Ayar sakin aure

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ya kai wannan Annabi a duk lokacin da kuka yi nufin sakin mata, to ku sake su cikin tsarkinsu (wanda mazajensu ba su kusance su ba a cikinsa) Kana ku lissafa (kwanakin) tsarkin kuma ku ji tsoron Allah Ubangijinku, kada ku kuskura ku fitar da su daga gidajensu, kada su ma (matan) su kuskura su fita (a lokacin da suke cikin idda), sai dai idan har sun zo da alfasha mabayyaniya, to wadannan su ne iyakokin Allah. Wanda duk ya ketare iyakokin Ubangiji, hakika ya zalunci kansa, (domin kuwa) ba ka sani ba ta yiwu Allah ya haifar da wani al'amari (na sulhu a

tsakaninku) bayan haka.(l)

1- Bayani kan yanda hakikanin saki yake a musulunce:

Ta yiwu daya daga cikin dalilan da ya sa ake kiran wannan sura da sunan surar saki (Talak) shi ne irin hukunce hukuncen sakin da suke kunshe a cikinta makil, wanda wannan yana nuna mana irin la'akarin da shari'ar musulunci ta yi dangane da al'amarin saki, saboda irin hatsarin da yake da shi, domin abu ne wanda in har ba'a yi da gaske ba, kuma ba'a yi shi yanda musuluci ya zo da shi ba, sai ka samu ya taimaka wajen wargaza al'umma da tarbiyyar iyali, kana da haifar da gaba da kiyayya a tsakanin dangi.

Kamar yanda rashin kiyaye hukuncin sakin ke iya haifar da aure kan aure, wanda daga karshe a dinga haife 'ya'ya marasa tabbas din iyaye.

Kamar yanda kuma, shi saki ba wani abu ne wanda shari'a ke karfafa gudanar da shi ba, bil hasali ma shi ne halas wanda Allah ya fi ki, kamar yanda ya zo a mashahuriyar ruwaya daga Ma'asumai (A.S.)

"Babu wani abu da Allah ya halatta kuma yake fushi da shi fiye da saki.

Wannan ruwayar ta zo cikin Wasa'ilus shi'ah juzu'i na 15 shafi na 266.

Sai dai kuma wani abin tambaya a nan shi ne, mene ne ya sa shari'a ta halatta yin saki ?

Amsa a nan ita ce a irin hali na zaman yau da gobe na ma'aurata a wasu lokuta za ka samu cewa akwai wasu halaye wadanda suke faruwa marasa dadi wanda in da za'a tilasta ci gaba da zama da juna a tare da wadannan halayen, sai mu samu rayuwa za ta yi ma wanda yake cutuwa, tsanani da kunci wanda zai iya kaiwa ga halaka da abin da ya yi kama da haka.

To saboda Allah ne mahaliccin kowa da komai, kuma asanin abin da zai kai ya kawo, don haka ya kawo magani da mafita a duk lokacin da irin wadannan matsaloli suka bijiro a tsakanin ma'aurata, wanda wannan magani shi ne saki, duk da cewa ba'a son al'amarin ya kai ga haka, sai ya zama dole.

Me ake nufi da sakin mataye a cikin tsarkinsu:

Malaman tafsiri sun tafi a kan cewa ayar da ta zo a farkon wannan sura tana bayani ne kan yanda ake saki, a inda take cewa idan har an yi nufin sakin. to a sake su a cikin tsarkinsu, abin da ake nufi da haka shi ne, a sake su bayan sun yi wanka daga al'adarsu (haila) kana mijin bai kusaci iyalinsa bayan wankan ba.

Wannan ma'anar ita ce wacce ta shahara gurin masana tafsiri, sai dai akwai sabani tsakanin mazhabobi kan cewa. wannan hukuncin da ayar nan ta zo da shi. wajibi ne ta yanda da mutum zai saki matarsa a tsarkin da ya kusace ta a ciki ko kuma a halin tana haila sai ya sake ta to shin ta saku ko ba ta saku ba'.'

