Hijabi Lullubin Musulunci

A- Gabatarwar Mawallafa

Hakika Musulunci ya haifar da gagarumin sauyi a tarihin mace, wadda har ya zuwa yau ba a samu na biyunsa ba. Domin ta hanyar sa ne, ta samu damar dawo da mutunci da hakkokinta da aka raba ta da su a karkashin zaluncin zamanin jahiliyya na karnoni da dama. Ta haka ne Musulunci ya kwato mata hakkokinta ta yadda za ta yi rayuwa cikin mutunci karkashin tsarin rayuwa mafificiya.

A karo na farko a tarihi, mace ta samu damar amfana da hakkokinta na dan'Adamtaka a karkashin tsari da dokoki irin na Musulunci. An yaye wa mata kangin zalunci, kana kuma ta samu damar rayuwa a matsayin dan'Adam mai mutunci, daukaka kana mai matsayi kamar dai-dai da na namiji. To amma fa dole ne wannan 'yanci ya kasance cikin iyakokin Allah Madaukakin Sarki Wanda Ya ba wa mace dama, kana kuma Ya tsara mata hanyar da za ta iya ba da nata gudummawar wajen gina rayuwa, daukaka, tabbatar da gaskiya da kuma yada alheri.

To hakika wannan kuduri zai kasance ne kawai kamar wani mafarki da tatsuniya a wajen wadansu, idan har ba a karfafa shi da wasu ayoyi na Alkur'ani mai girma da hadisan Annabi da kuma Mutanen gidansa (Ahlulbait) tsira da amincin Allah su tabbata a gare su ) ba.

(1) A zamanin jahiliyya, al'umma tana ganin mace a matsayin wata bi-tsami, wani abu na la'ana, matatta-rin muggan ayyukan shaidan, ko kuma sukan kwatanta ta da matsayin wata dabba da aka halicce ta a yanayin dan'adam. To amma ko da Alkur'ani ya zo sai ya karyata wannan kuduri, wanda ya saba wa gaskiya da kuma hakika. Ya ci gaba da nuna cewa namiji da mace wasu irin 'yan tagwaye ne da suka fito daga mabubbuga da kuma manufa guda.

" Ya ku mutane ! ku bi Ubangijinku da takawa, Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza masu yawa da mata....." ( Surar Nisa'i: 4:1)

" Shi ne Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya sanya daga gare ta, ma'aurata, domin ya natsu zuwa gare ta...." (Surar A'araf: 7:189)

"Kuma Allah Ya sanya muku matan aure daga kawunanku, kuma Ya sanya muku daga matan aurenku diya da jikoki...."(Surar Nahali: 16:72)

Bayan bayyana matsayin mace a rayuwa da kuma samuwar dan'adam a fili, Alkur'ani mai girma ya yi kakkausar suka ga al'adar nan ta bisne 'ya'ya mata da rai, wato Wa'id[1]

"Kuma idan wadda aka turbude ta da rai aka tambaye ta, saboda wani laifi ne aka kashe ta?"(Surar Takawir:   81:8-9)

Kana kuma ya kawo karshen zamanin da ake kange mace daga aure har sai ta biya kudin fansar kanta ko kuma cikin zalunci a gaje ta bayan mutuwarta.

" Ya ku wadanda suka yi imani ! ba ya halalta a gare ku, ku gaji mata a kan tilas. Kuma kada ku hana su aure domin ku tafi da sashen abin da kuka ba su...."(Surar Nisa'i: 4:19)

Sannan kuma ya yaye musu irin zalunci da wulakanta su da mazaje suke yi. Don haka ne ma Alkur'ani ya ba da muhimmanci mai girman gaske kan tausaya musu yayin mu'amala da su:

"....Kuma ku yi zamantakewa da su da alheri. Sa'an nan idan kun ki su, to, akwai tsammanin ku ki wani abu, alhali kuwa Allah Ya sanya wani alheri mai yawa a cikinsa."(Surar Nisa'i: 4:19)

 

Koda yake a da, talauci ma ya kan sa mutane su kashe 'ya'yayensu musamma ma 'ya'yaye mata, don haka Alkur'ani ya kawar da wannan al'amari ( daga kanta):

" Kuma kada ku kashe diyanku saboda talauci, Mu ne Mu ke arzurta ku da su..."(Surar An'ami: 6:151)

Kana kuma Musulunci ya bayyana cewa ma'aunin daukaka ba wai ya dogara kan mazantaka ba ne face kan imani (da Allah) da ayyuka na kwarai. Duk wanda ya aikata wani aiki to zai sami sakamakonsa, shi namiji ne ko mace:

" Lalle, Musulmi maza da Musulmi mata da Muminai maza da Muminai mata, da masu tawali'u maza da masu tawali'u mata, da masu gaskiya maza da masu gaskiya mata, da masu hakuri maza da masu hakuri mata, da masu tsoron Allah maza da masu tsoron Allah mata, da masu sadaka maza da masu sadaka mata, da masu azumi maza da masu azumi mata, da masu tsare farjojinsu maza da masu tsare farjojinsu mata, da masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambatonSa da yawa mata, Allah Ya yi musu tattalin wata gafara da wani sakamako mai girma." (Surar Ahazabi: 33:35)

Kana Musulunci ya ci gaba da nuna cewa muminai sashensu majibincin sashe ne. Sun kasance masu yada alheri a tsakaninsu kana suna umurni da abu mai kyau, sannan suna hani da munana:

" Kuma Muminai maza da Muminai mata, sashensu majibincin sashe ne, suna umurni da alheri kuma suna hani daga abin da ba a so, kuma suna tsayar da salla kuma suna bayar da zakka, kuma suna da'a ga Allah da ManzonSa. Wadannan Allah Zai yi musu rahama….." ( Surar Tauba : 9:71)

Hakika Musulunci ya tsaya wajen bayyana irin yanayin mu'amalar da ke tsakanin mace da namiji ta hanyar aure :

" Su tufa ne a gare ku, kuma ku tufa ne a gare su…." (Surar Bakara: 2: 187)

" Kuma akwai daga ayoyinSa, Ya halitta mu ku matan aure daga kanku, domin ku nitsu zuwa gare su, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku..." (Surar Rumi : 30:21)

Baya ga tsara dokoki kan hakkokin da 'yancin mace, hakika Alkur'ani mai girma ya mai da hankali kan wajibcin girmamawa da kuma kulawa gare ta, kana da kuma bata cikakkun hakkoki da 'yancinta.

Manzon Allah, Muhammad (s.a.w.a ) yana cewa :

"Babu wadanda za su girmama mata, face masu mutunci, kana babu wadanda za su cutar da su face marasa mutunc[2])"

"Kada ku nuna bambanci wajen kyauta a tsakanin 'ya'yayenku, hakika da za a ba ni zabi wajen taimako, lalle da na zabi mata ( don taimaka musu)[3]"

"Ba na tsammanin mutum zai samu karuwa a imaninsa, ba tare da kaunar mata sosai ba[4]"

Sannan bugu da kari, akwai tsarkakan nassosi masu yawan gaske da suke kira da a tabbatar da mace a kan matsayin da take da shi a cikin al'umma.

Kana kuma Musulunci ya ba da wasu muhimman abubuwa ga mace. Ya tsara mata sutura ta musamman don tabbatar da daukakarta da kuma kare mata mutuncinta daga lalacewa da rugujewa. Don haka ana iya cewa ta hanyar hijabi (Lullubin Musulunci), Musulunci ya sami cim ma manyan manufofi guda biyu:

 

Na farko, ya kare mata akidarta, yayin da take aikata abubuwan da suka hau kanta na wajen ba da gudummawarta ga al'umma, ci gaba da kuma Sakon Musulunci da kuma gudanar da al'amurran da suka shafi rayuwarta gwargwadon yadda Musulunci ya tsara.

Na biyu, yana kare tsarkakan mace da kuma toshe duk wata hanya da za ta kai ga aikata duk wani aiki da zai kai ta ga fadawa ga munanan ayyuka; ko kuma ya juya ta ta zama wani makami da ke lalata al'ummar da take rayuwa a cikinta -kamar yadda yake faruwa a kasashen Turai -. Baya ga irin nasarar da hijabi ya samu wajen kare mace da kuma tsara mata irin suturar da za ta sa da kuma haramcin da Musulunci ya yi na cakuduwan (mata) da wadanda ba muharramansu ba, da dai sauran ka'idoji, za mu ga irin matukar kokarin da Musulunci ya yi wajen kare namiji da mace, da kuma dukkan al'umma, daga yaduwar munanan ayyuka da kuma rayuwar da ba ta da amfani.

Dangane da wadannan ka'idoji da dokoki, Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:

Dangane da wadannan ka'idoji da dokoki, Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "Ka ce wa Muminai maza da su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjojinsu, wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah Mai kididdigewa ne ga abin da suke sana'antawa. Kuma ka ce da Muminai mata da su kawar da idanuwansu kuma su kiyaye farjojinsu, kada kuma su fito da adonsu sai dai abin da ya bayyana daga gare shi, kuma su dora mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna kawarsu face ga mazajensu ko ubanninsu, ko ubannin mazajensu, ko diyansu, ko diyan mazansu ko 'yan'uwansu, ko diyan 'yan-'uwansu mata ko matansu, ko abin da hannayensu na dama suka mallaka, ko mabiya wasun masu bukatar mata daga maza, ko jarirai wadanda ba su tsinkaya a kan al'aurar mata. Kuma kada su yi duka da kafafunsu, domin a san abin da suke boyewa daga kawarsu. Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba daya, Ya ku Muminai!, tsammaninku ku sami babbar rabo". (Surar Nuri: 24:30-31)

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, kana tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammadu (s.a.w.a) da Mutanen gidansa tsarkakku (a.s.).

                                                                                     MU'ASSASAR AL-BALAGH

B- Kalmomin Da Aka Yi Amfani Da Su A Wannan Bincike

 

  1. Lullube mata a zamanin Jahiliyya: Wato kange mata daga musharaka cikin rayuwar al'umma da kuma hana ta 'yancinta.
  2. Hijabin Musulunci: wato irin sanya tufafin da Musulunci ya yarda, wanda yake rufe dukkan jikin mace, amma ban da fuskanta da tafukanta.
  3. Mahram: Muharrami yana nufin 'yan-'uwan mace da namiji wadanda aure ya haramta a tsakaninsu, kamar iyayen mutum, 'yan'uwa maza, 'yan'uwa mata, kawunnai,gwaggwannai, dan dan-'uwa ko 'yar'uwa, 'yar dan'uwa ko 'yar'uwa, kakan-ni, jikoki da sirikai.
  4. Ajnabi ko Ajnabiyah (jam'insu shi ne ajanib ko ajnabiyat): Su ne wasun wadancan da aka ambata a sama wadanda aure ya halalta a tsakaninsu, misali 'ya'yan kawunnai ko gwaggwannai, ko kuma sauran dangi da bare. Ko kuma su ne wadanda babu wani haramci na Shari'a kan auratayya tsakaninsu.

 

1- Hijabin Musulunci: Yanayi Da Kuma Ma'anarsa

GABATARWA

Hakika an cutar da mace ta manyan hanyoyi guda biyu, wadanda hakan su ne manya abubuwan da suka haifar da keta, wahala da zaluncin da suka faru gare ta cikin tarihi.

Abu na farko shi ne irin ganin da ake yi wa mace a matsayin wata wulakantacciyar halitta da maza kan mallaka don biyan bukatunsu na jima'i, kana a dai-dai wannan lokaci kuma ita ba wata aba ba ce face kawai wata na'ura ta haifuwar yara. Kana kuma ana kwatanta ta da cewa wata rumbu ce ta ajiye gudan jini. Kana wasu siffofin da ake fadi game da mace suna nan kamar haka: ana ganinta cewa shaidan ce cikin rigar dan'Adam, ko kuma hanya ta rashin biyayya a rayuwa….da sauransu. To amma babbar manufar duk wadannan abubuwa ba kome ba ne face kawai a wulakanta ta, bautar da ita da kuma kwace mata 'yanci da hakkokinta, kana da kuma kange ta daga musharaka cikin al'amurran yau da kullum.

Hakika, tarihin mace yana cike da surorin irin azabtarwa, wahalhalu da zaluncin da ya faru gare ta kamar yadda za mu yi cikakken bayani nan gaba.

