MATASA DA RAYUWA

Wadda Ta Wallafa: MU'ASSASAR AL-BALAGH

Wanda Ya Fassara: MUHAMMAD AWWAL BAUCHI

Dubi Cikin Abubuwan Da Suke Kewaye Da Matasa

Tun lokacin da na bude idanuwana a kan abubuwan da suke kewaye da ni na rayuwa, kana tun lokacin da na fara fahimta da kuma gano motsin abubuwan da suke kewaye da ni, tun daga lokacin na fara hada tunani da kuma gano dukkan abubuwan da na sadu da su...

Wannan duniya mai girma da daukaka da ta kunshi: sama da taurari, rana da wata, ruwa da iska, haske da duhu, kasa da tsirrai, koguna da ruwan sama, bishiya da nau'o'in dabbbobi daban-daban, mutane da suke raye a al'ummance, suna magana kana kuma suna fahimtar da junansu, sannan kuma suna saye da sayarwa tsakaninsu....

Wadannan abubuwa da suka saba da junansu.... da suke cike da kyau da tsari, su suka sanya ni cikin tsananin tunani....kai suka sanya ni ina tambayan kaina: shin me ya sa ne ba zan fadada tunanina a kansu ba da kuma yin tunani kan girma da kuma daukakan wadannan halittu masu ban mamaki da suke kewaye da ni ba....kai me ya sa ne nake musu kallon daidaiku....ashe su ba abubuwa ne da suke tabbatar da cikan junansu ba....ashe su ba abubuwa ne da suke koyar da ni abubuwa da yawa ba....a takaice dai, me ya sa nake kallonsu a matsayin abubuwan da ba su da alaka da junansu?

Lalle gaskiya ce, cewa cikin dukkan abin da na sadu da shi akwai abubuwan al'ajabi da sanya tunani a cikinsa... hasken rana....zubowar ruwan sama.... fitowar tsirrai da kuma girmansu....nau'o'in furrai da kuma kamshinsu....launin sama....ja-ja-ja-jan fitar rana....duk wadannan suna da ban mamaki.

Me ya sa aka samu wadannan halittu da kuma irin wannan bambance-bambance.....shin wannan wani irin kyau ne na koli?

Kash! Ya ya girman wannan irin yanayi zai kasance, idan da a ce na fahimce su tun lokacin da aka haife ni ko kuma lokacin da na fara ganinsu?

Hakika na zo ne daga wata duniya ta daban....daga duniyar mahaifa.... daga duniya ma'abuciyar duhu da take kange daga wannan duniya.....

A halin yanzu ina jin wajibcin fahimtar wancar duniya....duniyar mahaifa wacce ban kasance ina tunaninta ba, kuma in fahimci wani abu daga cikinta ba. Lalle ina rayuwa cikinta ne ba tare da masaniya, ko nufi ko dogaro da kai ba.....na kasance dan tayi ne da ke rayuwa a kan jinin mahaifiyarsa.... tana rainonsa da kyau. Wannan ma wata rayuwa ce da ban san kome daga cikinta ba, face dai a halin yanzu na fahimci falalar wannan kulawa ta Ubangiji, da kuma kokarin mahaifiyata da ta rike ni cikin mahaifarta har na tsawon watannin tara, tana ciyar da ni da jininta, kana kuma tana mai kokarin ta ga na wuce wannan mataki cikin koshin lafiya....

Hakika na kasance ba ni da wani iko a wancar duniya da ban san kome ba dangane da ita ba....ba ni da karfi cikin samar da wani abu ko kuma zabi cikin yadda yanayina zai kasance, kuma ba ni da ikon samar wa kaina abinci ko isa ga iska ko kuma kare kaina daga hatsari. Don kuwa na kasance dan tayi ne, kamar kwai cikin injin kyankyasa ko kuma kamar hatsi a cikin kasa....na tashi ne bisa kulawa ta Ubangiji, sannan kuma mahaifiyata tana hakura da ni kan abubuwan da na ke mata alhali tana mai farin ciki, tana mai zagaye ni da so da kauna da kuma jira, tana mai kirga kwanaki don ta sadu da ni.....

Hakika na kasance a wancar duniya mai cike da duhu kana kuma ban san kome a kanta ba, karkashin kulawa da kauna iri biyu: kauna ta mahaifiyata da kuma kauna ta Ubangiji....

Na fara rayuwa ne karkashin inuwar so da rahama....lalle a halin yanzu ina jin girman wannan soyayya da kuma falalar wancan rahama da kuma kula. Ina jin lalle ina da bashin wanda ya nuna min wannan soyayya da kuma kulawa, kana kuma ya min guzuri da jininsa duk tsawon zama na cikin wannan yanayi ba tare da na san inda na ke ba, ko kuma tunanin wani abu daga cikin al'amurran rayuwa ta ba....

Lalle wannan babban kyautatawa ce mai girma, lalle ya zama wajibi in ce: "shin, kyautatawa na da wani sakamako, face kyautatawa"....kai lalle ya zama wajibi in ce: inkarin wannan kyautatawa sabo ne da kuma kauce wa hanya wanda ya cancanci azaba.

Lalle wajibi ne in kasance mai godiya....kana kuma in so wanda ya nuna min irin wannan so da kuma kyautatawa....

Dalilan Girman Ubangiji da kuma Tsari:

Daga wancan duniya (duniyar mahaifa) zuwa duniyar rana, haske, hankali, nufi da dogaro da kai.... lalle malamai sun bude mana kofofin sanin wannan duniya ta hanyar irin bincike-binciken da suka yi ta gudanarwa, sannan kuma suka bayyanar mana da sirruka da kuma abubuwan da suka shige mana duhu na dabi'a da kuma abubuwa masu rai; irinsu dabbobi da tsirrai. Kamar yadda kuma suka bude mana kofar sanin duniyar 'yan'Adam da abubuwan mamaki na cikinta da kuma karfin fahimta, magana da kuma tunani....

Hakika karanta irin wadannan abubuwa da malamai suka binciko mana, zai sanya mu cikin tsananin mamaki, kuma za su fitar mana da girman Ubangiji Mahalicci da kuma samuwar Wanda Ya tsara wannan duniya.....

Daya daga cikin wadannan malamai mai suna Karisi Maurisun ya wallafa wani littafi da ya ba shi sunan "al-Ilmu yad'u lil-Iman". A cikin wannan littafi, malamin ya yi bayani kan girman tsarin Ubangiji ga wannan duniya, inda ya tabbatar mana cewa dukkan wani abu da yake wannan duniya yana nuni ga girman Mahaliccinsa ne....lalle mutum yakan fahimci samuwar Allah da kuma girmanSa yayin da yake karanta wannan littafi.....