A nan ne malamai suke da sabani ta yanda wasu suke ganin cewa, a irin wannan halin sakin ya inganta wato hukuncin da ayar ta zo da shi ba wajibi ba ne wasu kuma suke ganin cewa sam bai inganta ba (ma'ana hukuncin da aya ta 20 da shi wajibi ne).

Mabiya mazhaban Ahlul Baiti (A.S.) a sakamakon ingantattun ruwayoyi da suka dogara da su, wadanda ke fassara ma'anar hakikanin hukuncin da wannan ayar ta zo da shi, sun yi ittifaki kan cewa, duk wani wanda ya saki matarsa a halin tana haila ko kuma ta gama hailar ya sadu da ita, sannan ya sake ta kafin ta yi tsarki to sakin nasa bai inganta ba, wato aurensa na nan, ita kuma matar ba ta gushe ba tana nan a matsayin matarsa.

Ga kadan daga cikin ruwayoyin

Ma'ana:

Bukhari da Muslim sun ruwaito daga kutaiba daga lais bin sa'ad daga Nafi'u daga Abdullah bin umar cewa: shi, Abdullah bin umar ya saki matarsa saki daya a halin tana haila, sai manzon Allah (S.A.W.A.) ya yi umami da ya mai da ita, kuma ya ci gaba da zama da ita har ya zuwa lokacin da za ta yi tsarki ta sake yin wata hailar a gidansa, kana yajira ta har sai ta yi tsarki daga wannan hailar tata, to in ya so ya sake ta, sai ya sake ta yayin da take cikin tsarkin da bai kusance ta a cikinsa ba to wannan ita ce iddar da Ubangiji Madaukakin sarki ya yi umami da a saki mata a cikinta".  

Ma'ana:

"Ya zo cikin sahih Muslim daga manzon Allah (S.A.W.A.) cewa:

A duk lokacin da wani mutum ya saki matarsa yayin da take cikin al'adarta, lallai ya zama wajibi kada ya kula da wannan saki da ya yi mata (ma'ana sakin bai yi ba) ya ci gaba da zama da matarsa har zuwa lokacin da za ta yi tsarki, sannan ya sake ta idan ya ga dama". Sahih muslim kitabut Talak juzu'i na2.

Ma'ana:

"An karbo daga Abu Ja'afar (A.S.) yana cewa: lallai sakin da Ubangiji Madaukakin sarki ya yi umami da shi a littafinsa kana Ma'aiki (S.A.W.A.) ya sunnanta shi, shi ne mutum ya nisanci matarsa, idan ta yi haila kana ta yi tsarki, sai ya kafa mutum biyu adilai a matsayin shaida kan cewa ya sake ta a halin tana cikin tsarkin da bai kusance ta a cikinsa ba, sannan shi ya fi cancantar ya mai da ita su ci gaba da zama, matukar ba ta kare idda ba (tsarki ko jini uku), to don haka duk wani saki wanda ya saba ma wannan Batacce ne, ba bakin komai yake ba, wato wanda aka yi mata shi tana nan a matsayinta na matarsa".

Wannan ruwayar ta zo cikin Alkafi juzu'i na 6 shafi na68 .

An samo daga Muhammad bin Muslim cewa ya tambayi Abu Ja'afar dangane da mutumin da ya ce wa matarsa: ke haramun ce a gare ni ko kuwa:

ba aure a tsakaninmu, ko kuwa: ba ki da miji kwata-kwata, ko kuwa ya ce: ba ni ba ke, ko ya ce: ke wofintacciya ce?

Sai Imam ya amsa masa da cewa:

Dukkannm wadannan ba a bakin komai suke ba, hakika yanda saki yake shi ne: kafin idda bayan ta yi tsarki, tsarkin da bai kusance ta a cikinsa ba, ya ce mata: ke sakakkiya ce (wato anti talikun), ko kuma ya ce da ita: "ki yi idda," da nufin cewa ya sake ta, kana ya kafa shaida da adilai biyu a kan haka."

