaci ba su iya karatu ba, saboda manzo ba wai ya kasance sikin mutane koma baya ba ne na wannan gari ballantana a ce saboda haka hak ne bai iya karatu ba. A wannan lokaci ne fa Allah cikin ikonsa ya sawa manzo ikon iya karatu inda a ka saukar masa da surar Alak wato ayoyi biyar na farkon surar.Imam Sadik a.s yana cewa: "Ikra'a ita ce farkon ayar da aka saukarw manzo mai girma."

 Don haka mataki na farko matakin karatu ne da hardace kur'ani, domin lokacin da aka saukar wa manzo wadannan ayoyi ya karanta sai ya hardace ce a cikin zuciyarsa mai albarka.

 Don haka anan zamu yi bincke akan wannan al'amari kamar haka:

Kalmar Hafiz(mahrdaci):

Wannan kalama "Hifz" acikin harshen larabci ta zo da ma'a noni guda biyu kamar haka:Ta zo da ma'anar kiyayewa da kuma hardace wani abu ko rike sa  acikin zuciya wato kishiyar mantuwa.

A cikin kur'ani ta zo da ma'ana ta farko ne wato wato kiyayewa. Hafiz sunan mai aiki ne wato mai hardako mahardaci, amma a cikin ilimin kur'ani ana cewa wanda ya hardace dukan kur'ani tare da tajwidinsa da kuma kira'ar da aka yarda da ita "hafiz". Sannan haka ma ga wanda ya yasan hadisan manzo kuma ya san wuraren da ake da sabani da kuma wuraren da ake da ittifaki  kuma ya san masu ruwaya da kyau,  kuma ya hardace hadisi akalla hadisi dubu dari ana ce ma sa "hafiz".

A farkon musulunci ba a cewa wadan da suka hardace kur'ani "Hafiz" a wancen lokaci ana ce musu"jamma'ul kur'an, hamalatul kur'an, kurra'ul kur'an. Amahi fil kur'an da makamantan wadannan kalmomin.

Saboda hka wannan kalma ta " Hafiz" an fara amfani da ita nega mahardacin kur'ani a karshen karni na farko ko kuma farkon karni na biyubayan hijrar manzo (s.a.a.w). Amma kalmomin da muka fada a sama ana amfani da su kafin a rika amfani da kalmar"Hafiz"ba wai kawai ana amfani da su ba ne ga  mutumin da ya hardace dukkan Alkur'ani, a lokacin koda mutum wani yanki daga  kur'ani ya hardace ana kiran sa da wadannan kalmomin.Bayan tafiyar anzo ne aka rika amfani da su ga wanda kawai ya hardace dukkan kur'ani.

Farkon mahardacin kur'ani

Hardace ayoyin  kur'ani ya fara ne tun farkon saukar da kur'anin. Saboda haka farkon wanda ya hardace wani abu daga kur'ani shi ne wanda aka saukar masa da kur'anin wato manzo s.a.a.w manzo ya kasance lokacin da ake saukar da kur'ani yana karantawa a dai-dai wannan lokaci don kada ya manta shi.Shehin malami nan Tabrasi a wajen bayanin daliln saukar da     a saukar ayar nan da take cew "kada ka yi gaggwa da shi kafin a saukar maka da shi" an saukar da ita ne akan bayanin yadda manzo zai rika amsar wahayi ta yadda zai karanta ba tare da kuskure ba kuma ya hardace shi.

Manzo s.a.a.w don ya samu natsuwa ya kasance yana karanta kur'anin ga mala'ikan whayi bayan ya karba, don ya tabbatar da cewa ya hardace shi kamar yadda aka saukar da shi din.

To da haka ne dai aka fara hardar kur'ani tun farkon tarihin musulunci.