Wannan marubuci yana cewa:

"Duniya takan juya sau guda a duk sa'o'i ashirin da hudu, ko kuma abin da ya yi daidai da mil dubu a ko wani awa guda. To amma a halin yanzu an kiyasta cewa tana juyawa da abin da ya yi daidai da mil dari kawai a duk sa'a guda. To amma me ya sa ba hakan ba? Don haka, a irin wancan hali, dare da ranarmu za su kasance masu tsawo fiye da yadda suke a halin yanzu har sau goma. A irin wannan hali, rana za ta kona tsirranmu a ko wace rana, sannan da daddare kuwa, dukkan tsirrai za su daskare....

Hakika rana wacce ita ce mabubbugan dukkan rayuwa, za ta kai darajar zafi da ya kai kimanin 12,000 ma'aunin faranhait, kuma kasa tana da nisa daga gare ta ta yadda za mu iya samun zafinta kamar yadda ya kamata. Wannan nisa tabbatacce ne kuma mai ban mamaki, sannan wannan canje-canje ya kan afku ne cikin miliyoyin shekaru; ta yadda rayuwa za ta ci gaba kamar yadda muka fadi. Idan darajar zafi ya karu a kasa da kimanin daraja hamsin a shekara guda, to dukkan tsirrai za su mutu tare da 'yan'Adam don zafi ko daskarewa.
Sannan kuma kasa takan kewaya rana kimanin mil goma sha takwas a ko wace dakika guda. Da a ce adadin kewayar tata zai kai misalin mil shida ko kuma mil arba'in a ko wace dakika, to da nisanmu da rana ko kusancinmu da ita zai kasance ta yadda zai hana wanzuwar irin wannan rayuwa ta mu da ita".

Sannan kuma wannan babban malami ya ci gaba da ce wa: "Nisan wata daga gare mu ya kai kimanin mil 240,000....da a ce nisan wata daga gare mu mil 50,000 misali, maimakon wannan nisa da a halin yanzu yake tsakaninmu da shi, to da tsawonsa ya kai karfin da ambaliyar ruwa za ta mamaye dukkan kasar da take karkashin makwararan ruwa ta sau biyu a rana, har ya girgiza duwatsu....kuma da duniya ma ta ruguje saboda wannan bala'in....".

Lalle yana da kyau ko wane daya daga cikinmu ya yi tunani yayin da yake karanta wannan hakika na ilimi, ya tambayi kansa ya ya aka yi aka sami irin wannan tsarin....kuma Wane ne Ya sana'anta hakan?

Hakika Alkur'ani mai girma ya amsa mana wannan tambaya, yayin da yake ce wa:

"....bisa sana'ar Allah Wanda Ya kyautata kowane abu....". (Surar Namli, 27: 88) "Shi ne Wanda Ya halitta sammai bakwai, dabakoki a kan juna, ba za ka ga goggociya ba a cikin halittar Allah Mai rahama...." (Surar Mulk, 67: 3)

"Kuma rana tana gudana zuwa ga wani matab-baci nata. Wanda kaddarawar Mabuwayi ne, Masani. Kuma da wata, Mun kaddara masa man-ziloli, har ya koma kamar tsumajiyar murlin dabino, wadda ta tsufa. Rana ba ya kamata a gare ta, ta riski wata. Kuma dare ba ya kamata a gare shi ya zama mai tsere wa yini, kuma dukkansu a cikin sarari guda suke yin iyo". (Surar Yasin, 36: 38-40)

To idan wannan ita ce duniyar kasa da sama, bari mu koma ga kogi da kuma abubuwan da suka kewaye mu.

Lalle wani irin kyau ne wannan duniya take da shi, duniyar da take cike da dabbobi, kifaye, lu'u-lu'u da murjani......

Hakika bincike da karatuttukan da kwararrun malami suka gudanar sun kai su ga gano abubuwan ban mamaki na wannan duniya....abubuwan da suke sanya mutum cikin tunani da mamakin girman wadannan sirrori da suke tattare da wadannan halittu na cikin ruwa.

Wannan sanannen malami (Karisi Maurisun) cikin wannan littafi nasa mai suna "al-Ilmu Yad'uw
lil-Iman" ya nakalto mana wani labari dangane da kifin salmon da kuma macijin ruwa, inda yake bayyana cewa:

"Bayan binciken da suka yi kan wadannan kifaye, malamai sun gano abubuwa masu ban al'ajabi kwarai. Wadannan kifaye su kan haihu a cikin kogi, amma sai su tafi su rayu na shekaru cikin teku, sannan daga baya su dawo cikin kogin da aka haife su. Kuma idan aka dauko su daga wannan kogi zuwa wani kogi na daban wanda suke hade, za su dinga iyo har sai sun koma cikin kogin da aka haife su.

Lalle sun san inda aka haife su, kuma suna da alaka da wajen, don haka suke neman wurin har sai sun koma wajen; don su rayu cikinsa".

Wannan malami ya sake kawo wata kissa mai ban mamaki dangane da rayuwar macijin ruwa......

Macijin ruwa ya kan yi hijira daga kogin da aka haife shi bayan ya girma, zuwa wani guri mai nisan gaske, inda zai je can ya rayu har ya mutu. Bayan isansu wannan guri da kuma haihuwa a wajen, 'ya'yayensu sukan sake shafe wannan tafiya mai nisan gaske su dawo inda aka haifi iyayensu, don su rayu a wajen. Ta haka ne dai wadannan halittu suke rayuwa.

Babu shakka wannan kissa ce mai ban mamaki wacce za ta bar mu cikin tsananin tunani da kuma tambayoyin da Alkur'ani mai girma ya amsa su cikin wadannan ayoyi:

"....Ubangijinmu Shi ne Wanda Ya bai wa dukkan kome halittarsa, sa'an nan Ya shiryar". (Surar Daha, 20: 50)

Lalle Allah Shi ne Wanda Ya shiryar da shi da kuma ba shi irin wannan ilimi.

Hakika wadannan lamurra suna bayyana mana ma'anar fadinSa Madaukakin Sarki cewa:

"..Malamai ne kawai ke tsoron Allah daga cikin bayinSa....". (Surar Fadir, 35: 28)

Hakika ba za mu taba sanin Allah Madaukakin Sarki ba sai ta ilimin nan dai da Alkur'ani mai girma ya kiraye mu da mu neme shi, kamar kuma yadda ya kiraye mu zuwa ga tunani da kuma amfani da hankali wajen sanin Allah Madaukaki, sanin halittunSa da kuma fahimtar littafinSa mai girma:

"Shin to, ba za su kula da Alkur'ani ba, ko kuwa a kan zukatansu akwai makullansu?" (Surar Muhammad, 47: 24)

Hakika babban abin da zai kasance mana shamaki tsakaninmu da Ubangiji Tabaraka wa Ta'ala da kuma fahimtar littafinSa, shi ne jahilci, don kuwa daga lokacin da muka samu rabonmu na ilimi, kofofin sanin Allah za su budu mana, kana kuma hasken littafinSa zai haskaka zukatanmu.