Wannan ruwayar ta zo cikin Alkafi juzu'i na 6 shafi na 69.

To a nan muna fata mai karatu zai zabura wajen kokarin gane hakikanin hukuncin da Allah da Ma'aikinsa suka bayyana ma al'ummar musulmi dangane da saki a cikin idda wato a saki mace tana cikin tsarkinta kamar yanda muke fatan mai karatu zai kasance tare da mu har zuwa karshen wannan bahasin da kuma wannan bayanin a inda zai ga dumbin hikimomi da suke kunshe a cikin yin aiki da wannan umarni na saki a cikin tsarki.

Kamar yanda zai kara samun nitsuwa kan irin hukuncin da Alkur'ani mai girma ya tabbatar, wanda da a ce al'ummar musulmi za su yi aiki da shi, to hakika da an sami saukin yawan mutuwar aure.

A ina ya wajaba mace ta yi idda:

Wani hukuncin da wannan ayar ke dauke da shi, mai muhimmancin gaske, wanda dukkan malaman mazhabobin musulunci sun yi ittifaki a kansa, shi ne, a duk lokacin da mutum ya saki matarsa, saki na raja'i wato sakin da zai iya yin bikonta a cikinsa, to wajibi ne ya bar ta, ta gama iddarta a cikin dakinta wato a cikin gidansa, bai halatta ya fitar da ita ba, kamar yanda yake ita ma sam bai halatta ta fita daga gidan ba har sai ta gama iddarta, sai dai in ta aikata alfasha, to a irin wannan hali ne kadai ake iya fitar da ita.

Kamar yanda ya wajaba ya ba ta matsuguni, haka nan kuma ya wajaba ya ci gaba da ciyar da ita har zuwa lokacin da za ta gama iddarta, domin kuwa matar da aka yi mata sakin da za a iya yin bikonta, tana nan a matsayin mata, don haka ne ma bai halarta ya auri kanwarta ko 'yarta, kamar yanda ba zai Kara aure ba, idan da ma adadin matansa hudu ne, har sai ta gama idda.

Haka nan kuma akwai gado a tsakaninsu idan dayansu ya rasu a halin iddar ba ta cika ba, kana wajibi ne ya tufatar da ita a lokacin iddar kamar yanda yake yi a da, a takaice dai, tana nan a matsayin matsarsa har sai ta gama idda, shi ya sa ma ba ya halatta ta fita zuwa unguwa sai da izininsa, kamar dai yanda take a da kafin ya furta sakinta.

Dangane da al'amarin da ya shafi mai da ita, shi ma abu ne wanda dukkannin malamai sun tafi a kan ganin cewa mutum yana da ikon da zai mai da matarsa wacce ya sake irin sakin da ake yin kome a cikinsa (wato sakin da bai wuce daya ko biyu ba kana kuma aka yi shi kamar yanda shari'a ta zo da shi)a duk lokacin da ya ga damar mai da ita to yana da ikon yin haka, ba tare da neman izinin wani ba, ko da kuwa ita kanta matar don kuwa matukar iddar ba ta kare ba, to wuka da nama na hannun mijinta, amma da zai yi sakaci har iddarta ta kare to bai da ikon da zai iya mai da ita sai ta yarda sannan sai an daura sabon aure.