Abu na biyu kuwa shi ne, ana ganin mace a matsayin wani abu ne kawai na jin dadin jima'i da kuma ribar duniya. Wannan mahanga kuwa ya samu asali ne daga irin al'adu da wayewa da ci gaban mai tonon rijiya na kasashen gabashin duniya (Turai). Domin idan har tsohon mahangan da ake wa mace na ganinta a matsayin wata wulakantacciya, kana mara wayewar halitta, wacce aka zalunta ta hanyar kwace mata 'yancinta, to ita kuwa sabuwar jahiliyyar wannan zamani sai ta yi mu'amala da ita ta hanyar da ya haifar da lalacewa da 'yancin zina ga mace. Hakika an yi amfani da hanyoyi daban-daban wadan-da suka hada da hanyoyin wayar da kai, makarantu, gidajen sinimomi, hanyoyi na dabara, dokoki, wasu tsare-tsare na siyasa na Turai da kasashen gabashin duniya don dasa wannan mahanga da kuma karfafa ta. An bi hanyoyi da matakai da dama wajen yada zinace-zinace, wanda hakan ba wai kawai ya tsaya ga zubar da mutunci da kimar mace ba ne, a'a, har ma da lalata al'umma da kuma zubar da kimar dan'adam a irin wadannan al'ummomi. Sannan daya daga cikin abubuwan da wannan al'amari yake haifarwa shi ne yaye mace da tura ta zuwa ga zinace-zinace ba tare da la'akari da kunya ko kuma wata doka ta Ubangiji ba.

Hakika wadannan irin zalunce-zalunce da wahal-halu da kuma zubar mata da kima da mutunci ya samu asali ne daga hanyoyi guda biyu: Hanyar Tsohuwar Jahilliya da kuma ta Sabuwar Jahiliyyar wannan zamani.

Lalle cikin tarihi, mace ba ta yi sa'a da kuma gamon katar da wani sako ko addini da ya kare mata mutuncinta, daidaitawa da kuma kiyaye matsayinta cikin al'umma ba, face addinin Musulunci, wannan sako na Allah Ta'ala, Ubangijin talikai. Don haka hijabi, kamar yadda wannan addini ya yi umurni da shi, ya kasance daya daga cikin hanyoyin tabbatar da irin wannan kulawan ta Ubangiji ga wannan madaukakiyar halitta kamar yadda za mu gani nan gaba.


2- Ka'idoji Biyu Kan Hijabi Mace.

Dangane da hijabi ga mace da kuma dangantakarsa da irin al'ummomin da suke kewaye da ita, hakika akwai manyan mahanga guda biyu kan kalmar hijabi cikin karnonin da suka gabata.

2- Mahangar Lokacin Jahiliyya Kan Hijabi.

Hakika kafin bayyanar Musulunci tsohuwar jahi-liyya ta samu daman kafa munanan manufofinta cikin tarihi, kana kuma mata sun dandani mummunan yanayi na zaluncin irin wancan lokacin. A wancan lokacin al'amari ya munana ta yadda aka kwace wa mace 'yancinta inda har ya kai ma ana ganinta kawai a matsayin wata haja ce ta saye da sayarwa, karkashin irin wannan mummunan tsari. An kwace mata kimarta na dan'Adamtaka, kana aka juya ta ta zamanto wata halitta kawai da mazaje suke amfani da ita don jin dadi, ko kuma a wani lokaci ma a matsayin baiwa. Lalle koma dai mene ne za a fadi a matsayin shi ne abin da ya sanya mazaje suka shafe matsayin mata da kuma zaluntarsu a rayuwa a wancan lokaci da ya gabata, shin hakan ya faru ne saboda dalilai na tattalin arziki, sha'awa ko kuma dalili na ruhi ko addini, to al'amarin dai a fili yake, shi ne cewa shi wannan tozartarwa ga mace da kuma kwace mata hakkokinta, wannan kwace mata kimarta na dan'Adamtaka ya kai wani matsayi da mutumin wannan zamani ba zai iya suranta shi ba.

Zaluncin da ya faru ga mata yana yawo ne tsakanin wadannan al'amurori na haramci da wa'id da kuma abin da ke tattare da na mummunan akidu da dabi'u wadanda suke da yawa.

Zaluncin da ya faru ga mata yana yawo ne tsakanin wadannan al'amurori na haramci da wa'id da kuma abin da ke tattare da na mummunan akidu da dabi'u wadanda suke da yawa.

Wadansu kuma suna ganin mace a matsayin shaidan ne cikin tufafin dan'Adam, don kawai ta bauta wa namiji, kana ya samu biyan bukatunsa ta hanyarta, kamar yadda mutanen Jahiliyya suke gani.

Wasu kuwa suna daukan cewa jikinta na mutum ne, amma ranta na dabba ne. Wannan ra'ayi ya samo asali ne daga kasashen Turai kafin sauye-sauyen da aka samu.

To mai karatu, ya rage maka ka sauwara irin babban bala'in da ya faru ga mace, lokacin da ake ganinta a matsayin shaidan ko kuma wata dabba ko kuma wata haja abin sayarwa kamar sauran kayayyaki.

To wadannan su ne wadansu daga cikin irin wahal-halun da mace ta fuskanta karkashin irin wadannan munanan akidoji.

Lalle Alkur'ani mai girma ya ambaci wasu daga cikin wahalhalun da suka sami mace a karkashin al'ummar Jahiliyya ta Larabawa wanda kuma Musu-lunci ya yi kakkausar suka gare su:-

"Kuma idan aka yi wa dayansu bushara da mace, sai fuskarsa ta wuni baka kirin, alhali yana mai cike da bakin ciki. Yana boyewa daga mutane domin munin abin da aka yi masa bushara da shi. Shin zai rike shi a kan wulakanci, ko zai turbude shi a cikin turbaya? To, abin da suke hukumtawa ya munana".(Surar Nahali : 16:58-59)

"Kuma kada ku kashe 'ya'yayenku domin tsoron talauci. Mu ne ke arzurta su, su da ku. Lalle ne kashe su ya kasance kuskure babba". (Surar Isra'i : 17: 31)
"Kuma idan wanda aka turbude ta da rai aka tambaye ta : saboda wane laifi ne aka kashe ta". (Surar Takawiri : 81: 8-9)

Kana kuma an ruwaito Annabin rahama (s.a.w.a) yana cewa:

"Wata rana wani mutum mai suna Qais bin Asim al-Tamimi, ya zo wajen Manzon Allah (s) ya ce: " a lokacin Jahiliyya na kasance na bisne 'ya'yayena mata guda takwas....[5]" .

Hakika za'a iya bayyana zamanin Jahiliyya na larabawa kafin zuwan Musulunci kamar haka :-

"An kasance ana bisne 'ya'yaye mata cikin mummunan yanayi; a kan bisne jariri da rai ! sukan yi amfani da hanyoyi daban-daban wajen gudanar da wannan al'ada. Idan aka haifa wa daya daga cikinsu diya mace, to sukan bar ta har na tsawon shekaru shida. Daga nan sai mahai-finta ya yi umrnin da a yi mata ado a shafa mata turare da karyar cewa zai kaita wurin danginta ne ! To amma a dai-dai lokacin an riga an tona mata wani rami cikin rairayin sahara. A lokacin da suka isa sai mahaifin nata ya ce mata ta leka ramin, nan take sai ya tura ta cikinsa , kana ya rufe ta da kasa !

Wasu kuwa sukan yi amfani da wannan hanyar :- Wato lokacin da nakuda ta kama mace sai ta je ta zauna a bakin wani rami (da aka riga aka tona). Idan har ta ga abin da ta haifa mace ce, sai ta jefa ta cikin ramin, kana ta rufe ta da kasa. Idan kuwa namiji ne, sai ta dauke shi zuwa gida !

" Kana wadanda ba sa so su bisne 'ya'yayen nasu mata, sai su barsu cikin wulakanci har su kai shekarun da za su iya yin kiwo, to sai a sanya musu riguna masu gashi a tura su rairayin sahara don kiwon rakuma !

"Sannan wadanda ba sa so su tura ta kiwo, sai su yi amfani da wasu muggan hanyoyi don wulakanta ta. Misali idan yarinyar ta girma ta isa aure sai a yi mata aure, idan mijin nata ya mutu sai uban (waliyin) nata ya zo ya sanya mata wasu irin tufafi na musamman wadanda ke nuna cewa ba ta da wani 'yancin yin aure ba tare da yardar uban nata ba. Ta haka ne za a tilasta mata yin aure ba tare da sonta ba ! To idan shi uban nata ba ya son ya aure ta, to za ta zauna nan a daure har ta mutu, kana kuma sai ya gaje ta. Idan kuwa har tana son ta fanshi kanta daga irin wannan hali, dole ne sai ta bayar da wasu kudade don ta 'yantar da kanta.

" Wasu kuwa sukan 'yantar da matan, amma fa da sharadin ba za su taba yin aure ba sai dai da izinin waliyin nasu, ko kuma dole ne ta biya diyya. Wasu kuwa sukan ajiye bazawarai wadanda mazajensu suka mutu har sai wani daga cikin 'ya'yayensu kanana ya girma kafin su aurar masa da ita.

" Dangane da mace marainiya kuwa, sukan ajiye ta ne a wajensu kana su hana ta aure da burin cewa za su aure ta lokacin da matayensu suka mutu, ko kuma su sanya ta ta auri daya daga cikin 'ya'yayensu don saboda su sami dukiyarta....[6]

Su kuwa Girkawa, suna ganin mace a matsayin wata doluwar halitta ce da bata da wani 'yanci guda-nar da duk wani al'amari.

Hatta wasu daga cikin falasafofin kasar Girka sun dauki kulle mace a cikin gida, kamar sanya ta cikin kurkuku ne. Wani mashahurin mai hikima na kasar Girka, Yosteen cewa yake:

" Muna auren mata ne kawai don su samar mana da halaltattun 'ya'yaye".

"Su kuwa Romawa, suna ganin matayensu a matsayin wani kaya maras kima da namiji ya mallaka. Sukan tafiyar da ita kamar yadda suke so. Sun taba yin wani taro a daya daga cikin majalisosinsu a birnin Roma don su tattauna kan al'amarin mata. Inda daga karshe suka kai ma natijar cewa ita (mace) kawai wata halitta ce da bata da kwakwalwa, kana kuma ba ta da wani rabo a rayuwar lahira. Ita kawai wata juji ce, ba za ta ci nama ba kana ba za ta yi dariya ba ko kuma bakin fadin wani abu ba. Dole ne ta tafiyar da rayuwarta cikin bauta da biyayya.

"Wasu daga cikin 'yan majalisar masanan Romawa sun fitar da wata doka da ta haramta wa mata mallakan fiye da rabin miskali na zinare. Dole ne ta sanya tufafi masu launi daban-daban kana kuma ba za ta yi tafiya a cikin keken dawaki na fiye da mil guda a wajen garin Roma ba sai dai in lokacin wani buki ne na gaba daya[7]"

Yayin da tarihin Turai yake magana kan kasar Girka ya nuna cewa a wani lokaci Bagirke guda ya kan ajiye mataye dari a gidansa.

Kana tsohon tarihin Iran ya bayyana faruwar wasu al'amurra makamantan wadannan na zamanin Jahilli-yar larabawa da kuma tsofin al'adun Turai. Idan ma dai akwai wani banbanci tsakaninsu to sai dai irin na bayani. A matsayin misali, yana da kyau mu yi dubi ga wadannan abubuwa:

"A zamanin da a Iran babu wani mutum da yake kange matayensa daga sauran mutane[8].

"Khosrow Parviz (wani sarkin gidan sasaniyawa) ya mallaki mataye kimanin 3000 a

cikin fadansa, amma da haka ba su ishe shi ba. Domin duk lokacin da ya ke so ya kawata fadarsa, to sai ya rubuta wasika zuwa ga gwamnoninsa a inda zai ba su siffofin irin macen da yake so. A nan take za su kawo masa irin wannan mace da ya siffanta[9]"

A wasu shekaru da suka gabata a kasashen Turai, mutane suna da kuduri kamar haka:

Mace ba wai kawai wata alama ce ta rashin da'a, kana kuma matattarar muggan abubuwa da lalacewa ba ne kawai, face ma dai ita ce asalin duk wani bala'i da ka iya samun dan'Adam. Ita ce ummul aba'isin din duk wani tashin hankali da wahala ga mutanen da suke bayan kasa. Sannan wani daga cikin Paparomo-min farko mai suna Tirroliyan ya yi cikakken bayani kan matsayin Kiristanci dangane da mata. Ya ba da gurbataccen ra'ayin Kiristanci dangane da mace; ita ce hanyar da Shaidan yakan bi wajen shiga ruhin mutum. Ita ce wacce ta ingiza mutum zuwa ga haramtacciyar bishiyar nan (da aka hana Annabi Adamu (a.s) cinta), aka saba wa umurnin Allah, wannan ita ce mace[10]".

Dangane da matsayin mace a shekarun da suka wuce ne, malamin falsafan nan na Biritaniya Herbert Spinser yake fadi a cikin littafinsa na "Describing Sociology" cewa: Hakika a karni na sha daya a Birtaniya, a kan sayar da mace (ga wanda zai aure ta) kana kuma a dai-dai wannan lokacin kuma sai kotuna, wanda dama su ke karkashin majami'ai ne, suka kafa wata doka wacce ta ba wa shi mijin daman chanzata ko kuma ba da hayar matar tasa ga wani namiji daban na wani kayyadad-den lokaci"[11] .