Dubi Cikin Zatin

Dole ne in fahimtar da kaina, in san mutumci da kuma matsayina a rayuwa....lalle ni mutum ne, kuma babu shakka mutum yana da matsayi mai girman gaske cikin rayuwa, don haka yana da babban nauyi a rayuwarsa. Hakika an haife ni cikin mutumci da daukaka.... lalle Allah Madaukakin Sarki ya arzurta ni da dukkan wadannan hakkoki, kamar yadda kuma Ya arzurta ni da wani yanki na wannan rayuwa ta duniya. Allah Ta'ala Yana ce wa:

"Kuma lalle ne Mun girmama 'yan'Adam, kuma Muka dauke su a cikin kasa da teku, kuma Muka arzurta su daga abubuwa masu dadi, kuma Muka fifita su a kan masu yawa daga wadanda Muka halitta, fifitawa". (Surar Isra', 17: 70)

Sannan kuma kamar yadda aka halicce ni a kan fidira (hanya madaidaiciya), ina tsarkakakke daga dukkan sharri da mugun nufi, haka kuma aka halicci sha'auce-sha'auce da ji-a-jika tare da ni. Kana kuma na ci gaba da girma kana kuma kwakwalwata ta ci gaba da buduwa. Da wadannan ne na ci gaba da rayuwa....lalle hakki na ne in yi cikakken bayani dangane da dukkan wadannan abubuwa....sannan kuma in fahimci cewa ina da babban nauyin kulawa da kuma kiyaye wannan farar takarda ta rayuwata....

Lalle mutumci da kuma rayuwata ta gobe amana ce da take hannuna, ina da 'yancin tafiyar da ita kamar yadda nake so, sannan kuma in ja-goranci kaina duk yadda na so. Hakika hanyoyin rayuwa suna da yawa, akwai hanyoyin bata da kauce wa hanya, kana kuma akwai na alheri da shiriya.

Da dama daga cikin mutane sun kauce wa hanya, alhali kuwa tun ba su girma ba, wasunsu ma ba su wuce shekaru goma sha bakwai na rayuwarsu ba. Sun kasance masu zuwa kulob-kulob da kuma biyan sha'awarsu ta hanyoyin da ba su dace ba....

Lalle jahilci ko ji-ji da kai sun mamaye wadannan mutane, ko kuma sun bar borin mafarki da wahami ya hau kansu, ko kuma sun bari jin dadi da sha'awa sun ja-gorance su zuwa wuta, da kuma bata takardun ayyukansu. Hakika cibiyoyin binciken laifuffuka sun tabbatar da irin wadannan yanayi, ta yadda har al'umma suke kallon masu irin wadannan halaye kallo na wulakanci da cin mutumci. Da wuya ka ga wanda yake musu kallo tausayawa da kuma kokarin tsamo su daga irin wannan hali da suke ciki.

Ya ya Zan Yi Mu'amala Da Sha'awa Da kuma Karfina?

Zatin dan'Adam yana dauke da shu'urin so da kuma ki, yarda da kuma fushi, sha'awar abinci da kuma jinsi, son kai da iko, son dukiya, da kuma son doruwa a kan sauran mutane. Babu shakka irin wadannan abubuwa su ne suke tura mutum zuwa ga sharri da kuma munanan ayyuka; kamar yadda kuma suke tura shi zuwa ga ayyukan alheri da kuma abubuwan da shari'a ta yarda da su.

Don haka matsayi mafi inganci shi ne mu dinga tunanin karshen al'amari kafin mu je ga aikata shi, don mu san mene ne sakamakon wannan abin da muke son aikatawa, shin sharri ne ko alheri....

Kamar yadda kuma yana da kyau mu dinga amfani da kwarewar da wasu suka samu kan wannan abu da kuma shawartar wadanda muka yarda da su; kamar uba, uwa, dan'uwa, abokai, malamanmu, kwararru kan lamarin da dai sauransu.

Akwai abubuwa da dama da suke motsa dan'-Adam zuwa ga fushi, kiyayya, son kai, aikata laifi da kuma sanya kai cikin ayyukan da ba zai iya tsira daga mummunan sakamakonsu ba.

Tana iya yiwuwa wahami da kuma rashin tabbaci su auri mutum, ta yadda zai dinga kitsa wasu abubuwa da ba za su iya tabbatuwa ba ko kuma burace-burace don cimma biyan bukatan sha'awarsa, da suka hada da son dukiya, ko kuma shahara ko kuma wani matsayi da dai makamantan hakan. Don haka sai ya bata lokaci da dukiyarsa ba tare da ya samu wannan abu da yake burin samu ba, face ma dai dukkan wadannan abubuwa su tafi a banza.

Kana kuma tana yiwuwa sha'awa da kuma burace-buracensa na son jin dadi su sanya shi sabawa da wasu munanan dabi'u, kamar shan muggan kwayoyi, taba, zinace-zinace da sauran ayyukan da za su sanya shi cikin nadama da bala'i, ta yadda ba zai taba fahimtar haka ba sai bayan da lokaci ya kure.

Hakika yana daga cikin hikima da kuma sanin ya kamata kar mutum ya sake aikata kuskuren da ya riga ya aikata kuma ya ga sakamakonsa, kamar yadda kuma ya kasance yana daga cikin hikima kada mutum ya aikata kuskuren da waninsa ya aikata....lalle kwarewar makaranta tana koyar da mutum isa ga manufa da kuma yin kuskure. Don haka ya hau kansa ya yi amfani da kuskurensa da kuma kuskuren sauran mutane don gyara kansa da kuma tsira daga fadawa cikin kuskure.

Masu iya magana suna cewa: "Wanda ya jarraba abubuwan jarrabawa, to ya tsira daga nadama".

Imam Ali (a.s.) yana ce wa:

"Mai samun rabo shi ne wanda ya wa'aztu da waninsa"[1].

Girmama Halin Mutum:

Hakika mafi girman da kuma daukakan abin da mutum zai iya mallaka a rayuwarsa shi ne hali da kuma mutumcin kansa, hakan kuwa wata amana ce da take a kan wuyansa wacce Allah Madaukakin Sarki Ya daukaka shi da ita. Sannan kuma Ya haramta masa ha'intar kansa ko kuma kaskantar da ita da kuma ha'intar abin da Ya ba shi na kwarewa.