Kamar yanda an so, matar da aka yi wa sakin kome, ta dinga yawan yin kwalliya don jawo hankalin mijinta, kamar yanda shi ma, in ya so mai da ita zai iya yin hakan a aikace, wato ta hanyar yi mata wani abu wanda ba ya  Suratut Talak  To idan sun yi dab da karewar iddarsu to ku ci gaba da zama da su (bayan kun mai da su) ta kyakkyawar hanya, ko kuma ku rabu da su ta kyakkyawar hanya, kana (a lokacin da za ku yi sakin) ku tsai da shaidu biyu adilai daga cikinku, to (ku kuma wadanda aka nemi ku yi shaidar) ku tsai da shaidar domin Allah, to da wadannan (abubuwan da suka gabata ne) ake wa'azi da su ga dukkannin wanda ya yi imani da Allah da ranar tashin Alkiyama  kuma duk wanda ya ji tsoron  Allah, (Allah) zai sanya masa mafita.(2)2

halatta mutum ya yi wa matar da ba tasa ba, na sumbanta da makamantansu, kamar yanda yana iya yin amfani da lafazi gurin furta cewa ya mai da ita.

To wannan shi ne irin hukuncin da Allah ya zo da shi a littafinsa sai dai abin tambaya a nan musulmi na aiki da shi ko a'a?

2- Shin ana iya sakin mace saki uku lokaci guda?

Yana daga cikin hukunce-hukuncen da suka shafi saki na sunna, wadanda aka sami sabani tsakanin malamai a cikinsu, a saki mace saki uku lokaci guda, da kuma wajabcin kafa shaidu adalai a lokacin da za'a yi saki.

A inda mafi yawan malaman ahlus sunna suka tafi a kan ingancin aukuwar saki uku a lokaci guda, wato a yi wa mace saki uku cikin lafazi daya tak kuma ta saku saki uku alhali da can ba wata igiyar aure da ta katse a tsakaninsu.

Bisa dogaro da suka yi da wasu sashe na ruwayoyi da ke magana kan saki duk da cewa ruwayoyin da suka zo a wannan babin sun kasu kashi biyu, wasunsu suna nuna cewa, saki uku lokaci guda ya inganta, wasunsu kuma na nuna cewa saki uku lokaci guda daidai yake da saki daya, ko da kuwa a wurare daban daban ne aka furta sakin.

Kamar yanda ruwayoyi da dama ingantattu suke nuna cewa daga baya ne, bayan Manzo ya faku ake lizimta wa wanda ya yi saki uku lokaci guda da cewa sakin nasa ya tabbata saki uku, wato bai da ikon yin kome har sai matar da aka saka ta yi idda, ta yi sabon aure.

Kamar yanda muslim ya ruwaito a cikin kitabut Talak babin Talakus salas.

A inda ya fitar da hadisai uku da lafuzza daban daban wadanda suke dauke da cewa lallai bayan fakuwar Ma'aiki (S.A.W.A.) ne aka lizimta wa mutane yin riko da saki uku a lokaci guda.

Ga daya daga cikinsu:

Is'hak bin Ibrahim da Muhammad bin Rafi'i sun zantar da mu, (amma lafazin na Ibnu Rafi'i ne) Is'hak ya ce: Ma'amar ya ba mu labari.

Ibnu Rafi'i kuma ya ce Abdur Razzak ya zantar da mu) Ma'amar ya ba mu labari daga Ibnu Tawus daga babansa, daga Ibnu Abbas: cewa: saki uku a lokacin Manzon Allah da Abu bakar (r.a.) da shekaru biyu na halifancin Umar (r.a.) ya kasance ana lissafa shi a saki daya tak, sai Umar bin Khattab (r.a.) ya ce: Hakika mutane suna gaggawa cikin lamarin da suka ga suna da wata dama ta yin kome a cikinsa, me zai hana mu zartar da shi a kansu? Sai kuwa ya zartar da shi a kansu." Wato abin da wannan hadisi ke nunawa shi ne cewa, zamanin Ma'aiki da zamanin halifancin Abu bakar (r.a.) kana da shekaru biyu na halifancin Umar (r.a.), sahabbai sun kasance in sun furta saki uku a lokaci guda yana nan a matsayin saki daya tak, to irin wannan al'ada da suka kasance suna yi ba ta yi wa halifa Umar (r.a.) dadi ba, sai ya ce ba komai ya sa suke haka ba, face damar da suke da ita, na mai da matan da suka saka da irin wannan lafazi.