Lalle kan wannan mummunar dabi'a ga mace wanda ya hada da tsoratarwa, kulle ta a cikin gida da kuma kange ta daga duk wani nau'i na rayuwa da jin dadi, domin kuwa tarihi ya hakaito kange mace da aka yi, wato kange ta daga taka rawa cikin al'amurran rayuwa, da kuma hana ta 'yancin da take da shi.

Hakika irin wannan bakar akida ta kange mace da ya faru a zamanin jahiliyya, da kuma duk fadin duniya har da kasar Iran (ta wancan lokacin), Indiya, Masar, Turai da kuma kasashen larabawa kana da kuma irin yadda ake tafiyar da mace, shi ya ba da dama wajen kirkiro kungiyoyin kira ga kwato wa mata hakkinsu. To amma irin lamurran hijabi da kuma kula da mace da Musulunci ya zo da shi, ya saba wa irin kangewar lokacin harem, wa'id da kuma lokacin cinikin bayi inda mata suka wahala da gasken gaske.
.
Mahangar Musulunci Dangane Da Hijabi

Hakika, irin nau'in hijabi (kangewa) da Musulunci ya dauka, nesa ba kusa ba, ya saba wa irin nau'in kangewar zamanin Jahiliyya da kuma mummunan irin yanayin da ya wanzu a fadojin wasu sarakunan Umayyawa da Abbasiyawa dangane da amfani da mata don cim ma burinsu na sha'awa. Kai hatta ma dai hakikanin wannan kalma ta hijabi, ba ta shiga rayuwar Musulmi ba face kwanannan. To koma dai mene ne za a ce dangane da mace, al'amarin dai guda ne cewa saboda irin muhimmancin da Musulunci ya bawa mace, shi ya sa har ya tsara mata wani irin nau'in tufafi, wanda haka yana nuna irin girma da daukakan da Musulunci yake ganin mace tana da shi, da kuma kula da tsabtarta.

Lalle dai a Musulunci, da kuma duk abin da ya kunsa, babu wata doka ko ka'ida da ta hana mace musharaka cikin al'amurran rayuwa, ko kuma ya tsare ta a cikin gida kamar yadda ya faru a zamanin Jahiliyya. Hatta ma dai wannan kalma ta hijabi kwanan nan aka fara amfani da ita cikin akidar Musulunci[12].

Bugu da kari kan irin tufafi na musamman da mace take sa wa yayin da za ta fita daga gidanta- kamar yadda za mu yi bayani nan gaba- to Musulunci ya yi amfani da kalmar "sitr" (lullubi) ne ga wannan irin aiki.

Hakika Musulunci ya wajabta wa maza da mata da su kawar da idanuwansu daga kallon juna, face dai matayensu, mazajensu ko kuma muharramansu. A bangare guda kuma, Musulunci ya wajabta wa mace sanya hijabi, kana a daya bangaren kuma ya sanya wasu dokoki ga shi ma namijin.

Idan har an tsara wa mace wani nau'i na tufafi don ta kare kyawun jikinta; to shi kuma namiji a daya bangaren, an wajabta masa kawar da idanunsa daga kallon mataye, face dai muharramansa da kuma kare farjinsa.

Don samun daidaituwar wannan kalma ta hijabi da ainihin manufan Musulunci da kuma abin da yake nufi, to yana da kyau mu yi bayanin cewa: Lullubi da kamewa a Musulunci ya hada da maza da mata ne; to amma yanayinsu ya sha banban ne ta yadda dai za su iya kiyaye kyawawan dabi'u, kare dabi'u da kuma girmama matsayin mace a dukkan rayuwa. Domin shi Musulunci ba ruwansa da tsarewa ko kuma kange mace daga tafiyar da 'yancin da Allah Ya bata, kana a cikin tsari da ka'idojinSa, babu cutarwa da kaskantar da darajar mace. Hakika ya zamanto abin alfahari ga Musulunci, cewa saboda tabbatar dokokinsa ne aka kawo karshen yanayin wulakanci da bautar da mata, da mazaje suke yi a zamanin Jahiliyya, wanda ya bakanta tarihin dan'Adam, kafin bayyanar Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma sakonsa.

A takaice za a iya fassara hijabi (lullubin) Musulunci da cewa wani irin nau'i ne na sutura da kuma takaita alaka tsakanin maza da mata, wadanda ba muharraman juna ba, da sanya mace a tsarkakakken tafarki na girmamawa da kuma tabbatar mata da 'yancinta.

Me Ya Sa Hijabi Kawai?

Muna fatan an fahimci irin bayanin da muka yi dangane da bambancin da ke tsakanin hijabi (kange-wa) irin wadda aka dauka a zamanin jahiliyya danga-ne da mu'amalolin mace, da kuma hijabin da Musu-lunci ya dauka a matsayin garkuwa da zai kare mace daga zalunci da tozarta kimarta da wasu wawaye ke yi.

Abin da ya saura kawai shi ne mu yi bayani kan babban dalilin da Musulunci ya dogara da shi wajen tsara wa mace wani irin tufafi daidai da yadda Allah Ta'ala yake so ga bayinsa.

To don saboda bayani kan wannan babban dalili ko manufa, ba tare da tsawaitawa ba, bari mu ambato wadan-nan abubuwa:

Da farko, akwai mahanga guda biyu dangane da mu'amala tsakanin namiji da mace:

Mahanga ta farko tana ganin mutum yana iya saduwa (jima'i) da kowace mace a cikin al'umma, kuma yin hakan ba zina ba ce.

Mahanga ta biyu kuwa, ta takaita 'yancin jima'in mutum ga matar da suka yi aure ne kawai, kana in ba tare da aure ba, to ba shi da 'yancin saduwa da wata mace.

Wannan mahanga ta farko irin ta ce a halin yanzu ake gudanarwa a Turai.

 

Sannan mahanga ta biyu kuwa ita ce mahangar Musulunci dangane da mu'amala tsakanin mace da namiji.

Wannan shi ne babban jigon wannan al'amari, wanda kuma duk wani bayani daga jikin shi aka ciro. Duk wata dabi'ar mutum dangane da mace an ciro ta ne daga wannan mahanga ta farko, wadda ke da alaka da sha'awarsa ta jima'i da mace a wuraren bukukuwa, tarurruka da wasu mataye da ba matayensa ba da kuma cakuda tsakanin jinsosi, da kuma sanya mace ta zamanto wata abin kawa da burge mazaje da dai sauran abubuwa makamantan haka.

Dangane da mahangar Musulunci kuwa, al'amarin ya kasu kashi-kashi:

Lalle umurnin mace da ta rufe dukkan jikinta, in banda fuskoki da tafukanta, daga idanuwan mazaje, face mijinta da danginta, kana kada ta bata lokacinta wajen zance maras amfani da kuma tafiya da mazaje da makamancin haka, sannan kuma haramta ta keban-tu da wani namiji in dai ba danginta ba, da kuma sauran mu'amaloli da fikihun Musulunci ya yi bayani, da kuma mahangar Musulunci dangane da alakar namiji da mace, duk kariya ce da kuma kiyayewa daga lalacewa da rashin kunya. Hakika idan muka yi la'akari da irin yanayin wadannan ra'ayoyi guda biyu da kuma abubuwan da suka haifar, to lalle za mu kai ga natijar cewa Musu-lunci yana tsananin kishi dangane mutuncin mace da kuma daukakarta, tsarki da girmanta, ta yadda ba za ta zama wata haja abin sayarwa ga mazaje ba.

Don haka, Musulunci yake ba da muhimmanci wajen daidaitawa da tsara alaka irin ta jima'i, kana kuma ya yi kokari wajen toshe duk wata hanyar da wadannan mugayen mutane suke amfani da ita wajen tozarta mace don biyan bukatunsu na sha'awa (da ita) yadda suke so.

Sannan kuma abin da ita wannan mahanga ta jahiliyya, tsohuwar ce ko sabuwar, take son ta cim ma shi ne yin rikon sakainar kashi ga wannan ka'ida don saboda amfanin maza. Babbar matsalar wannan mahanga ita ce cewa ta ginu ne kan amfanin namiji da biyan bukatansa ko da kuwa macen tana iya samun wani amfani!!

Kana idan muka sake yin la'akari da irin girman amfani da ribar da mazaje sukan samu ta bangaren jima'i da tattalin arziki a karkashin wannan mahanga, za mu ga wannan al'amari na haramci da kuma dabi'ar tozarta mace da aka gudanar a zamanin jahiliyya, daidai yake da irin abin da ake gudanarwa a yau da sunan wayewa,
wadda hakan cutarwa ce ga ita mace. Lalle irin iyakance mace da aka yi a sabuwar jahiliyya (ta wannan zamani) kawai ya banbanta da tsohuwar (jahiliyya) ce kawai ta bangaren zahiri da abin da ya fito fili. Amma yana nan dai a matsayinsa na sarka da ta dabaibaye mace, ta hana ta 'yancinta, kuma ta kwace mata ikonta. Don haka namiji ya mai da mace kamar wata kamammiya ko kuma baiwa ta hanyar amfani da hanyoyi daban-daban na kasuwanci, gidajen karuwai, gidajen sinimomi, gidajen radiyoyi da talabijin, jaridu da wuraren nuna kawa don biyan bukatunsa.

Koda yake, a lokacin da wadansu matayen suka fara nuna damuwarsu da irin wahalhalun da suke fuskanta a karkashin irin wannan al'ada ta Turai, to an samu wasu mazaje 'yan kadan wadanda suka mike tsaye don kalubalantar irin wannan bala'i da mata suke fuskanta a Turai, saboda dabi'un wasu mazajen.

Ga wadansu misalai nan da suke nuna irin wuce gona da irin da mazaje suke yi wa mataye da kuma mummunan sakamakonsa:

A kasar Biritaniya, 'yan mata 9 daga cikin 12 - 'yan kasa da shekaru 20 - suna fuskantar fyade da sacewa. To amma jami'an tsaro sun sami daman kama kashi 13 cikin dari ne kawai na daga cikin masu laifin. Kana kuma a 'yan shekaru da suka gabata yanayin aikata laifuffuka ya karu da kashi 84 cikin dari; kana kuma laifuffukan kananan yara ya karu da ninki biyar a watannin farko na shekarar 1975[13]

Wata jaridar kasar Italiya mai suna "Omiga" ta fitar da wasu labarurruka kan irin laifuffukan da aka aikata a wannan kasa inda take cewa:

" Hakika mace Ba'italiya tana tsoron fita daga gidanta, don kare mutuncinta daga lalatattun samari wadanda suke yawo a kan tituna da kuma wadanda ba su da wani aiki face kai hari ga mataye da budurwaye da kuma sace su da nufin yin fashi ko kuma aikata fyade… hakika mace takan ki yarda da duk wani aiki kome daukakarsa, idan dai har aikin zai kai ta ga dawowa gida cikin dare ne, don kada ta sanya mutunci da lafiyarta cikin hatsari"[14].

A wani rahoto da kungiyar Kulawa da Iyali ta kasar Amirka ta buga ta bayyana cewa:

" Lalacewar iyali (aure) wanda ya zamanto ruwan dare, ita ce babbar matsalar da take damun al'umma. Domin a kowace shekara a kan raba auren ma'aurata sama da miliyan daya, wanda haka ya nunka na karnin da ya gabata har sau bakwai."

" Kana yawan shegun 'ya'ya ya karu sau uku in aka yi la'akari da na shekarar 1938, sannan a duk shekara a kasar Amirka a kan haifi shegun 'ya'ya sama da miliyan hudu. Sannan dangane da matsalar lalacewar matasa kuwa wanda hakan yana da alaka da irin rabe-raben aure da ke faruwa, kididdigar ta nuna cewa al'amarin ya nunka na shekarar 1940 har sau uku".

Wani rahoton kuma cewa yake:

"A wani rahoton da Hukumar Binciken Laifuffuka ta Kasar Amirka (F.B.I) ta fitar, ya nuna cewa a cikin irin shari'o'in kisan kai da ke faruwa a tsakanin iyalai, sau da dama mazajen ne ke kashe matayen nasu; kana kuma kashi 15 cikin dari na laifuffukan da suka shafi iyali cutarwar da ke cikinsa tana dawowa ne ga yara kanana ne".

Sannan wata kididdiga da Êungiyar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ta nuna cewa "kashi 60 cikin dari na matan aure a Amirka da Turai sun sami kansu cikin kunci, damuwa da halin kaka-ni-ka-yi"[15].

A lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Dr. Homer wata baturiyar kasar Sweden kan ta yi bincike kan matsayin mata a kasashen Larabawa a shekarar 1975, inda ta sanar cewa:

" Hakika macen kasar Sweden ce, take da bukatuwa da ta nemi 'yancinta, domin kuwa su matan kasa-shen larabawa sun riga sun sami nasu 'yancin tuntuni karkashin addinin Musulunci". Ta ci gaba da cewa: " a wannan lokaci macen kasar Sweden ta yi ta kokarin ganin an bayyanar da wannan shekarar a matsayin "Shekarar Mata ta Duniya" kana kuma a sake bayyanar da wata shekarar a matsayin ta mazaje, don ya samu daman kwato hakkokinsa daga wajen mataye."

Dr. Homer ta ci gaba da cewa: " Kashi 25 cikin dari na matayen kasar Sweden suna fama da ciwon ruhi da na jiki, sannan ana kashe kashi 40 cikin dari na kudin shigar kasar Sweden ne a wajen magance wadannan cututtuka da wannan 'yanci na jeka-na-yika da matayen kasar Sweden suke gudanarwa ya haifar. Hakika, babbar matsalar macen kasar Sweden ita ce irin wannan yanke kauna wanda ya tura ta zuwa ga gabar wani abu mai hatsarin gaske da ke fuskantar rugujewa[16]".

Hakika wannan bakar cuta ta haifar da rugujewar zaman lafiyar iyali a kasar Biritaniya, wanda hakan ya haifar da karuwar adadin zaurawa ko kuma maza da matan da suke zaman daduro. A bisa kididdigar da gwamnatin Birtaniya ta buga a ran 14 ga watan Janairun shekarar 1988, ta nuna cewa yawan haihu-war shegun 'ya'ya ya tashi daga kashi 4 cikin dari a shekara ta 1950 zuwa kashi 21 cikin dari na dukkan haihuwar da aka yi a shekara ta 1986, kana in banda kasar Denmark da take da kashi 43 cikin dari, kasar Birtaniya ce take da adadi mafi yawa a duk kasashen Turai.

Kididdigar da aka yi ta nuna cewa kasar Biritaniya ce take da adadin shika mafi yawa a kasashen Turai, kusan ninki biyu na kasashen Faransa da Jamus.

An gano cewa tsakanin shekarar 1979 da kuma shekarar 1985, adadin maza da matan da suke zama da junansu ba tare da aure ba, ya kusan ninkuwa. Kana a shekarar 1985, kashi 15 cikin dari na dukkan matayen da ba su da aure, har ma da wadanda aka sake su, suna aikata daduro.

Hakika za a iya fahimtar yanayin yadda ake tafiyar da mace a kasashen Turai, wadanda suke ikirarin cewa su ne ma'abuta 'yanci da adalci, daga Taron Duniya Kan Mata da Kafafen Watsa Labarai da aka gudanar a birnin Athens na kasar Girka ran 20 ga watan Nuwamban shekaran 1985.

A wannan taro, daya daga cikin mahalalta taron mai suna, Petra Kelly 'yar majalisar kasar Jamus, ta yi kukan cewa: " A kasar Jamus, suna

tafiyar da mu (matayen Jamus) kamar 'yan tsiraru, wadanda ba su da amfani, musakan cikin al'umma kamar yara. Suna amfani da mu wajen tallen kayayyakinsu kuma suka dauka cewa zaluntarmu ba laifi ba ne. A duk cikin mintuna 15 sai an yi fyade wa wata mace."

Daga baya wannan taro, ya yi kira ga majalisar kasar Girka da ta kafa dokar da ta haramta amfani da mata a talibijin don biyan wata bukata. Ko da yake an tabbatar da ana wulakanta mata a wadannan kasashe, to amma su ma matayen wadannan kasashe da suke ikirarin ci gaba su ne abin zargi. Don kuwa idan mata ba su yarda ba, to da ba a yi amfani da su wajen buga littattafa da finafinan jima'i da kuma tallace – tallace da su tsirara ba.

Wannan kididdiga mai zuwa za ta nuna mana irin yadda wannan al'amari na rugujewar iyali ya zamanto a al'ummomin da ba na Musulunci ba:

A Kasar Faransa

Daya daga cikin aurarraki hudu yana karewa ne ta hanyar shika; a birane ma adadin ya fi haka yana kai wa kashi 50 cikin dari. A kowace shekara kimanin masoya 600,000 ne suke yin aure, 100,000 kuma suke zaban su zauna tare ba

tare da aure ba, kana a kan sami rabuwar aure guda 100,000.

A Kasar Kanada

Kusan kashi 40 cikin dari na aurarrakin fari, sukan kare ne ta hanyar shika. Sannan a tsakanin shekarun 1972 zuwa 1982, an sami ninkuwan wannan adadi har sau biyu.

A Tsohuwar Tarayyar Sobiyet

Kimanin kashi 70 cikin dari na aurarraki sukan lalace ne cikin shekaru goma, dalilan da ke jawo hakan kuwa sun hada da shaye-shaye, rashin kudi da kuma rashin wadatuwa da juna da sirri.

A Kasashen Amirka ta Tsakiya da ta Kudu:

Wata jaridar kungiyar UNESCO ta Majalisar Din-kin Duniya tana cewa sau da dama ana samun 'ya'yaye masu iyaye guda (wadanda suka tashi karka-shin kulawan uwa kawai ko kuma uba kawai) ne ta hanyar irin hijirar da mataye suke yi zuwa birane da kuma samar da 'ya'yaye a aurarrakin da ba jimawa suke yi ba. A dalilan shaye-shaye da kuma gazawar miji wajen samun takamammen aiki, yakan haifar da watsewar iyali da kuma barin uwaye da 'ya'yayensu cikin tsananin talauci da wahalhalu. A duk duniya kasashen da suka fi adadin shegun 'ya'ya su ne kasashen Karebiya, Tsakiya da kuma Kudancin Amirka.

Kasar Sin (China):

Ko da yake adadin shika a kasar Sin yana da karanci a kan da dama daga kasashen Turai, to amma a cikin shekaru biyar, an sami hauhawansa da kashi 70 cikin dari. Mujallar Peiking Review ta kawo rahoton cewa ana samun hauhawar adadin shika a kasar.

Kasar Amirka:

Kimanin rabin adadin aurarrakin da aka yi suna karewa ne ta hanyar shika. Don haka ne ma kashi 60 cikin dari na yaran da aka haifa suna tafiyar da bangaren yarintarsu ne a wajen uwa ko ubansu.

Kasar Japan:

A shekaru ashirin da suka gabata, adadin shika ya ninku kashi biyu. Kafin shekarar 1947, mazaje suna da daman shikan matayensu ko da a kan titi ne. to amma yanzu, kashi 70 cikin dari na shikan, matayen ne suke jawo shi.
Kasar Afirka Ta Kudu:

Kungiyar kwato hakkin matayen Afirka ta Kudu tana cewa a rayuwar daya daga cikin biyun matayen Afirka ta Kudu ana musu fyade. Hakan kuwa ya hada har da kananan yara da tsofi.

Kasar Biritaniya:

Adadin shika a kasar Biritaniya ya dara na kowace kasa a kasashen Yammacin Turai. Kusan mace guda cikin mataye marasa maza guda bakwai masu shekaru 18 zuwa 49, suna zama da wani namiji ba tare da aure ba.

Wata mujallar birnin London mai suna "The Hospital Today", a bugunta na watan Afrilun shekarar1975, ta buga rahoton shekara-shekara na Ma'aikatar Lafiya da Jin Dadin Al'umma ta kasar Biritaniya, inda take cewa:

"…..duk da yawan abubuwan hana daukan ciki da kuma halaccin zubar da ciki, to amma duk da haka an gano cewa kashi 86 cikin dari na yara, mata da ba su da maza ne suke haihuwarsu! A nan gaba akwai babban matsala. A shekarar 1973 an sami wadannan rahotanni kamar haka: an sami rahoto guda na wata yarinya 'yar shekara 11 da ciki; rahotanni guda shida na yara 'yan shekaru 12 masu ciki; rahotanni guda 38 na yara 'yan shekaru13 masu ciki; rahotanni 255 na yara 'yan shekaru 14 masu ciki. Kana kuma a dai-dai wannan shekarar an sami rahoton zubar da ciki har guda 166,000, kashi 50 cikin dari na wannan adadi ya faru ne daga mata marasa aure[17].

Idan muka koma ga gabashin (duniya) kuwa, za mu ga lalacewar al'umma a duniyar kwaminisanci ba boyayyen al'amari ba ne a kan na duniyar 'yan jari hujja. Mujallar "Interphase" a bugunta na watan Afrilun shekarar 1977 ta ba da rahoton cewa:

"Babbar matsalar 'yan Gurguzun kasar Sobiyet ita ce cewa, a yammacin kasar Rasha daya daga cikin aurarraki biyu da suke daurawa yana karewa ne ta hanyar shika. Misali, a birnin Mosko, kusan kashi 49 cikin dari na aurarraki, sukan kare ne ta hanyar shika bayan da aka haifi dan farko. A yankin Mavadanski kawai adadin shika ya kai yawan kashi 72.9 cikin dari. A saboda haka ne ma wani taron kara wa juna ilimi na likitoci da aka yi a Jami'ar Mosko a shekarar 1975, taron ya yi kira da a nemo wata mafita ga wannan matsala ta yawan hauhawar adadin shika da karancin adadin haihuwa[18] ".

Ko da yake ya kamata a gane cewa wadannan matsaloli na iyali sun ta'allaka ne kawai ga garuruwan da ba na musulmai ba ne na Tarayyar Sobiyet. Duk da irin hana gudanar da koyarwa irin ta Musulunci a garuruwan musulmai da suke karkashin kasar Sobiyet daga bangaren 'yan Gurguzu, to amma sai da Musulunci ya ci gaba da tasirinsa a rayuwa da dabi'un musulman wadancan garuruwa, yana mai rage matsalolin iyali da kuma wulakanta mata.

Wadannan bala'o'i da makamantansu, su ne abubuwan da wannan mahanga ta Turai kan mu'amaloli tsakanin maza da mata ta haifar.

A dalilin haka ne, Musulunci ya dauki matakan ruguza tushen lalacewar al'umma da kuma kokarin tsayar da wulakanci da ake wa mata da kwace musu hakkokinsu kana da kuma tabbatar da mutunci da girmamawa a cikin rayuwar 'yan 'Adam.

Don haka, hijabi yana daga cikin mashahuran abubuwan da Ubangiji Ya yi amfani da su wajen kare mutuncin mace da kuma gina tsarkakakkiyar al'umma.

Za mu iya ganin irin halin da ke wanzuwa a da dama daga cikin kasashen musulmai wadanda suka maye gurbin koyarwar Musulunci da na kasashen Turai. Al'ummar wadannan kasashe sun kaurace wa ka'idojin Musulunci, wadanda suka hada har da hijabi, inda suka dauki halayen kasashen Turai a matsayin abin koyi. Don haka ne shika, karuwanci, shaye-shayen giya da muggan kwayoyi, kana da kuma bullar cututtuka irin su ciwon kanjamau (AIDS) da dai sauransu, suka buwayi wadannan al'ummomi da suka zabi su bijire wa ka'idojin addininsu. Kana kuma suka halalta haramtacciyar mu'amaloli tsakanin samari da 'yan mata, maza da mata kuma alal akalla ana iya cewa suka yi musu rikon sakainar kashi.

To amma a kasashen musulmai wadanda al'umma da gwamnatocinsu suka kasance suna bin ka'idojin Musulunci, akwai karancin afkuwar keta alfarmar mata, rashin kunya, shika da sauran muggan ayyuka. Ginshikin iyali yana da karfin gaske, mataye ba sa da sauran tsoro kana kuma suna cikin aminci wajen yawo a kan tituna da kasuwanni.

To a nan wani tsari ne ya fi? Shin za mu zabi takaitaccen 'yanci ne, wanda daga karshe yake haifar da rugujewa da rashin samun nasara, ko kuma tsarin da ke kai wa ga kiyaye al'umma, sannan wanda yake kare namiji da mace ba tare da nuna wani bambanci ba?

Masana kimiyya ta hanyar binciken rayuwar dan'Adam sun gano cewa, an halicci mutum da wasu sha'awoyi guda biyu:

(A)- Su ne sha'awoyin da suke bijirowa da kansu ba tare da tasirin wasu abubuwa daga waje ba, kamar sha'awar abinci, sha'awar nuna kansa ga sauran mutane da kuma sha'awar mallaka da dai sauransu.

(B)- Su ne sha'awoyin da duk da suna nan tare da mutum, to amma ba sa bijirowa sai wasu abubuwa daga waje sun motsar da su.

Daga cikin muhimman irin wadannan sha'awoyi, akwai: Sha'awar jima'i, wanda wakoki da littattafan batsa da tsiraici da dai sauransu suke haifar da ita.