Imam Sadik (a.s.) ya yi bayanin wannan al'amari mai muhimmanci cikin fadinsa ce wa:

"Allah Madaukakin Sarki Ya bar (halalta) wa mumini dukkan kome in ban da wulakantar da kansa[2] ".

Lalle babban nauyin da ke kan mutum dangane da kan kansa shi ne ya kiyaye abin da zai zubar masa da mutumcinsa cikin al'ummar da yake raye a ciki. Don kuwa ayyukansa suna nan a kan idanuwan al'umman da yake tare da su, kada ya aikata wani abin da zai zubar masa da mutumcinsa ta yadda shi ma da kansa zai yi dan da-na-sanin wannan aiki.

Kamar yadda hanyoyin girmama zatin dan'Adam da kuma samar da daukaka ga mutumcinsa suke da yawa, haka ma hanyoyin ha'intar kai da kuma zubar da mutumci suke da yawa....

Misali, karya da ta'addanci a kan al'umma, ya kan haifar da wulakantar da kai, haka ma aikata muggan ayyukan da suka saba wa dabi'u na kwarai, yarda da wulakanci ko don saboda neman kudi, jin dadi ko matsayi, duk hakan suna haifar da wulakanci, munafunci, tsoro.....da dai sauransu.

Haka nan kuma jin kaskanci da kuma sanya wa zuciya tunanin gajiyawa ta rashin iya aikata wani aiki, hada kai cikin aikin alheri da kuma hidima ga al'umma, duk hakan sukan kashe zuciyar mai yin su.

Don kuwa Allah Madaukakin Sarki Ya arzurta dukkan 'yan'Adam da karfi da kuma iyawa, don haka ya rage musu ne kawai su yi amfani da su wajen cimma manufarsu ta rayuwa. Don haka ba ya halalta gare su da su yi wasa da karfi da ikon da Allah Ya ba su.....

Hakika Allah Madaukakin Sarki ba Ya haramta wa bayinSa ni'imominsa....wasu suna da karfin fahimtar ilimin magani, wasu kuwa ilimin yare, wasu kuma karfin kirkiro abubuwa suke da shi. Sannan wasu kuma karfin kasuwanci suke da shi, wasu kuma na ayyukan hannu suke da shi, wasu kuma na iya gudanar da mulki suke da shi, sannan wasu kuma karfin siyasa da ayyukan soji suke da shi....da dai sauransu.

Haka lamarin yake, don kuwa dan'Adam yakan gano iko da karfin da Allah Ya yi masa ne ta hanyar gwaji, don haka kada mutum ya wulakantar da abin da Allah Ya arzurta shi na daga karfi da kuma iko.

Sau da dama mutane sukan wofantar da kwarewa da kuma karfin tunani da kuma na aiki da Allah Ya ba su saboda yanke kauna da kuma jin gazawa. Ta hakan sai ka ga sun lalata karfin da suke da shi da kuma hana kansu hakkin da ya dace da ita da kuma hana ta damar ci gaba da kuma samun nasara.

Lalle babu shakka, yarda da kai, buri da kuma kokari sukan karfafa rai da kuma ba ta dukkan abin da take bukata wajen ci gaba da kuma gudanar da ayyukanta kamar yadda ya dace. Don kuwa dogaro ga Allah da kuma yarda da kai, mabudi ne na aiki da kuma cimma nasara a rayuwa.

Dan'Adam Da Al'ummarsa

Al'umma, adadi ne na wasu mutane ko kuma zuriya wadanda suke da alakoki daban-daban a tsakanin junansu, kamar alaka ta akida ko kuma ta kusanci, ko kuma suna da manufa iri guda, ko kuma alaka ta tarihi da dai sauransu.

Kowane mutum yakan ji kusanci ko kuma jinginuwa ga zuriyarsa ko kuma al'ummar da ya fito daga cikinta, hakan kuwa don shi wani sashi ne na wannan zuriya ko kuma al'umma....

Mutum da al'ummarsa sukan yi musanyan amfanoni da suke samu a tsakaninsu. Haka nan ma ta hanyar al'umman da yake rayuwa a cikinta yakan iya tabbatar da hanyar rayuwarsa, dabi'u da kuma tunaninsa.....

Lalle ba makawa dan'Adam yana da manufofi da yanayi masu cin gashin kansu, kamar yadda al'umma ma take da tata manufofi da yanayi masu cin gashin kansu. A lokuta da dama akan sami rashin jituwa tsakanin manufofin mutum da na al'ummarsa; don haka ne dokokin mutane da na Ubangiji suka ba da muhimmanci wajen tsara irin wadannan alakoki da kuma magance irin wadannan karo da juna da ake samu tsakanin manufofin guda biyu: na mutum da na al'umma....

Koyarwar addinin Musulunci ta ba da muhim-mancin gaske wajen kyautata rayuwar mutum da ta al'umma; don kiyaye hakkokin wajibi na dan'-Adam, kamar yadda kuma ilmummukan kyawawan dabi'u da na zamantakewa suka ba da muhimmanci wajen gyara rayuwar mutum da ta al'umma, da kuma tabbatar da su bisa asasin kyawawan dabi'u da kuma 'yantaccen shu'uri.....

Ko da yake wasu daga cikin mutane sun fi damuwa da tabbatar da manufofin kansu, ba tare da la'akari da manufofi da matsalolin sauran mutane ba....

Misali, dan kasuwan da ke boye abinci da kuma masu sanya kayayyaki su yi tsada, ba sa wani tunani in ban da yadda za su sami riba mai yawa. Ba sa tunanin irin halin da fakirai marasa abin hannu za su shiga saboda tsadar kayayyakin bukatun yau da kullum, su dai babban burinsu shi ne samun riba....

Haka nan mabukaci, ba ya tunanin kome face yadda zai biya wannan bukata ta sa ba tare da tunanin bukatun sauran mutane ba. A wasu lokuta, hakan kuwa yakan sabbaba wa mutane matsaloli masu yawan gaske.....
Haka nan ma mutumin da yake da wata manufa ta siyasa, ba ya barci har sai ya cimma wannan manufa ta sa, ko kuma isa ga wani matsayi na siyasa da yake bukata. To amma idan har ya samu biyan wannan bukata, sai ka ga ba abin da ya dame shi na daga irin matsaloli da wahalhalun da sauran mutane za su shiga na rayuwa da kuma siyasa.....