Don haka sai ya yi gurin cewa me zai hana ya lizimta musu saki ukun in sun farta shi a lokaci guda, duk da cewa lokacin Manzo ba haka nan hukuncin yake ba? Sai kuwa ya lizimta musu, aka wayi gari an ci gaba da aiki da wannan hukunci, duk da cewa bako ne in an kwatanta shi da hukuncin da sahabbal suke a kai, a zamanin Manzo da zamanin halifa Abu bakar.

Kamar yanda muka fada ne a farkon bayani cewa mabiya mazhabar Ahlul Bait (A.S) a bisa dogaro da ingantattun ruwayoyin da suka samu daga Imaman Ahlul Bait (A.S) sun tafi a kan cewa duk matar da aka sake ta saki uku a lokaci guda to yana nan saki bai zama uku ba.

Kamar yanda duk sakin da aka gudanar da shi ba tare da shaidu adilai ba, to wannan saki bai inganta ba.

Ga daya daga cikin dalilan da ke nuna cewa duk sakin da aka yi shi ba tare da shaidu ba wannan saki bai inganta ba.

"An karbo daga zurara daga Abu Ja'afar (A.S) cewa an tambaye shi kan wata mata wacce ta ji mijinta ya sake ta, kana daga baya sai ya musanta sakin da ya yi mata, shin za ta ci gaba da zama da shi (a matsayin matarsa)?

Sai Imam ya ce: Me zai hana, domin Lallai sakin da ya yi ba tare da shaidu ba, ba saki ba ne, sannan bai halatta ya yi saki ba tare da shaidu ba."

Wannan ruwayar ta zo cikin Alkafi juzu' na 6 shafi na 59.

Ga kadan daga cikin tarin hadisan da suke nuni kan rashin ingancin saki uku alokaci guda.

"An karbo daga Safwan, ya ce na ji Abu Abdullah (A.S) lokcin da warn mutum ya zo ya tambaye shi cewa: Na saki matata saki uku tashi guda? Sai Imam ya ce:

Wannan sakin ba a bakin komai yake ba." Wannan ruwayar ta zo   cikin Kurbul Isnad.

An samo cewa Imam Rida (A.S) ya ce; Abdullah bin Umar ya saki matarsa saki uku, sai Ma'aiki mai tsira da aminci ya mai da wannan saki uku zuwa saki guda, ta yanda ya sanya hakan irin sakin littafin Allah da Sunnar Ma'aiki."

Wannan ruwayar ta zo cikin littafin Tahzib.

Kamar yanda akwai ayoyin da Malamai ke kafa hujja da su wurin kore ingancin saki uku a lokaci guda, mai neman cikakken bayani dangane da haka ya koma ga tafsirin aya ta 229 cikin Suratui Bakara.

Yanda sakin Sunna yake:

Kamar yanda bayanai suka gabata cewa wannan sura, an rada mata suna da surar saki ce sabili da tarin hukunce hukuncen saki wadanda shari'a ta wajabta da suke a cikinta, mai karatu ya karanta wasu daga irin wadannan hukunce hukunce, kamar wanda ya shafi yin iddar matar da aka yi mata sakin kome a gidan mijinta, da wajabcin ciyar da ita na tsawon lokacin da take cikin idda, kamar yanda saki ba a cikin tsarki ba, bai inganta ba wato dole ne sakin ya zamo ya auku ne cikin tsarkin da ba a sadu da ita a cikinsa ba haka nan ma mun karanta batun rashin ingancin sakin da aka yi shi ba gaban shaidu guda biyu adalai ba, kana kuma ya gabata magana kan cewa dukkannin sakin da aka yi shi da lafazin saki uku a lokaci guda, irin wannan saki ba a bakin komai yake ba face saki daya.