Musulunci, wannan addini na Ubangijin talikai, Mahalicci, Masanin kome, yana da cikakkiyar masaniya kan mafi karancin al'amurran da suke tankwara dan'Adam da kuma hatsarin da ke tattare da rayuwar mutum a duk lokacin da ya ketare haddin da aka sanya masa. Wanda idan da zai bi shi, da zai samu daman daidaita wadannan sha'awoyi a duk bangarorin rayuwarsa.

Saboda masaniyar Musulunci kan wadannan al'amurra ne, ya sa ya haramta motsa wadannan bakaken abubuwa da suke motsa sha'awa.

Don kiyaye wannan bukata, Musulunci ya sanya wadansu tsarurruka na zamantakewa, tattalin arziki da siyasa. Wadannan tsarurruka sun haifar da kyakkyawan yanayi na yarda tsakanin wadannan bukatu na cikin dan'Adam da kuma bukatun sauran jama'a da kuma al'ummar da yake raye a ciki.

Wannan tsari na Musulunci kan hijabi da kuma kyautata alakar da ke tsakanin namiji da mace, an gina shi ne a bangare guda don kiyaye daidaituwan da ke tsakanin bukatuwan mutum da kuma babban burinsa na tsarkake da kuma kiyaye alakar da ke tsakanin wadannan jinsuna guda biyu a daya banga-ren. Don haka, hijabi ya kasance wani asasi ne da ke da alaka da yanayin rayuwar dan'Adam, bugu da kari kan kiyaye kyawawan dabi'u kana kuma tsarkaka da kuma tsara rayuwar al'umma dai-dai da koyarwar Musulunci.

Musulunci, ta hanyar tsara hijabi ga mata, ya takaita yanayin alakoki tsakanin wadannan jinsuna biyu ta mafi kyan tafarki. Kana ya tafiyar da namiji da mace gaba dayansu, yana mai takaita ayyuka ga kowane daya daga cikinsu don gudanar da su yadda ya dace. A al'amarin hijabi ne kawai aka bambance mace da namiji, to amma a sauran ayyuka, daya suke.

Hakan kuwa ba wai yana nuna cewa gudummawar maza da na mata a al'ummar musulmai dai-dai yake ba, lalle ba dai-dai suke ba. Shi namiji shi yake daukan nauyin kula da gida ta hanyar amfani da dukiyarsa wajen samar da abinci, matsuguni, sitira, kula da lafiya da dai sauran abubuwan jin dadin iyali. Mace kuwa tana da 'yancin neman kudi da kuma sarrafar da shi yadda take so, to amma ba hakkinta ba ne ta ciyar da gida.

Hakkin mace musulma ne kulawa da kuma tarbiyyantar da 'ya'yayenta da kuma samar da kyak-kyawan yanayi na ci gaba da daukakar iyali.

Hakika hijabi yana da amfani ta bangaren iyali da kuma ga al'umma. Domin a gidan da ake girmama hijabi da kuma sanya shi, za mu ga iyalan gidan suna nuna tausayawa, taimakawa da kuma neman zaman lafiya tsakaninsu. Kana a dalilin rarraba wadannan jinsuna biyu, za a iya magance aikata laifuffukan zinace-zinace wanda ya zama ruwan dare a al'ummar kasashen Turai, inda zina tsakanin 'yan gida guda (misali wa da kanwa ko kuma kani da yarsa) ya zama jiki.

Hijabin Musulunci ba wai kawai ya takaita da rufe jiki ba ne. A'a shi wani lullubi ne da yake aiki a matsayin abin da ke nisantar wa daga aikata duk wani laifi da sabo wanda ke lalata mutum da kuma al'umma.

4- Abin Da Ya Hau Namiji da Mace Kan Hijabi

Bari mu yi dubi cikin muhimman al'amurran da suka shafi dukkan jinsunan biyu, don bambance abubuwan da suka hau kansu dangane da wannan muhimmin al'amari na hijabi.

Namiji da mace suna da abubuwan da suka hau kansu, kamar yadda wannan aya ta Alku'ani ta bayyana:

"Ka ce wa muminai maza da su kawar da idanuwansu kuma su tsare farjojinsu, wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai kididdigewa ne ga abin da suke sana'antawa. Kuma ka ce wa muminai mata su kawar da idanuwansu, kuma su tsare farjojinsu, kuma kada su bayyana kawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dora mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna kawarsu face ga mazajensu…". (Surar Nur 24: 30-31)
Manyan malumman fikihu sun yi bayanin wannan hukumci kamar haka:

(A)- Dole ne mace ta rufe dukkan jikinta daga idon wanda ba muharraminta ba.

(B)- Haramun ne ga mutum ya dubi jiki da gashin macen da ba muharramansa ba, amma ban da fuska da tafukan hannayenta. Kana kuma haramun ne ga mace ta kalli maza in dai ba mahaifanta ko danta ko kaninta ko kakanta ko dan'uwanta da kuma sauran wadanda suke da dangantaka da ita ba.

(C)- Haramun ne ga mutum ya kalli fuska ko hannayen macen da ba muharramansa ba da nufin jin dadi, haka ita ma macen.

(D)- Ya halalta ga mutum ya kalli jikin macen da yake son ya aura don ya ga irin yanayin jikinta, haka ita ma macen.

(E)- Yana halalta namiji ko mace su kalli jikin muharramansu (amma ban da al'auranta) matukar dai ba da niyyar jin dadi ba ne, amma kallo irin na sha'awa yana haramta ga muharramai da ma wadanda ba muharramai ba.

(F)- Wajibi ne ga mace da ta rufe jikinta da kuma gashinta daga idon mazajen da ba muharramanta ba.

(G)- Haramun ne ga namiji da ya kadaita da matar da ba muharramansa ba a wajen da babu mai shigansa, idan har suna jin tsoron faruwar aikata haramun; to amma babu laifi ga mutum ya kadaita da macen da ba muharramansa ba a wajen da mutane suke da 'yancin shiga.

(H)- Haramun ne ga mutum ya taba jikin macen da ba muharramansa ba, haka ita macen, ya haramta ta taba jikin namijin da ba muharraminta ba, kamar gaisuwa ta hannu da dai sauransu.

(I)- A yayin lalura, kamar wajen yin magani ko kuma kubutar da mutumin da ruwa yake kokarin cinyewa, yana halalta ga namiji da ya taba jikin mace ko kuma ita macen ta taba namiji, matukar dai babu macen da za ta iya wannan aiki ga 'yan'uwanta mata ko kuma namiji ga 'yan'uwansa maza.

(J)- Yana halalta ga mazaje su saurari muryar macen da ba muharramansu ba ce, matukar dai ba da niyyar jin dadin ko kuma wani abin da zai kai mutum ga aikata haramun ba. Haka kuma yana halalta ga mace da ta jiyar da muryarta ta hanyar tattaunawa da kuma yin jawabi ga mazajen da ba muharramanta ba. To amma da sharadin muryar na ta ba zai janyo fitina ga masu sauraronta ba, domin haramun ne ga mace ta yi magana da mazaje cikin rangwadi da karya murya.

 (K)- Mustahabi ne ga mace da ta kiyaye kyau da adonta ga mijinta kawai, don kuwa jan hankali da kuma kyau suna da muhimmiyar rawa da suke takawa a rayuwar mace, kuma muhimmin al'amari ne cikin abubuwan da suke kawo jin dadin rayuwar iyali.

(L)- Haramun ne ga mace da ta kwaikwayi maza (wajen sa tufafi, aiki da dabi'a), haka shi ma namijin.

(M)- Haramun ne ga mace ta bude kanta da shafa turare yayin da za ta fita waje, wato haramun ne ta sanya turare ta yadda mazajen da ba muharramanta ba za su iya jin kamshin nasa lokacin da take wucewa cikinsu ko kuma yin mu'amala da ita.

Idan muka dubi wadannan shar'antattun ayyuka wadanda suke karkashin hijabin Musulunci da kyau, za mu ga cewa dukkan mazaje da mataye suna da nasu kaso cikin wannan doka, tare da jaddadawa ga mata wajen rufe dukkan jikinsu. Hakika hakan a fili yana nuna mana cewa Musulunci yana so ne ya assasa tsarkakakkiyar alaka tsakanin wadannan jinsu-na biyu; yada tsarki da mutunci tsakanin al'umma; kana da kuma kare al'umma ta hanyar kyawawan mu'amaloli. Kana kuma ba burinsa (Musulunci) ba ne ya wulakanta matsayin mace ko kuma ya
kange ta daga ba da tata gudummawa ga rayuwa ba, kamar yadda wadannan dokoki da suka gabata suka nuna a fili.

Hakika idan har muna so mu yi hukumci kan al'amarin rufe dukkan jiki ga mata, kana ga shi kuwa mun ce maza da mata daya suke a mahanga ta gaba daya dangane da hijabin Musulunci, to tambaya a nan ita ce: Me ya sa mace kawai ne aka kallafa mata rufe dukkan jikinta ba namiji ba?

Amsa a nan, wanda babu wani cikakken mutum da zai musanta, ita ce cewa dalilin kallafa wa mace rufe jiki ita kadai yana da alaka da irin dabi'u da kuma zahirinta. Domin kuwa bangaren janyo hankalin abu da mace take da shi ya fi na namiji; tana da cikakkun abubuwan motsa rai. Don haka, ado da kyau suna daga cikin abubuwan da ake fara siffanta ta da su. Hakika idan har ba a takaita su ba, to tana iya sanya kamilin mutum, da saninsa ko kuma ba da saninsa ba, ya aikata haramun.

Wannan irin siffa da mace take da shi, wanda ke ba ta daman janyo hankalin maza gare ta, shi ne babban ummul aba'isin da ya sanya Musulunci ya wajabta wa mace rufe jikinta don magance faruwar barna. Don haka bai dace a umurci namiji da ya rufe dukkan jikinsa kamar mace ba; domin kuwa namiji bai mallaki wadannan siffofi ba, kuma shi ba a halicce shi da dabi'ar yin ado da kawata kansa, don ya jawo hankalin mata ba. To amma duk da haka fa, Musulunci bai son mutum ya yi mummunan shigar da ba ta dace ba, don kada ya nuna wasu wuraren da ba su dace ba na daga jikinsa.

Dangane da janyo hankali, akwai wasu abubuwa guda biyu da suke wanzuwa, daya ga mace dayan kuwa ga namiji. Wanda yake tare da mace kuwa shi ne sha'awar nuna ado da kyanta, hakan yana daga cikin dabi'unta. Na namiji kuwa shi ne sha'awar kallon mace ba wai kallo kawai ba, a'a har ma da samun jin dadi daga hakan. Duk wadannan abubuwa suna nan tare da su. Wani masani mai suna, Will Durant yana cewa, a wannan duniya babu wani abu da ya fi tabbatuwa kuma ake so a tabbatar da shi kamar sha'awar da mutum yake da ita na kallon mace.

Kana kuma a fili yake cewa sha'awoyin maza da mata na jima'i suna iya tashi ne ta hanyoyi daban-daban. Mace, a matsayinta na halitta mai taushin zuciya, tana bukatuwa da shafa jikinta wajen tayar mata da hankali. A daya bangaren kuma shi namiji halitta ne mai kaurin jiki da karfin sha'awa, hanka-linsa na iya tashi ta hanyar kallo kawai. Don haka mace take rufe jikinta don kada ta nuna jikinta kana shi kuma namiji ba zai ga wani abu da zai tayar masa da hankali ba. Madalla da Musulunci da ya zaba wa al'umma hijabi! Hakika ya yi dai-dai da irin yanayin mace!.

A saboda la'akari da wannan al'amari na jan han-kali, za mu ga kuma Musulunci ya haramta abubuwa kamar su luwadi ga mazaje da kuma madigo tsakanini mataye, domin kowane guda daga cikin wadannan dokoki guda biyu yana da abubuwa da yake haifarwa da kuma dalilansa, kamar yadda sauran dokoki na shari'a suke da nasu dalilan da suka dogara da su.

Wadannan su ne manyan abubuwan da aka lura da su wajen kafa wannan doka; wato ta hijabin Musulunci.

5- Shubhohi Kan Hijabi.

Tambaya a nan ita ce dai: shin masu inkarin ci gaba (kasashen Turai) za su iya yarda da hijabi tattare da irin fahimtar da suka yi masa na cewa shi wani kokari ne na mayar da mace baya da kuma raunanar da ita daga tawaye ga zaluncin da ake mata, wanda hakan raunana rabin al'umma ne?

Hakika, wannan mummunar fahimta ta faro ne daga irin yadda wasu masana da 'yan siyasar kasashen musulmai suke nuna hijabi wanda ya saba wa 'yancin mace da kuma kange ta daga cim ma burinta na yin kafada-kafada da mazaje cikin ayyukan gina kasa.