Haka kuma manomin da ya mallaki wata gona, ba ya hada kai da sauran manoma wajen samar da ruwan da za su yi amfani da shi a gonakin nasu matukar dai gonarsa ta samu ruwan.

Irin wadannan mutane ba sa dubin lamurra da kuma matsaloli face in suna da manufa da maslaha a cikinsu.

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi bayani kan wannan matsala ta zamantakewa mai matukar muhimmanci, da kuma kan wannan son kai wanda yake matukar cutar da maslahohin al'umma. Inda yake ce wa:

"Babu wanda zai yi imani daga cikinku (musulmai) har sai ya so wa dan'uwansa abin da yake so wa kansa na alheri[3] ".

Ta haka ne Manzon Allah (s.a.w.a.) ya hada tsakanin tunani kan maslahohin al'umma da kuma fita daga son kai na mutum guda. Don mutum ma'abucin son kai wanda ba ya tunanin maslahohin al'umma, ba mumini ne na gaskiya ba. Kana kuma duk wanda ba ya tunanin maslahar sauran mutane, to babu wanda zai yi tunanin maslaharsa....to hakan kuwa zai kasance babbar kafar ungulu ga hadin kan al'umma da kuma ci gabanta.

Matukar dai ingantaccen shu'urin taimakekke-niya bai tabbata ga mutum da al'umma ba, kana kuma matukar babu wasu dokokin da za su kiyaye maslahohin mutum da na al'umma.... to ba makawa al'umma za su zamanto cikin rashin tsari da son zuciya, kana kuma da yawa daga cikin mutane za su kasance cikin wahalhalu. Daga nan kuma sai masu karfi su samu daman cutar da marasa karfi da kuma takura masu rayuwa....

Hakika shu'urin taimakekkeniya da kuma na kyawawan dabi'u da suke tare da mu, bugu da kari kan ka'idoji na Ubangiji madaukaka, suna kiranmu zuwa ga kiyaye maslahohin al'umma, kamar yadda kuma suke kiranmu zuwa ga kula da maslahohin da suka kebanta gare mu. Kuma a lokuta da dama maslahohin mutum guda sukan cutar da maslahohin al'umma, don haka ya zama wajibi mu nesance su.

A matsayin misali, lalatawa da kuma kara kudi a kan takardun kudi (rasidin kudi) yakan samar da makudan kudade ga masu wannan mummunan aiki, sai dai kuma hakan yakan haifar da mummunan gibi ga tattalin arzikin al'umma. To don haka ne ma dokokin Musulunci suka haramta wannan aiki da kuma hukumta masu yin sa.

To amma cikin ayyukan tsarkakakkun mutane muna iya ganin daidaituwa kan maslahar mutum shi kadai da kuma ta al'umma.... Daga cikin irin wadannan kyawawan ayyuka shi ne abin da aka ruwaito daga Shugaban musulmi, Abu Abdullah, Ja'afar bin Muhammad al-Sadik (a.s.). An ruwaito daya daga cikin sahabbansa (sunansa Mu'attab) wanda shi ne mai kula da harkokin cikin gidansa yana cewa:

"Wata rana Abu Abdullah ya ce min, a lokacin kuwa farashin kayayyaki ya tashi a garin Madina,: ya ya yawan abincin da muke da shi?, sai na ce masa: muna da abin da zai ishe mu na tsawon watanni. Sai ya ce: Fitar da shi ka sayar wa mutane, sai na ce masa: babu abinci a garin Madina fa. Sai ya ce: ka sayar dai, to lokacin da na sayar, sai ya ce min: je ka dinga saya tare da mutane rana-rana.

Sai Imam Sadik ya ce: Ya Mu'attab, ka sanya abinci iyalaina ya zamanto rabi sha'iri rabin kuwa alkama, hakika Allah Ya san cewa ina da karfin ciyar da iyalaina da alkama, to amma ina son Allah Ya gan ni ina kyautata rayuwa gwargwadon bukatata[4]".

Wannan kissa tana nuna mana irin yadda Musulunci yake ba da muhimmanci a aikace ga al'amurran da suka shafi al'umma.

Don Imam Sadik (a.s.) ya ki yarda ya ajiye abincin da zai ci na watanni ga iyalinsa, a daidai lokacin da sauran al'umma suke cikin rashi da kuma kuncin abin da za su ci na rana guda. Kana kuma ya aikata hakan ne don wanda yake da karfin sayan abinci da yawa ya tara a gidansa ya nesance yin hakan don a samu kayayyakin abincin a kasuwa da yawa, ta yadda kudinsu za su sauko kasa kuma marasa karfi su sami daman saya.

A nan za mu ga ce wa Imam Sadik (a.s.), kamar yadda ya ba da muhimmanci ga al'amarin al'umma, to haka ma a bangare guda ya bai wa lamarin kula da iyalansa nasa muhimmancin shi ma. To wannan shi ne cikakken imani na gaskiya.

A nan yana da kyau a fahimci cewa, abu mai wahalar gaske ga mutumin da ya cutar da al'umma shi ma ya tsira daga zafin wannan cutarwa, don kuwa a dabi'ance mutum yana so ya rayu cikin al'umma wacce take cikakkiya wacce ta tsira daga dukkan cutarwa. To don haka matukar dai al'umma ba su tsira daga cutarwa ba, shi ma ba zai tsira ba, don kuwa shi ma cikin wannan al'umma yake raye.

Gaskiya da Wajibi:

Dukkan wata halitta a wannan duniya tamu, tana da wata siffa ta taimakekkeniya da 'yan-'uwanta, tana bayarwa da kuma karba daga 'yar'uwan nata. Misali, mutum, dabbobi, tsirrai da dabi'a, duk suna jujjuya amfani tsakaninsu, da suka hada da iskar "oxygen" da "carbondioxide", abinci, haske, ruwa....da dai sauransu.

Haka shi ma mutum, yana rayuwa ne cikin iyali da al'ummarsa, yana alaka da sauran mutane kana kuma suna jujjuya amfanoni a tsakaninsu. Don haka yana da hakkoki a kan iyali da kuma al'ummarsa, kamar yadda su ma suke da hakkoki a kansa....

Ko wane mutum yana da hakki, yana kuma da wajiban da suka hau kansa, to amma wannan daidaituwa ta al'ummance da dokoki na al'umma ba za su taba tabbatuwa ba kana kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali ba za su samu ba, har sai an kiyaye wadannan al'amurra....

Hakika duk wanda ya bukaci wani abin da ba hakkinsa ba ne, to ba makawa yana zaluntar sauran mutane ne, don kuwa so yake ya bautar da al'umma. A sabili da haka ne al'umma suke ki da kuma jefar da shi.