Don haka muke ganin ya kamata a nan mu kawo cikon wasu sharudda wadanda idan har ba su tabbata ba, to saki babu yanda za a yi ya inganta a wajen Allah da Ma'aiki. Yana daga cikin irin wadannan sharuddan cewa shi saki dole ne a yi furuci da shi wato da za a yi shi a rubuce kadai ko kuma da ishara kadai ko hannunka mai sanda ga mutumin da ba bebe ko kurma ba, to a shari'a dai irin wadannan sakin ba su inganta ba.

Kamar yanda mafi yawan malamai sun tafi a kan wajabcin furuci da saki ya kasance da siga kebantacciya wacce take da yaren larabci wato ita ce fadin mai saki ga matarsa: (Anti talikun)

Wato "Anti talikun" Ma'ana "Ke sakakkiya ce"

Sai dai kuma sun tafi kan cewa dukkan wanda ba zai iya kawo wannan furucin da yaren larabci ba, to zai iya yi da yaren da zai iya, kamar yanda mutumin da ya gaza yin furuci da saki, ko da kuwa shi ba kurma ko bebe ba ne a sakamakon wata larura, to irin wannan zai iya amfani da ishara ko rubutu gurin sakin matarsa duk da cewa an fi son rubutu a irin wannan halin.

Wani daga sharuddan da saki ba ya inganta sai da shi, shi ne nufi wato wanda zai yi sakin ya zama ya kudurta cewa wannan kalma da yake furtawa ta saki yana nufin aiwatar da saki ne da ita, don haka mutumin da ya saki matarsa a halin yana maye ko kuma ba da niyyar yin saki ba, to sakin bai yi ba.

Kamar yanda wanda ya furta saki a sakamakon takura da dole da aka yi masa, nan ma sakin daidai yake da sakin mahaukaci, wato ya bi ruwa.

Wadannan su ne wasu daga cikin muhimman sharuddan da sai sun cika kafin saki ya inganta. Mai neman karin bayani yana iya komawa zuwa ga littattafan da suka yi bayani kan hukunce hukuncen aure da saki a mazhabar Ahlul Baiti (A.S.)

Hikimomin da suke Kunshe cikin saki irin na Sunna:

Daya daga cikin abin da yake kawo tabarbarewan tarbiyya shi ne yawan samun rabuwar aure a cikin al'umma, duk da cewa shari'ar musulunci ta halatta yin saki a lokacin da ci gaba da rayuwar aure ta faskara ta yanda in har ba a rabu ba to dayansu ko dukkansu za su fada cikin wani hali na kaka ni kai, sai dai za ka samu cewa shari’a ta dauki matakin da ta kare mutane daga aukawa cikin hatsarin rabuwar aure ta hanyar sanya ka'idoji da iyakoki wadanda idan musulmi suka yi aiki da su, sai ka samu abu ne mai wahala wani ya saki matarsa kuma ta saku.

Irin wadannan matakan wadanda shari'a ta yi amfani da su wurin kare mutane daga hadarin rabuwar aure su ne ake kira da hikimomin da suke kunshe cikin saki irin na sunna. Ga kadan daga cikinsu.

Yana daga cikin irin wadannan hikimomi a wajabta wa mace zama a gidan mijinta bayan kuma ya sake ta har zuwa lokacin da za ta gama idda, muddun dai sakin ba ba'ini ba ne kamar yanda aka wajabta wa namiji ci gaba da rike ta a gidansa, da ciyar da ita da shayar da ita da tufatar da ita har tsayin lokacin da ta gama idda.

Kamar yanda akwai ruwayoyin da suke dauke da bayanai kan yanda ya kamata matar da aka sake ta sakin kome, ta kasance kullum cikin ado, da sa turare kana da kyautata dabi'u wadanda za su jawo ran mijinta ya yi sanyi, ya kuma karkato hankalinsa zuma gare ta.