Wannan al'amari yana bukatar da a fahimci tushen matsalar, ita ce kuwa: shin su wadannan masu ikirarin ci gaba da gaske suke yi yayin da suke yada wannan jita-jita? Shin me suke nufi da " 'yancin" mata?

Idan har abin da ake nufi shi ne 'yancin fadin albarkacin baki; mutum ya fadi ra'ayinsa, 'yancin mallaka; 'yancin zaben mijin aure da kuma 'yanci cikin ayyukan yau da kullum da dai saurans; to ai a Musulunci babu wani abu da ya hana ta wannan 'yancin da kuma makamantansu!

Shin hijabi ya hana mata musharaka cikin bangaro-rin rayuwar yau da kullum da kuma neman ilimi ne?

Shin hijabi ya hana mata fadin albarkacin bakinsu ne?

Shin hijabi ya shiga tsakanin mace da kuma hakkinta na mallakan dukiya ne?

Yana da kyau a tambaya cewa, shin tun asali hijabi yana da wata alaka da wadannan tambayoyi ko kuma shi wani al'amari ne wanda yake da alaka da irin sa tufafin mace, mutunci da kuma irin kyakkyawan alakarta da wadanda suke tare da ita.

Sannan kuma wannan al'amari na hijabi ya shafi al'amurran tattalin arziki da kuma samar da abubu-wan bukatuwa ne. Domin irin hasarar da ake yi a fili take. A bisa misali mu dauka cewa akwai asasai guda biyu na samar da abubuwa:

Na farko yana da alaka da ma'aikata mata, wadanda suke sanya hijabin Musulunci kana kuma suna mu'amala da mazajen da ba muharramansu, ba mu'amala irin wadda Musulunci ya yarda da ita.
Na biyun kuma yana da alaka da ma'aikata mata wadanda suke sanya tufafi masu janyo hankali, kana suke bin irin tafarkin Turai wajen mu'amala da mazaje.

To hakika, za mu ga cewa asasin da ke kulawa da hijabi sai ya fi kokari da kuma samar da abubuwa da ake bukata, saboda irin alakar da ke tsakanin maza da mata.

Kana, a daya bangaren kuwa, za mu ga cewa a daya asasin (asasi na biyu), wanda lalata da munanan ayyuka suke kan gaba, ana bata lokaci mai yawan gaske wajen mu'amaloli na neman biyan bukatun sha'awa (jima'i).

Kana mu dauka cewa akwai dakunan karatu guda biyu:

A na farkon ana kula da mu'amalolin samari da 'yan mata kamar yadda Musulunci ya tsara.

Kana ana biyun kuma ba a kula da mu'amaloli tsakanin samari da 'yan mata kamar yadda Musulunci ya tanada. Shin me ku ke tsammanin zai faru dangane da gudanar da aiki a kowane daya daga cikin wadannan misalai?

Shin za a iya bayyana daki na biyu a matsayin wurin da ya dace da karatu?

A takaice dai, ashe bai fito fili cewa hijabin Musulunci, duk da irin yanayinsa, bai kasance

abin barazana ga 'yancin mace ko aiki ko kuma sauran mu'amaloli na rayuwa ba.

Lalle gaskiya ne (hijabi mummunan abu ne) idan mutum ya yi la'akari da irin hijabin (kulle) da ake yi a kasar Indiya, Iran, Masar da sauransu a lokacin jahiliyya, inda suke kulle mata a cikin gida. Hakika dole ne mace ta ji cewa an take mata hakkinta da kuma katsalandan cikin ayyukanta, wanda abin da hakan zai haifar shi ne ruguje rabin al'umma ko ma fiye. Lalle wannan al'amari ne da ya kamata mu yi dubi cikinsa dangane da irin mummunan yanayin da irin wannan hijabin da ke kange mata daga duk wani irin aiki na ci gaban al'umma yake haifarwa. Musulunci ya yi Allah wadai da irin wannan hijabi na jahiliyya, inda ya sauya shi da wani lullubin wanda ke cike da tsarkake mu'amala karkashin sunan hijabi. Kamar yadda muka bayyana, akwai bambance-bambance masu girman gaske tsakanin wadannan nau'o'i guda biyu na hijabi.

Hakika yadda masu ikirarin ci gaba suke daukan hijabi ya saba wa asalin al'amarin. Al'ummar da lalata ta yi kanta a cikinta, hakan shi ne babban dalilin rashin ci gabanta, saboda abubuwa da kuma karfin da take da su suna tafiya ne wajen al'amurran zinace-zinace, neman mata da almubazzaranci, sabanin al'ummar da tsarkakakkiyar mu'amala take gudana tsakanin mata da maza.

Kana dangane da tunaninsu kan danne wa mata 'yancinsu karkashin inuwar sanya tufafi da kuma tsarkaka wanda hijabin Musulunci ya zo da shi, lalle abin da suke nufi da 'yanci a nan shi ne 'yancin zinace-zinace da duk wasu bangarorinsa wanda ake yadawa a kowane lungu da kuma yanayi. To amma dangane da sauran 'yancocin kuwa ko ma tunaninsu ma ba sa yi.

A takaice dai, hijabi, a mahangar Musulunci, ba shi da wani mummunan tunani dangane da 'yancin mace ko kuma duk wani aiki nata da kuma musharakanta cikin al'amurran yau da kullum. Face ma dai hijabin Musulunci ya tabbatar da 'yancin mata ne da kuma mutuncinsu, bugu da kari kan irin babbar gudummawar da ya bayar wajen tabbatar da 'yancin mata da kuma musharakansu cikin ayyukan ci gaban al'umma.

Sama da haka ma, hijabin Musulunci a ainihinsa, yana ba wa mace mutuncinta ne da kuma daukaka matsayinta a cikin al'umma. Don kuwa mutane sukan yi mu'amala da duk macen da take sa tufafi irin na Musulunci (hijabi) ta bangaren cewa ita cikakkiyar 'yar'Adam ce. Kana ita kuwa macen da ba ta kula da hijabi, ita ma jama'a suna mu'amala da ita ne a matsayin

'yar'Adam, amma saboda abin da take da shi a matsayinta ta mace da kuma jikinta da take barinsa a waje don dadinsu. Don haka, hijabin Musulunci zai ci gaba da zama wani makami na yakan bakin ciki, damuwa da wulakanci.

Yana da kyau a nan a gane cewa duk da irin muhimmancin da Musulunci ya bayar wajen mace ta rufe jikinta gaba ga mazajen da ba muharramanta; yana kuma kiranta da ta kula da kanta da jikinta (wajen yin ado) a cikin gidanta, don kawata matsayin da take da shi na mace wanda Allah Madaukakin Sarki Ya arzurta ta da shi, kuma don biyan bukatunta wadanda shari'ar Musulunci ta halalta mata.

Duk da cewa an hana mace nuna jiki da adonta ga sauran mutane, to amma an kwadaita mata cewa ta gyara jikinta da kuma yin ado wa mijinta. Hakika ma ana yabonta a duk lokacin da ta kawata kanta domin mijinta da kuma jin dadi tare da shi.

Wani abin da ya kamata a ambata a nan shi ne cewa macen da take kula da shiga irin ta Musulunci (hijabi) baya ga irin girmamawa da mutuntawar da take samu daga wajen jama'a da kuma iyalanta, tana kuma dadadawa Ubangiji Mahaliccinta rai ne kana tana samun lada daga wajenSa saboda biyayyar da ta yi wa umurninSa.
Hakika wannan babban nasara ce gare ta, don kuwa tana biyayya ne ga Alkur'ani mai girma da kuma hadisan AnnabinSa (s.a.w.a); kana tana kare al'umma ne daga munanan ayyuka da lalata. Tana mai kawar da munanan tunanunnuka da ayyuka; tana mai daga yanayin aiki da samar da abubuwan bukata da kuma kawo tsarki da daukaka ga al'umma. Duk ta sami damar gudanar da hakan ne kuwa ta hanyar amfani da hijabin Musulunci. Lalle irin albarkatun da za ta samu kan wannan babban aiki, ba zai iya lissaftuwa ba.

Shakka babu, a duk lokacin da mace ta kiyaye zakin muryarta, yanayin motsin jikinta, yanayin dabi'unta da kuma sirrin kanta daga wadanda ba su da 'yancin amfanuwa da su a shar'ance, to hakan taimakon al'umma ne.

Wannan babban aiki da ta dauka yana haifar da kwanciyar hankali da sauki ga sauran halittu 'yan-'uwanta, don ta haka ne za mu iya fahimtar dalilin da ya sa Musulunci ya sanya irin wannan muhimmanci a gare ta cikin sauki. Don ita ce kashin bayan al'umma kuma asasin ci gaban mutum a matsayinsa na dan-'Adam. A saboda haka ne a duk lokacin da ta lalace, to za ta lalata dukkan al'umma ne. Kana kuma a lokacin da ta tsarkaka kuma ta samu kiyayewa irin ta hijabi, to al'umma ma za ta tsarkaka.

Hakika za a iya magance da yawa daga cikin bala'o'i da cututtukan da suka addabi kasashen Yammaci, shaye-shayen giya da kwayoyi, zinace-zinace da sauran matsaloli, idan har aka bar mata suka fahimci akidar hijabi. A wadancan al'ummai, ana kula da kwakwalen mutane da kuma zaluntar samuwarsu da kuma hana su isa zuwa ga kamala, kamar yadda aka halicce su. Wadannan lalatattun al'umma da kuma shuwagabanninsu sun gano hanyar cimma wannan buri na su, don haka sai suka lalata mata, kuma ta haka ne sai suka sami damar lalata al'umma.

6- Gudummawar Mace A Wayewar Musulunci.

Hikayoyi Da Misalai

A shafuffukan da suka gabata mun ga matsayin Musulunci dangane da mace da kuma hijabi. Hakika tabbataccen ra'ayi ne. To amma hakan ya tabbata? Ya ya mace, a tarihin Musulunci, ta gudanar da ayyukan-ta, kana kuma wace gudummawa ta bayar wanda ke nuna irin babban matsayin da Musulunci ya bata yayin da ta fita daga zaluncin lokacin jahiliyya, kana ta rungumi hijabin Musulunci? A shafuffuka masu zuwa, za mu yi dubi ne a aikace na wasu mataye wadanda suka tsinka sasarin bauta ga mazaje, kana suka dauki bautar Ubangiji, Allah Madaukakin Sarki.

Hakika Musulunci da kansa, ya tabbatar da irin hikimar da ke cikin dokokinsa, kuma suka ci gaba da zama wasu matakala na shiriya zuwa ga madaukakiyar rayuwa wacce take cike da kyautatawa da samar da sakamako mai kyau, samun kyawawan dabi'u, tsira da kuma tsarkaka.
Tun da hasken Musulunci ya bayyana ne a Jazirar Larabawa, mace musulma ta sami damar kade kurar wulakanci da bauta kana kuma ta yi ban kwana da ranakun zalunci da kuma bisine 'ya'ya mata da rai. Inda ta fara rayuwa irin wadda wahayi da kuma dokokin Allah Madaukakin Sarki suka tsara. Kana ta fara taka rawa cikin aikin gina madaukakiyar al'umma wacce Manzon Allah (s.a.w.a.) yake kula da ita.

Don haka, 'yan'Adam suka gano irin wannan sabon yanayi wanda ya haskaku da hasken annabci. Wannan hanya wadda wata mace wato Khadija bint Khuwailid, shugaban iyayen muminai, ta fara zabenta. Inda ta ba da dukkan dukiyarta don gudanar da dukkan ayyukan wannan da'awa, yayin da Annabi (s.a.w.a.) yake gwagwarmaya da masu bautan gumaka na lokacin Jahiliyya. Hakika ma dai, irin wannan taimakon kudi na wannan mace madaukakiya a wancan lokaci ya kasance mafi girman makami na fada tsakanin shiriya da kuma bata (gaskiya da kuma karya).

Hakika wannan madaukakiyar mace ta fuskanci da yawa daga cikin wahalhalun rashin abin duniya ne saboda irin ci gaba da tayi na taimakon da'awa zuwa ga gaskiya da kuma da'awar wannan mai ceto, Annabi Muhammadu (s.a.w.a.); da kuma irin tsayuwar dakan da ta yi a kan imani da kuma kare wannan sako da kuma wanda ya zo da shi. Tun daga farkon da'awar, ta kasance a gefen Manzon Allah (s.a.w.a.), tana mai bashi taimakon dukiya, kana da taimako mafi muhimmanci na karfafa shi, soyayya da kuma tausayi ga wannan "Rahama ga Talikai". Ita ce ta farko da ta yi imani da shi, kare shi da dukiya da matsayinta, kuma ita ce ta karfafa shi da kuma kwantar masa da hankali a lokuta mafi wahala na rayuwarsa.