Dan'Adam yana da hakkin rayuwa, kamar yadda kuma rayuwar hakkinsa ce, haka nan ma samar masa da abubuwan da rayuwar take bukatuwa da su....sannan kuma yana daga cikin hakkinsa a bude masa hanyoyin ayyuka da kuma 'yancin samun abin hannu da kuma mallaka....kuma hakkinsa ne ya samu nasa rabon na albarkatun kasar da yake raye cikinta....

Muna iya ganin hakkokin dan'Adam a fili cikin fadin Allah Madaukakin Sarki:

"Kuma kasa ya aza ta domin talikai". (Surar Rahman, 55: 10)

Don haka an sanya kasa ne don kowa da kowa ya amfana da ita, kuma ba ya halalta ga wani mutum ya ajiye ta a matsayin kayansa kawai ya hana saura amfanuwa da ita.....

Dan'Adam wani sashi ne na wannan al'umma, yana da hakkin amfanuwa da dukkan abubuwan da suke cikin al'ummarsa....

Hakika kange amfani da alherorin da suke cikin kasa ga wata al'umma ko kuma kungiya da kuma haramta wa wata, zalunci ne da kuma gaba da dokokin rayuwa da kuma ka'idojin adalci.... Alkur'ani mai girma yana tabbatar da wannan ka'ida cikin fadinSa Madaukakin Sarki:

"Lalle Allah Na yin umurni da adalci da kyautatawa....". (Surar Nahl, 16: 90)

Don haka "mutane daidai suke kamar hakwaran matsefin kai", kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fadi.

Lalle babu makawa a duk lokacin da mutane suka yi shiru kan zalunci da kuma babakeren da ake musu, to cutarwar za ta koma ga kowa da kowa ne, daga karshe sai ya zamanto wata kungiya ta azzalumai ta hau kan dukkan al'umma da kuma raunana ta.

Don haka, kamar kowane mutum yake kokari wajen sama wa kansa 'yanci, haka nan ya za ma wajibi a kansa ya yi kokari wajen samar wa sauran mutane ma, kada ya takaita shi ga kansa kawai.

Sannan kuma yana daga cikin hakkin dan'Adam ya rayu cikin tsaro da kwanciyar
hankali, shi da dukiyarsa da kuma dukkan abin da ya mallaka, hana shi wannan 'yanci kuwa zalunci da babakere ne wanda mai aikata hakan ya cancanci azaba.

Kana kuma kamar yadda hakan ya zamanto 'yancinsa, haka nan ma ya zamanto 'yancin wasunsa ne....don haka a duk lokacin da ya yi wasa da tsaron lafiyar wasunsa, ko kuma ya aikata wani abin da zai tsoratar da su, ko kuma ya haifar da rashin tabbas da kwanciyar hankali a cikin mutane, to ba makawa ya zamanto abokin gaban al'umma, kuma hakan ma wasa ne da tsaron kan kansa shi ma.

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya tabbatar da ka'idar tsaro da kwanciyar hankalin al'umma cikin fadinsa cewa:

"Musulmi dan'uwan musulmi ne, don haka kada ya cutar da shi, ko ha'intarsa ko ya fadi mummunar magana dangane da shi. Sannan kuma jininsa ba ya halalta a gare shi, haka ma dukiyarsa sai da yardarsa[5] ".

Daraja da daukakar dan'Adam tana ga mutumci da karamarsa ne, don haka shari'ar Musulunci ta haramta giba, bata suna, yada kararraki da zubar da mutumcin mutum ta hanyar magana ko aiki ko kuma ta hanyar bincike da bayyana asirin mutum da dai sauransu.

Wannan doka ta Musulunci tana wajabta wa mutum girmama mutumcin sauran mutane, kan kuma ba ya halalta ya keta hurumin sauran mutane....

Allah Madaukakin Sarki Yana ce wa:

"Ya ku wadanda suka yi imani! Kada wadansu mutane su yi izgili game da wadansu mutane, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (masu izgilin), kuma wadansu mata kada su yi izgili game da wadansu mata mai yiwu-wa ne su kasance mafifita daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jefi juna da miyagun sunaye na lakabobi. Tir da suna na fasicci a bayan imani. Kuma wanda bai tuba ba, to, wadannan su ne azzalumai. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku nisanci abu mai yawa na zato. Lalle sashen zato laifi ne. kuma kada ku yi rahoto, kuma kada sashenku ya yi gibar sashe. Shin dayanku na son ya ci naman dan'uwansa yana matacce? To, kun ki shi (cin naman). Kuma ku bi Allah da takawa. Lalle Allah Mai karbar tuba ne, Mai jin kai". (Surar Hujurat, 49: 11-12)

Haka nan kuma mutum yana da wasu hakkoki a kan al'umma da kuma kasarsa, wadanda gwam-nati ce take daukan mafiya yawa daga cikinsu; wadannan hakkoki sun hada da bayar da ilimi, tarbiyya, kula da samar da tsaro, kiwon lafiya da dai sauransu....

Kamar yadda kuma kasa da al'umma suke da wasu hakkoki a kan mutum, kamar su kiyaye maslahohin al'umma da kuma kare su, bugu da kari kan wajiban da suka hau kansa wadanda doka ta yi bayaninsu, wadanda matukar dai bai kula da kuma kiyaye su ba, to rayuwar al'umma za ta kasance tana fuskantar matsaloli da kuma rugujewa. A irin wannan hali shi ma ba zai tsira daga bala'in da zai fada wa sauran al'umma ba.

Ya Ya Za Mu Fahimci Rayuwa?

Wannan rayuwa da muke cikinta....ya ya za mu iya fahimtarta?....kana kuma ya ya za mu yi mu'amala da ita?

Rayuwar dan'Adam ita ce ayyukan jiki, tunani da na ruhi da mutum yake aikatawa tun daga haihuwarsa har zuwa mutuwarsa. Kuma ta hakan ne yake tabbatar da samuwarsa da kuma cika zati, ruhi da kuma yanayinsa....

Yakan cika hakan ne kuwa ta hanyar abubuwan da ya mallaka, na daga rayuwa, hankali, karfin yanayin abubuwan da suke kewaye da shi, jin dadi da kuma ciwo, gano abubuwan halitta da hankalinsa yake yi....da dai sauransu.

Hakika mun kasance muna ci da sha, muna sa tufafi, muna wasa da jin dadin kyawawan abubuwa, muna yin jima'i, muna jin soyayya da kiyayya, farin ciki da bakin ciki, jin dadi da kuma jin zafi, muna dariya da kuka, mukan yanke kauna kan al'amurra da kuma burace-burace....