An karbo daga Imam Bakir (A.S.) yana cewa: Matar da aka saki ya kamata a ce tana yin kunshi tana kuma rangada kwalli, kuma tana fesa turare, kana tana caba ado yanda ta ga dama, domin Allah Ta' ala yana cewa "ta yiwu bayan haka Allah ya haifar da wani abu (a tsakaninsu)" watakila shaukin mai da ita ya darsu a cikin zuciyarsa sai ka ga ya mai da ita.Wannan ruwayar ta zo cikin Tafsirus sakalain juzu'i na 5 shafi na 352.

Wata hikimar kuma ita ce maganar a saki mace a cikin tsarkin da ba a kwanta da ita a cikinsa ba, ta yanda da za a yi sakin a halin an sadu da ita a cikin wannan tsarkin to sakin bai yi ba, wato dole ne a jira sai ta yi tsarki daga al'adanta. Wanda wannan jiran abu ne wanda zai iya taimakawa wajen hucewar fushin mijinta, ka ga sun dawo sun ci gaba da zaman lafiya a tsakaninsu.

Kana yana daga cikin manya manyan hikimomin da ke hana saurin aukuwar rabuwar aure, maganar kafa shaidu biyu adalai, wadanda idan da za a yi saki babu su ko kuma babu daya daga cikinsu, to wannan sakin sam bai yi ba a shar'ance. Wannan magana ta shaidu biyu adalai ta magance mana matsalar sakin mata da tsakar dare, kamar yanda ko da an samu shaidu biyu matsawar ba su sifantu da sifa ta adalci ba ko kuma daya daga cikinsu ba adali ba ne shi ma dai saki bai yi ba.

Kamar yanda kuma shari'a take kwadaitar da cewa ya kamata miji ya yi wa matar da ya saka, saki na sunna, (ya yi mata) ihsani wato ya kyautata mata kyautatawa su rabu cikin mutunci, wanda tasirin yin haka yana da yawan gaske, kadan daga cikin irin wannan tasiri shi ne yanda matar ba za ta kullace shi a ranta ba ta yanda idan akwai haihuwa a tsakaninsu, gaba da kiyayya ba za su faru ba sakamakon irin wannan rabuwa ta mutunci da suka   yi.

Idan kuma har ba 'ya'ya to zumunci ba zai rushe tsakanin danginta da dangin tsohon mijinta, wanda suka rabu cikin mutunci ba.

A nan za mu so mu cike wannan binciken da wasu kalmomi na nasiha ga ma'aurata. Akwai tarin hadisai daga Ma'aiki (S.A.W.A.) wadanda ke yin horo ga miji da mata kan lizimtan tsabta da nesantar kazanta da duk wani abu wanda zai haifar da kyamar juna, kana da aikata dukkannin wani abu da zai jawo kauna da soyayya tsakaninsu, shin ta hanyar magana ne ko mu'amala ta hanyar ado ne ko kuma zuwa da abin dariya da nishadi a tsakaninsu.

Wani abin takaici sai ka samu wasu maza suna yin nishadi a tsakanin abokan hirarsu amma da zarar sun iso soron gidan da iyalansu suke ciki take sai ka ga sun murtuke fuska, kana sun shiga kaurara murya wai su manya ne, alhali kuwa fiyayyen talikai, shugaban Manzanni Annabi Muhammad (S.A.W.A.) ga abin da yake fadi kan yanda ya kamata mu'amala ta kasance tsakanin miji da mata.Kana ya azurta shi ta inda bai yi tsammani ba, kuma duk wanda ya dogara ga Allah to shi (Allah) ya ishe shi, hakika Allah mai isar da al'amarinsa ne, lallai Ubangiji ya sanya wa kowane abu iyaka.