Amirul Muminina, Imam Ali (a.s.) a daya daga cikin huduboninsa a littafin Nahjul Balaga yana fadi dangane da matsayinta cewa:

"...a kowace shekara ya (Annabi) kasance yakan zauna a kogon hira na wani lokaci, babu wani wanda yake tare da shi sai ni. Babu wani wanda zai ganshi ko ya ji shi ko kuma ya kusace shi sai ni. A wancan lokaci babu wani musulmi daga Annabi (s.a.w.a.) sai matarsa Khadija, sai kuma ni na ukunsu. A duk duniyan nan babu wani wanda ya karbi Musulunci. A wasu lokuta a wancan lokacin nakan ga hasken wahayi kana na kan ji kamshi mai dadi irin na annabci"[19].

Sauran matayen Annabi (s.a.w.a.), bayan rasuwar Khadija (a.s.), su ma sun sami wani
babban matsayi cikin tarihi. Ba za mu taba mancewa da irin gudummawar Ummu Salama wacce ta haddace da yawa daga cikin hadisan Manzon Allah (s.a.w.a.) ba. Hakika irin kauna da biyayyarta ga gaskiya da kuma hanya madaidaiciya, shahararren abu ne a cikin tarihin Musulunci inda har wasu daga cikin Imaman Ahlulbaiti (a.s.) sukan bata amanar abubuwan da suka gada na annabci yayin da suke cikin mawuyacin yanayi.

Lalle irin gudummawar mata a tarihin zamantakewa da siyasar Musulunci yana da muhimmanci gaske. Daga cikin shahidan farko na Musulunci akwai wata mace mai suna Sumayya, matar Yasir, wacce aka gana mata tsananin azaba inda daga karshe ta kasance wacce ta fara yin shahada a Musulunci. Hakika za a iya ganin gudummawa da zaluntakan mata musulmai a shafuffukan tarihi. Wadannan mataye irin su Sumayya suna da madauka-kiyar daraja. Irin gudummawar da suka bayar ga al'amurran addini da siyasa sun zama darussa ga mataye a duk duniya wajen dawo da mutuncinsu da suka rasa.

Daga cikin irin misalin karfin da Musulunci ya ba wa mataye a farko-farkon tarihi, ita ce wata mace da ake kira Nusaiba wacce take zaune a birnin Madina. Ta kasance Ba'ansariya (mutanen Madina wadanda suka taimaki musulman da suka yi hijira daga garin Makka) ce ana kiranta da Nusaibatu Jarrah. Ta yi aure, sannan tana da 'ya'yaye guda biyu, masu suna Amarah da Abdullah. Sunanta ya fara fitowa ne a cikin tarihi yayin wata bai'a da wadansu Ansarawa, mazaje guda sittin da mataye guda biyu, suka yi wa Manzon Allah (s.a.w.a.) bayan da suka karbi Musulunci. Wannan bai'a ana kiranta da Bai'atul Akbah.

Manzon Allah (s.a.w.a.) wanda yake tsananin girmama mata, yayin wannan bai'a sai ya sanya hannunsa cikin kwano cike da ruwa kana ya mika wa wadannan mata, inda su ma suka yi hakan. Wadannan mutane sun taimaki gwamnatin Manzon Allah (s.a.w.a.) matukar taimako. Domin mijin wannan mata Sumayya ya yi shahada a yakin Badar, kana daya daga cikin 'ya'yayenta ma ya yi shahada a wannan lokacin.

Hakika tarihi ya nuna mana irin yadda wannan mace Nusaiba ta kasance a wurin yaki tare da Manzon Allah (s.a.w.a.) a matsayin likita. Ta yi musharaka cikin yakukuwa da daman gaske, tana dauke da jakar ruwa, inda take yin magani ga marasa lafiya da wadanda aka ji musu rauni a filin daga.
Kana kuma Nusaiba tare da danta da ya saura, Amarah, sun halarci yakin Uhudu. Yayin wannan yakin, lokacin da musulmai suka tarwatse, sai ta dauki jakan ruwanta tana bi tana shayar da masu jin kishirwa da kuma taimakon wadanda aka raunana ta hanyar magunguna da take da su.

An ruwaito ta tana cewa: "Lokacin ana tsakiyar yakin, sai na ga dana yana gudu, sai na tsai da shi na ce masa: Ya dana! Ina za ka? Shin daga wa kake gudu? Daga Allah ko daga ManzonSa?".

Nan take ta komar da shi, kana ta tsaya tana kallo daga nesa. Daga nan ne ta ga makiya sun kewaye Manzon Allah (s.a.w.a.), nan da nan ita da wannan da nata suka nufi inda Annabi (s.a.w.a.) yake don kai masa agaji. A nan ne daya daga cikin kafirai ya kashe wannan da nata, ita kuma Nusaiba sai ta dauki takobin dan nata, da taimakon Allah ta kashe wanda ya kashe mata da. Ko da ganin haka, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce mata: "An gaishe ki, Ya Nusaiba, Allah Ya yi miki albarka".

A wannan yaki ne wannan jarumar mace ta sami raununnuka har guda goma sha uku, daya daga cikinsu saran takobi ne a wuyanta, sannan kuma ta rasa hannunta guda a yakin Yamama. An ruwaito cewa wannan mace mai tsananin sadaukarwa za ta dawo lokacin Imami na karshe, Imam Mahdi (a.s.) a matsayin likita (wacce za ta taimaka masa).

Sayyida Zainab (a.s.), wannan jarumar 'ya ta Imam Ali (a.s.), ita ma ta kaddamar da muhimmiyar gudummawa lokacin da ta dauki nauyin isar da sakon dan'uwanta Imam Husaini (a.s.) bayan shahadarsa a Karbala a hannun azzaluman sarakunan Umayyawa, karkashin ja-gorancin Yazid bin Mu'awiyya.

Ta dauki nauyin yin bayani da kuma isar da dalili da manufar wannan babban yunkuri na Imam Husaini (a.s.) a duk guri ko kuma taron da ta halarta. Kana ta tona asiran azzalumai a garuruwan Kufa, Damaskas da Madina. Sannan kuma ta dauki nauyin kare fursu-nonin gidan Manzon Allah (s.a.w.a.), wadanta suka hada da mata da kananan yara, tare da yankakken kan Imam Husaini (a.s.) daga sahara mai zafin gasken nan ta Karbala zuwa birinin Damaskas.

Hakika tarihi ya rusunar da kai cikin kunya gaba ga wannan madaukakiyar mace wacce Musulunci da raunana ke gode mata, saboda irin sadaukarwar da ta yi, da kuma irin juriya, hakuri da kuma gudumma-warta ga tafarkin gaskiya.
Cikin jarunta ta fuskanci azzalumai kana ta tona munanan ayyuka da tsarur-rukansu. Ta bayyanar da sakon gwagwarmaya, daukaka, mutunci da gaskiya a dukkan garuruwa.

Jawabanta a fadojin wadanda suka kamo ta, suna cike da hikima da motsa rai. Lalle ta shahara ta wajen fuskantar Yazid da ta yi a fadarsa da ke Damaskas. Ta fuskance su gaba dayansu kana ta zarge su kan abubuwan da suka aikata ba tare da tsoron mutuwa ko gallazawa, wanda ya zamanto ruwan dare ga makiyan wancan hukuma.

Haka ta ci gaba har karshen rayuwarta wajen tona asirin zalunci da azzalumai da kuma isar da sakon dan'uwanta (a.s.). Ta kasance mai fada da zalunci, kana ta mallaki tsarkakakkiyar dabi'a da jaruntaka a duk tsawon rayuwarta. Tana daga cikin madaukakan mutane a duk inda ta kasance. Ta ci gaba da gwa-gwarmayar Imam Husaini (a.s.) da kuma taimakon al'umma wajen fahimtar abin da ya hau kansu na yakan zalunci da babakere.

Idan har muna son mu yi bincike cikin shafuffukan tarihin Musulunci, babu yadda za a yi mu mance da ayyukan Hamida, matar Imam Ja'afar Sadik (a.s.) kuma mahaifiyar Imam Musa Kazim (a.s.). Ta kasance tana kula da mabukata da marasa galihu na birnin Madina, a bisa umurnin Imam Sadik (a.s.). Inda take rarraba kudi ga fakirai da kuma ziyarar marasa galihu, don taimaka musu da abubuwan da suke bukata.

Misalin wata matar kuma mai tsoron Allah wacce ta ba da muhimmiyar gudummawa a tarihin Musulunci, ita ce Salil, mahaifiyar Imam Hasan bin Ali al-Askari (a.s.).

Ta ba da muhimmiyar gudummawa wajen kare gaskiya da kuma kulawa da shiriyar Ubangiji. Wannan mace mai daukaka ta kasance a matsayin mai sadarwa tsakanin Imaman nan guda biyu, wato: Imam Aliyu al-Hadi da Hasan Askari (a.s.), da sansanin muminai mabiyansu lokacin da wadannan Imamai suka shiga halin tsanantawa daga wajen azzaluman zamaninsu. Ita take isar da sako da umur-nonin wadannan Imamai ga muminai mabiyansu, kana ta isar da tambayoyi da sakonninsu da kuma halin da suke ciki ga wadannan Imamai (a.s.).

Yana da muhimmanci mu fahimci cewa kasancewar mata a cikin al'amurran siyasa yana da matukar muhimmanci. Domin kuwa, a wasu lokuta, mataye sukan dauki rabin adadin al'ummar kowace kasa, kuma su kan iya canza alkiblar al'umma zuwa ga alheri ko sharri gwargwadon irin wayewarsu ta siyasa da kuma

musharakarsu. Hakika hijabi ba ya hana irin wannan gudummawa kamar yadda bai hana kowacce daga cikin wadannan mataye da muka ambata a baya ba.

A wannan zamani namu za mu ga misalin irin wannan wayewa da kasancewa a lokacin gwagwar-mayar Musulunci a kasar Iran. Inda mata duk da cewa ga jarirai a hannayensu kana ga kananan yara a gefensu, amma haka suke fitowa kan tituna don nuna rashin amincewarsu ga gwamnatin zalunci ta Sarki Shah, sanna kuma ga 'yan sanda suna karkashe su. A sakamakon haka da dama daga cikin wadannan iyaye mata da 'ya'yayensu suka yi shahada yayin zanga-zangogin da suka dinga yi.

A lokacin da sakon gaskiya ya bayyana kana aka sake rayar da sautin gwagwarmaya a karni na ashirin, za mu ga yadda matan Palasdinawa, suke nuna hannu wa sojojin Yahudawa 'yan-share-guri zauna, kana a daya hannun kuma suna dauke da duwatsu suna jiran samun dama don su jefi abokan gaba. A halin yanzu, wadannan mataye da sauran mataye irinsu a duk fadin duniya, ana daukarsu a matsayin kashin bayan wannan gwagwarmaya. Hakika hijabi shi ne tutarsu kuma suna alfahari da matsayinsu na masu yaki da babban makiyin gaskiya.

Kana za mu ga irin tasirin da Musulunci yake da shi a kan jama'a kana shi kuma hijabi a kan mata, idan muka yi la'akari da abubuwan da suka faru a kasashen Azarbaijan da kuma Bosniya Hazgovina.

Musulunci ya bayyanar da kansa a cikin su kana kuma ya ba su jaruntaka da karfin jure wa zaluncin da ya mamaye su. Tun shekaru da dama tsarin kwaminisanci da Gurguzu ya cire musu tsarin Musulunci daga al'adunsu. Suna kiran kansu musulmai to amma sun jahilci dokoki da tsare-tsaren Musulunci. Lokacin da suka sami 'yancin kansu daga wannan tsari da babu Allah a ciki, sai suka juya zuwa ga hasken gaskiya, kana suka karbo abin da da suka rasa. Babu shakka, daya daga cikin alamun hakan shi ne yin hijabi ga mata.

Wadannan misalai suna ba da tunanin irin abin da matayen musulmi masu bin dokoki da ka'idojin Musulunci za su iya cimmawa. Suna nuni da irin babbar gudummawar da ta bayar ga rayuwar al'um-ma, wanda ya saba wa irin wadancan munanan tuna-nunnuka da kuma ra'ayoyi na wadanda suka jahilci Musulunci da kuma irin tabbatacciyar karfinsa na ruguza kangin da yake hana mata musulmai gudanar da ayyukansu karkashin inuwar ci gaban Musulunci.

7- Abubuwan da Alkur'ani Da Kuma Hadisai Suka Fadi Kan Mace Da Kuma Rayuwa
Neman Izini

" Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku shiga gidaje wadanda ba gidajenku ba, sai kun sami izini, kuma kun yi sallama a kan ma'abutansu. Wannan ne mafi alheri a gare ku, tsammaninku, za ku tuna". (Surar Nur, 24: 27)
Yin Kama

Imam Ali (a.s.) ya ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:

"Allah Ya la'anci mazaje masu mai da kansu kamar mata, ko kuma matan da suke mai da kansu kamar maza"[20].