Sannan kuma mukan yi tunani da kuma kirkiro abubuwa, mukan gano sabbin abubuwa sannan kuma mu sanya wasu, kuma mukan yi bayanin abubuwan da suke damunmu ta hanyar magana, rubutu, wake, farin ciki da kuma bakin ciki.

Kana kuma mukan gano abubuwan da suka fita daga wannan duniya tamu ta hanyar hankali da kuma tunaninmu, muna masu tunanin girmansu da kuma yadda aka samar da su. Kuma mukan gano ka'idojin samuwa da kuma Wanda Ya samar da ita....

Hakika mun kasance muna tunani, muna ji, muna aiki, kuma mukan tsara rayuwarmu da tunani da kuma shu'urinmu, da kuma ayyukan da suke fitowa daga gare mu.....

Mu mun kasance jiki, ruhi da kuma hankali ne wadanda aka arzurta mu da su. Mu muke sana'anta rayuwarmu kamar yadda mai zane yake zana hoto.... rayuwar kowanne daga cikinmu hotonsa ne na zati, to a cikinmu wane ne yake so hotonsa (zatinsa) ya kasance abin kyama....

Hakika rayuwa ba wai jin dadi da annashuwa ba ce kawai, face dai tana hade da abubuwan bakin ciki da dacin rai kuma. Ita ba wai kawai sakaka take ba.... face dai ita nauyi ce....nauyi ce a gaban Allah Ta'ala, nauyi ce a gaban al'umma da kuma mutanen da muke rayuwa da su. Sannan kuma nauyi ce a gaban dokoki, mutumci da kuma

Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:

"Sa'an nan lalle ne Muna tambayar wadanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Muna tambayar Manzannin".(Surar A'araf,7: 6)

Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:"Dukkanku makiwata ne, kuma dukkanku abin tambaya ne kan abubuwan da aka ba ku kiwonsu".

Hakika Ubangijin halitta Ya yi bayanin dabi'ar rayuwa, kuma Yakan buga misalai wadanda za su kusanto da lamurra zuwa ga hankulanmu....Ya yi bayanin cewa ita (rayuwa) aiki ne na girma, daukaka da kuma kamala, kana kuma daga baya ta zamanto abin jefarwa da kuma karewa. To haka rayuwar ko wane mutum a wannan duniya take....

"Ka buga musu misalin rayuwar duniya, kamar ruwa ne wanda Muka saukar da shi daga sama, sa'an nan tsirin kasa ya garwaya da shi, sa'an nan ya wayi gari dudduga, iska tana shikar sa. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan ikon yi ne a kan dukkan kome". (Surar Kahf, 18: 45)

Don haka rayuwa, duk da irin kawa, kyau, jin dadi da annashuwan da ke cikinta, wata aba ce samammiya kana mai karewa, kamar yadda tsirrai sukan girma su yi fure masu kyau, amma daga baya su yi 'ya'ya kana su bushe iska ta debe su....

A lokacin da wannan marhala ta rayuwar mutum ta kare, sai kuma wata sabuwar marhala ta rayuwar tasa ta kunno kai, ita ce kuwa rayuwar lahira. Wannan kuwa ita ce dawwamammiyar rayuwa....duniyar da babu wani canji ko gushewa a cikinta....duniyar ni'ima, kyau da kuma jin dadi, ko kuma duniyar tabewa da kuma azaba.

Hakika abin da ke tabbatar da makomar mutum a wancan duniyar, shi ne yanayin ayyuka da kuma akidarsa a wannan duniya....kamar yadda kokarin dalibi yake tabbatar da sakamakon jarrabawarsa da kuma ci gaban karatunsa.....

Lalle a wannan rayuwa ce mutum yakan share fagen rayuwarsa ta lahira, kamar yadda duniyar mahaifa take share fagen rayuwa duniya.

Alkur'ani mai girma ya yi mana bayanin wannan hakika cikin fadinSa Ta'ala ce wa:

"Wanda ya kafirta, to, kafircinsa na kansa, kuma wanda ya aikata aikin kwarai, to, saboda kansu suke yin shimfida". (Surar Rum, 30: 44)

Don haka ne dokokin Ubangiji suka zo don tsara ayyukan dan'Adam da kuma yanayin rayuwarsa.....

Abu ne mai yiwuwa mutum ya bi sha'awace-sha'awacensa, jin dadi da kuma annashuwa, ko kuma ji-ji da kai, jahilci ko kiyayya su sami iko a kansa, ta haka sai rayuwa ta kasance wata hanya ce ta biya sha'awa da jin dadi a gare shi. Ko kuma ta kasance hanya ce ta aikata laifuffuka da yada fasadi a bayan kasa da kuma bauta ga jin dadin duniya saboda son zuciya da kuma ji-ji da kai.

Hakika Mahaliccin rayuwa Ya bai wa mutum ita (rayuwa) ce don ya rayu cikin kwanciyar hankali da jin dadin abubuwan jin dadin cikinta da kuma kawaice-kawaicenta, gwargwadon yadda dokokin kiyaye rayuwa da kuma kyautata dabi'u suka tanadar. Ta yadda zai iya tabbatar da alheri a kansa da kuma al'umma da yake rayuwa a cikinta....

Babu shakka, a lokacin da mutum ya yi kuskuren fahimtar rayuwa, to lalle zai cuci rayuwarsa da kuma ja-gorantarta zuwa ga halaka, kuma da wuya ya iya gane wannan kuskure na sa sai bayan gushewar lokaci.

Don da yawa daga cikin mutane, sha'awoyi, son zuciyarsu da kuma gururi sun kai su zuwa ga halaka da kuma nadama, hakan kuwa bayan kurewar lokaci..

Rayuwar irin wadannan mutane ta kare a gidajen yari daban-daban, kashe kai, kamuwa da muggan cututtukan jima'i (irinsu ciwon AIDS da dai sauransu), shan muggan kwayoyi, damuwa, tabewa da dai sauransu.

Cibiyoyin kididdiga da bincike irin su asibitoci, cibiyoyin lafiya da kuma na muggan laifuffuka sun

tabbatar da adadi mai yawan gaske na faruwar irin wadannan laifuffuka a tsakanin al'umma....

Hakika rayuwarmu kyauta ce ta Ubangiji Mai rahama, don haka dole ne mu yi mu'amala da rayuwarmu daidai da dokokin kiyaye lafiya da kuma rayuwa. Hakan kuwa su ne dokokin Ubangiji, Wanda Ya haramta mana duk wani abin da zai cutar da mu, sannan kuma ya halalta mana dukkan alherori da jin dadin da suke da amfani a gare mu....