Kuma wadanda suka yanke kauna daga yin haila cikin matayenku idan har kuka yi kokwanton (suna da ciki ko ba su da shi) to iddarsu wata uku ce, haka nan kuma matan da ba sa yin haila (su ma iddarsu wata uku ce), ma'abuta ciki kuma iddarsu ita ce haife cikinsu kana, wanda duk yaji tsoron Allah, (Allah) zai saukaka al'amarinsa.(3)

Wadannan (hukunce hukuncen) umarnin Allah ne da ya saukar zuwa gare ku, kuma duk wanda ya ji tsoron Allah, to Allah zai kankare masa munanan ayyukansa kana ya girmama masa lada.(4)

"Mafifici daga cikinku shi ne wanda ya fi kyautata wa iyalinsa kana ni na fi ku kyautata wa iyalina."(5)

Kuma akwai ruwayoyi da ke nuna mana karara irin illar da ke tattare da rashin yin tsabtar ma'aurata.

An karbo daga Imam Sadik (A.S.) yana cewa: "Hakika mata sun fita daga kame kansu zuwa ga yin lalata, ba komai ya sa suka auka zuwa ga lalata ba face karancin tsabtan mazajensu."

Wannan ruwayar ta zo cikin Makarimul Akhlak shafi na 91-107.

Ku zaunar da su (wadannan mata da kuka saka) a inda kuke zaune gwargwadon karfm wadatarku, kada ku cutar da su domin ku takura musu (har su gudu daga gidan), (amma) idan sun kasance ma'abuta ciki to ku ciyar da su har [ sai sun haife cikinsu kana idan suka | shayar muku da ('ya'yanku) to ku biya su ladan shayarwarsu, (sannan  dangane da dan da za'a shayar) ku yi kyakkyawar shawara wacce ta dace a tsakaninku, idan kuma har  (shawarar) ta ci tura, sai wata matar daban ta shayar masa da dan.(6)

(Kana dangane da ciyar da wadanda  aka saka) Mawadaci lallai ya ciyar daga wadatar da yake da ita, duk  wanda kuma aka kuntata masa  arzikinsa (wato talaka) to lallai shi  ma ya ciyar daga abin da Allah ya ba  shi, Allah ba ya kallafa wa wani  bawa face gwargwadon ikon da ya ba shi, (domin) ba da dadewa ba  Allah zai kawo  sauki bayan tsanani.(7)

 Akwai da yawa daga cikin birane da alkaryu wadan da mutanensu suka kangare wa umarnin Ubangijinsu da  manzanninsa sai muka yi musu hisabi matsananci kuma muka yi musu azaba ta ki .(8)

Sannan suka dandani musifa, kana karshen al'amarinsu ya kasance tabewa.(9)

(Asakamakon sabawar da suka yi wa umamin Ubangji sai allah ya tanadar musu azaba mai tsanani, (to don haka) ya ku masu hankalin da kuka yi imani kuji tsoron Allah, domin hakika Ubangiji ya saukar da abin da yake tunatarwa a gareku.(10)

Ya aiko muku da Manzo, wanda yake karanta muku ayoyin Allah mabayyana don ya fitar da wadanda  suka yi imani kana suka yi aiki na gari daga nau'oin duhu zuwa ga haske duk wanda ya yi imani da Allah kana ya yi aiki na gari to Allah   zai shigar da shi gidajen Aljanna    I wadanda koramu ke gudana a karkashinsu, suna masu dauwama a cikinsu har abada, hakika (duk wanda ya shiga cikin Aljanna to) Allah ya kyautata masa arziki.(l 1)

Allah shi ne wanda ya halicci sammai bakwai kana ya halicci kasa kwatankwacinsu (wanda kuma a ko da yaushe) umaminSa na sauka a tsakaninsu (sammai da kassai) don ku san cewa hakika Ubangiji mai iko ne kan kowane abu kana ku san cewa lallai ilimin Allah ya kewaye dukkan komai.(12)

Rabi'ul Mu'uminina