Shafa Turare Yayin Fita Waje

Imam Husaini (a.s.) ya ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:

"Duk macen da ta shafa turare sannan ta fita wajen gidanta, Mala'iku suna la'antanta kana ana debe mata albarkar Ubangiji har sai ta dawo gida"[21].

Mummunan Kallo

Imam Husaini (a.s.) ya ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:

"Mummunan kallo daya ne daga cikin kibiyoyi masu guba na Shaidan, kana mummunan kallo yana haifar da mummunar nadama"[22].

Nesantar Abubuwan Haramun:

Imam Bakir (a.s.) yana cewa:

"A ranar kiyama, dukkan idanuwa za su yi kuka, in banda guda uku: idon da yaki barci don gadin musulmai (dukiyoyinsu, kasarsu da dai sauransu), saboda Allah; kana da idon da ya yi kuka don tsoron Allah; da kuma idon da aka rufe shi daga kallon abubuwan da Allah Ya haramta"[23].

Kallon Mata

An tambayi Imam Sadik (a.s.) kan ko ya halalta ga namiji ya kalli fuskan macen da yake son ya aura, kuma ya kalle ta ta baya. Sai ya ce:

"Na'am babu laifi ga namiji ya kalli fuskar macen da yake son ya aura da kuma kallon ta ta baya"[24].

Gaishe Da Mata

Imam Husaini (a.s.) yana cewa:

"Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yakan gaishe da mata, kana su ma sukan mayar masa da sallamar tasa. Kana Amirul Muminina, Imam Ali (a.s.) shi ma ya kasance yakan yi sallama ga mataye, to amma ba ya son ya gai da budurwaye daga cikin matayen, inda yake cewa: "Ina tsoron kada muryarta ta yi min tasiri, har ya kai ni ga aikata zunubi maimakon samun lada"[25].

Azabar kallon Mata

Imam Sadik (a.s.) yana cewa: "Wata rana wani saurayi Ba'ansare ya gamu da wata mace a garin Makka. A wancan lokacin, mata sukan sanya lullubi, sai ya fara kallonta tun tana zuwa. Lokacin da ta wuce sai ya ci gaba da kallonta, har sai da ta shiga wani lungu. Kana ya ci gaba da kallonta yayin da yake wucewa ta lungun, har lokacin da wani kashin da ke jikin garu ya kwarzane shi a fuska, inda daga nan macen ta bace masa. Kwatsam sai ya ga jini yana zuba masa. Daga nan sai ya ce: Dole ne in je in sanar da Manzon Allah (s.a.w.a.) wannan abu da ya faru. Lokacin da Annabi (s.a.w.a.) ya gan shi cikin wannan hali sai ya tambaye shi me ya faru ne. Sai ya gaya wa Annabi (s.a.w.a.) duk abin da ya faru. Nan take sai Mala'ika Jibril (a.s.) ya sauko da wannan aya:

"Ka ce wa muminai maza su runtse idanuwar-su, kuma su tsare farjojinsu, wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai kididdigewa ne ga abin da suke sana'antawa"[26].

Zaman Gefen Titi

Abu Sa'id al-Khudri yana cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Ku guji zama a gefen titi",sai wasu sahabbai su ka tambaye shi cewa: "Ya Manzon Allah! Ba za mu iya barin zama a gefen titi inda muke tattauna abubuwan daban-daban ba". Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce musu: "Idan ba za ku iya barin hakan ba, to ku ba wa titin hakkokinsa". Sai suka ce: "Menene hakkokin titin". Sai yace: "Su ne ku rufe idanuwanku; ku nisanci cutar da sauran jama'a; ku amsa sallama; kuma ku yi umurni da alheri, kana ku yi hani da sharri[27]).

Kwadayin Daukakan Muminai:

Amirul Muminina (a.s.) yana cewa:

"Lalle Allah Yana fushi da daukakar masu imani maza da masu imani mata. Saboda haka tilas mai imani ya yi fushi (da daukakar da yake samu), saboda wanda bai yi fushi da daukakar da ya samu ba, shi ne mai juyayyiyar zuciya"[28].

Falalar Kawar Da Idanuwa:

Abu Imamah yana cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:

"Musulmi shi ne wanda yayin da ya kalli mace kyakkyawa sai ya kawar da idanuwansa, Allah Zai ba shi ladar ibadar da dadinta a zuciyarsa take"[29].

Kiyaye Kai

Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:

"Ku kiyaye kanku daga abubuwa guda shida, ni kuwa zan lamunce muku aljanna; idan za ku yi magana, ku fadi gaskiya; in kuka dauki alkawari, to ku cika; ku rike amana; ku kare farjojinku (sai ga matayenku); ku kawar da idanuwanku (daga kallon haram); kana ku kame hannayenku daga aikata zalunci da kuma abubuwan haramun[30]).

Girmama Mace Yayin da yake jawabi wa musulmai lokacin aikin hajjin ban-kwana, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya gargade su dangane da abubuwan da yake tsoron za su bar su bayan rasuwarsa, inda ya ambaci mace a matsayin daya daga cikin muhimman abubuwa. Ya na cewa:

"Ku ji tsoron Allah dangane da mata, kana ku kula da su da kyau"[31].

 

Aure Mai Albarka:

Anas ya ruwaito cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:

"Duk wanda ya auri mace don daukaka da kyawunta, to Allah ba zai kara masa nasa ba, face ma ya kawo masa wulakantuwa; duk wanda ya aure ta don dukiyarta, Allah ba Zai kara masa nasa ba, sai dai ma Ya sanya masa talauci; duk wanda ya aure ta don dangantakanta, to Allah ba Zai kara masa nasa ba, sai dai ya mai she shi ba kome ba; duk wanda ya auri mace ba don kome ba face sai don ya kalle ta (ya ji dadi), kuma ya kare farjinsa (daga aikata haramun) da kuma kulla zumunta, Allah Zai albarkace shi ta hanyarta, haka ita ma[32]).

Alkur'ani mai girma yana cewa:

"Kuma daga ayoyinSa, Ya halitta muku matan aure daga kanku, domin ku nitsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani".(Surar Rum, 30:21)

A wata ayar kuma, ana magana kan mace mai biyayya:

"…..to, salihan mata masu da'a ne, masu tsarewa (yayin da mazansu ba sa nan) kan abin da Allah ya tsare....".(Surar Nisa'i, 4: 34)

Kwadaitarwa Da Kuma Kulawa Da Hijabi:

Musulunci, duk da irin tausayin mata da yake yi, yana kwadaita musu kulawa da hijabi a wannan aya ta Alkur'ani mai girma:

"Ya kai Annabi! Ka ce wa matanka da 'ya'yanka da matayen muminai su kusantar da kasa daga manyan tufafin da ke a kansu. Wancan ya fi sauki ga a gane su domin kada a cuce su. Kuma Allah Ya kasance Mai gafara, Mai jin kai". (Surar Ahzabi, 33:59)

Daidaitawa

A ayoyi da dama, Alkur'ani mai girma yana magana kan daidaitawa tsakanin jinsosin nan biyu. A daya daga cikinsu yana cewa:

"....kuma su matan suna da kamar abin da yake a kansu, yadda aka sani...". (Surar Bakara, 2: 228)

A wani gurin kuma, Alkur'ani mai girma yana cewa:

"Ya ku mutane! Lalle ne mu, mun halitta ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku dangogi da kabiloli, domin ku san juna. Lalle mafificinku daraja a wurin Allah, (Shi ne) wanda yake mafificinku a takawa. Lalle ne, Allah Masani ne, Mai kididdigewa".(Surar Hujurati, 49:13)

Dangane da aiki da kuma aikata kyawawan dabi'u, kuma Alkur'ani mai girma ya bayyana daukakan Musulunci da kuma daidaitawarsa ga ma'aikata. Hakika hakan wani abu ne da kasashen Turai suka gagara tabbatar da shi. Alkur'ani mai girma yana cewa:

"Kuma wanda ya yi aiki daga ayyukan kwarai, namiji ne ko kuwa mace, alhali kuwa yana mumini, to wadannan suna shiga aljanna kuma ba za a zalunce su da gwargwadon hancin dabino ba". (Surar Nisa'i, 4: 124)
(Wanda ya aikata aiki na kwarai daga namiji ko kuwa mace, alhali yana mumini, to hakika, Muna rayar da shi, rayuwa mai dadi. Kuma hakika, Muna saka musu ladarsu da mafi kyawun abin da suka kasance suna aikatawa). (Surar Nahali, 16: 97)

A wata ayar kuma, Allah Madaukakin Sarki Ya yi alkawarin cewa:

"...lalle ne Ni, ba zan tozartar da aikin wani mai aiki ba daga gare ku, namiji ne ko kuwa mace, sashenku daga sashe....". (Surar Ali Imrana, 3:195)

ALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMIN.


[1] "Wa'id" a larabce yana nufin bisne 'ya mace da rai. A zamanin jahiliyya, Larabawa sun kasance suna aikata wannan dabi'a ta hanyoyi daban-daban. To lokacin da Musulunci ya zo sai ya hana su aikata wannan mummunan dabi'a

[2] Saeed Afghani cikin littafin " Islam wal Mar'ah (Musulunci da kuma Mace) ya ruwaito shi daga Tirmizi.

[3] Kamar na sama, Jami al-Saghir.

[4] - Shaikh Saduk cikin litafinsa "Man la Yahdhuruhu al-Fakih, juzu'i na 3 , babi na 103 Hub al-Nisa (Son mata

[5] Shahid Sayyid Kutb cikin littafin "Fi Dhilal al-kur'an", juzu'I na 8, shafi na 479, bugun Darul Ihya al-Turath al-Arabi, 1971, Beirut.

[6] Al-Mar'a fi jami al-Adyan wal Usur" na Muhammad Abdulla Maqsud, shafi na 38, ya ciro shi daga littafin "Woman During History", shafi na 41.

[7] Kamar na sama, ya ciro daga littafin "The Right of a Husband Upon His Wife and the Right of a Wife Upon Her Husband" (Hakkin miji akan matarsa kana da kuma hakkin mata akan mijinta) na Taha Abdullah Afifi, shafi na 12-13.

[8]  "Nizamul Hukuk al-Mar'a fil Islam" na Shahid Sheik Murtadha Mutahari, shafi na 269, bayan bugun farko, 1404 B.H, Tehran. 3- "Mas'alat al-Hijab" na Shahid Mutahari, shafi na 49, bugun farko 1407, B.H, Tehran.

[9] Kamar na sama, shafi na 87, ya ciro daga littafin "Iran During Sassanian Period".

[10] Mujallar al-Ifaf, adadi na 9, shafin na 25.

[11] "Al-Mar'a fi jami'i al-Adyan wal usur" na Muhammad Abdullah Maksud, shafi na 48

[12].- "Mas'alat al-Hijab", na Shahid Mutahari

[13] Jaridar kasar Kuwait ta "al-?abas" ta ranar 6/2/1976, ita ma ta ciro ne daga wata mujallar kasar Italiyya mai suna Timbo

[14]. kamar na sama ta ranar 6/10/1976

[15] Littafin "Man and Religion", na turanci, bugun farko, shafi na 81, wadda Mu'assasar Al-Balagh ta buga , tana ciro shi ne daga wata makala ta Jami'ar Iskandariyya

[16] Kamar na sama shafi na 82

[17] Kamar na sama shafi na 84.

[18] Kama na sama.

[19] Nahjul Balagah, huduba ta 192.

[20] Bihar al-Anwar na Allamah Majlisi, juzu'i na 79, shafi na 64, Ibn Dawud, Tirmizi, Nisa'i, Bukhari da Ibn Majah duk sun ruwaito shi.

[21] Al-Kafi, juzu'i na 3, shafi na 74.

[22] Kamar na sama, shafi na 82.

[23] Mishkat al-Anwar, shafi na 155.

[24] Al-Kafi, juzu'i na 3, shafi na 63. 3- Kamar na sama, juzu'i na 1, shafi na 163.

[25] Wasa'il al-Shi'ah, juzu'i na 9, shafi na 63. Ayar kuma ta na cikin Surar Nur ne aya ta 30.

[26] Sahih Bukhari, juzu'i na 7-9, shafi na 63.

[27] Mishkat al-Anwar, shafi na 236.

[28] Al-Targib wa al-Tarhib min Hadith al-Sharif, juzu'i na 3.

[29] Al-Targib wa al-Tarhib min Hadith al-Sharif, juzu'i na 3.

[30] Kamar na sama, shafi na 35.

[31] Tuhaf al-Ukul an Aali al-Rasul na al-Harrani, shafi na 23.

[32] Al-Targib wa al-Tarhib, juzu'i na 3, shafi na 46.