Akwai hanyoyi na fahimtar rayuwa, don haka wajibi ne mu koma gare su da kuma dogaro da su. Wadannan hanyoyi kuwa su ne:

  1. Littafin Allah da kuma shiryarwar Annabci; wadannan abubuwa guda biyu suna mana cikkakken bayanin rayuwa da kuma hanyoyi da tafarkin shiriya cikin rayuwarmu. Don haka dole ne mu karanta su tare da tunani da kuma cikakkiyar fahimta, don mu san abin da ke cikinsu na alheri da kuma hikima.
  2. Mabubbuga ta biyu na fahimtar rayuwa shi ne ilimi da bincike-bincikensa. Hakika ilimi ya arzurta mu da masaniya da kuma fahimta, ta yadda ya iya bayyana mana abubuwa masu cutarwa da kuwa masu amfanarwa. Sannan kuma wadannan abubuwa da ilimi ya tabbatar da su sai suka yi dai-dai da abin da Alkur'ani mai girma ya tabbatar na haram da halal....

Hakika ilimi ya gano hadarin da ke tattare da giya, muggan kwayoyi, zinace-zinace, cin kudin ruwa, haka nan kuma ya gano fa'idar tsabta, soyayya, sada zumunci tsakanin 'yan'uwa da kuma tasirin da yake da shi wajen kiyaye zaman lafiyan al'umma, da kuma tasirin imani wajen sa'adar dan'Adam, tabbatuwa cikin dabi'u na kwarai, tsira daga damuwa da kuma muggan laifuffuka.....da dai sauransu.

Kamar yadda ilimi kuma ya ba da gagarumar gudummawa wajen daga martabar fahimtar dan'-Adam ga rayuwa, ci gabantar da hanyoyin kerekere da kuma tsara rayuwar al'umma. Ya taimaka wajen biyan bukatun dan'Adam da kuma samo sabbin hanyoyi magance matsalolin rayuwa.

Babu makawa, kirkiro wutan lantarki, man fetur, radiyo da talabijin, hanyoyi rubutu da buge-buge da kuma na safara da dai sauransu, sun bude wa dan'-Adam sabuwar fahimta ta rayuwa. Kuma sanannen abu ne cewa a duk lokacin da fahimta da masani-yarmu da rayuwa ta karu, fahimtarmu ga addini da ma'anar imani ma za ta karu. Don haka ilimi abu ne da yake kira zuwa ga imani kana kuma abokin zaman rayuwa.

  1. Hankali da kwarewa: Hankali shi ne fitilar dan'Adam a rayuwarsa, don haka a duk lokacin da mutum ya yi amfani da hankali kamar yadda ya dace, to ba makawa zai kai shi ga alheri da kuma tsamar da shi daga halaka, bata da kuma nadama.

Dan'Adam ya kasance mai aikata abubuwa da daman gaske a rayuwarsa, don haka ya mallaki kwarewa daban-daban a rayuwartasa. A saboda haka, ya za ma dole ya yi amfani da wannan kwarewa da ya samu wajen kyautata rayuwarsa, kamar yadda kuma yake wajibi ya yi amfani da kwarewar sauran mutane a dukkan bangarori na rayuwarsa shi kadai, da na aure, tattalin arziki, siyasa, wayewa da dai sauransu.

A saboda haka ne ma, Alkur'ani mai girma ya yi mana umurni da amfani da hankali da kuma kwarewar al'umman da suka wuce. Don kuwa kwarewar mutane da kuma abubuwan da suka faru a baya na tarihi, bugu da kari kan abubuwan da hankali mutum ya kirkiro na ilimi, hikima da dai sauransu, abubuwa ne da suke taimakawa, nesa ba kusa ba, wajen tabbatar da kyakkyawar rayuwa da kuma bube sabbin kofofin fahimtarta.

Don haka ne Alkur'ani mai girma yake shiryar da mu zuwa ga amfani da kwarewar al'ummomi da kuma daidaikun mutane bugu da kari kan tunani da kuma amfani da hankali. Allah Madaukakin Sarki Yana ce wa:

"Kuma Shi ne Wanda Ya shimfida kasa, kuma Ya sanya duwatsu da koguna a cikinta, kuma daga dukkan 'ya'yan itace Ya sanya ma'aura biyu cikinsu. Yana sanya dare ya rufe yini. Lalle ne a cikin wancan, hakika akwai ayoyi ga mutane wakanda suke yin tunani". (Surar Ra'ad, 13: 3)

"Kuma ba Mu aika ba a gabanninka face mazaje, Muna wahayi zuwa gare su, daga mutanen kauyuka. Shin fa, ba su yi tafiya a cikin kasa ba, domin su duba yadda karshen wadanda suka kasance daga gabanninsu ta zama? Kuma lalle ne gidan Lahira shi ne mafi alheri ga wadanda suka yi takawa, shin fa, ba ku hankalta? Har a lokacin da Manzanni suka yanke tsammani, kuma suka yi zaton cewa an jingina su ga karya, sai taimakonMu ya je musu, sa'an nan Mu tserar da wanda Muke so, kuma ba a mayar da azabarMu daga mutane masu laifi. Lalle ne, hakika, abin kula ya kasance a cikin kissoshinsu ga masu hankali. Bai kasance wani kirkiran labari ba, kuma amma shi gaskatawa ne ga abin da yake a gaba gare shi, da rarrabewar dukkan abubuwa, da shiriya da rahama ga mutane wadanda suka yi imani". (Surar Yusuf, 12: 109-111)

An ruwaito Imam Ali (a.s.) yayin da yake huduba ga dansa Imam Hasan (a.s.), yana shawartarsa da yin amfani da kwarewar sauran mutane, inda yake ce masa:

".....don ka shirya wa karbar kwarewar wasunka ta hanyar tunaninka, don ka tsira daga fadawa cikin abubuwan da suka fada. Ta haka sai ka tsere wa wahalar nemansa da kuma wahalar gwaji. Don haka, sai ka ga ka san abin da muka gani kana muka shaida da ma abubuwan da suka bayyana maka wadanda watakila mu ba mu riske su ba....."[6] .

Hakika a duk lokacin da muka samar wa kawukanmu ingantacciyar fahimta ta rayuwa, bisa ka'idojin shari'a, hankali da kuma ilimi, to za mu sami damar tafiyar da rayuwarmu cikin jin dadi da kuma nasara.


[1] Mizan al-Hikma na Muhammad Ri Shahri, juzu'i na 4 /(al-Sa'adah).

[2] Mizan al-Hikma na Muhammad Ri Shahri, juzu'i na 3 / (al-Zilla).

[3] Mizan al-Hikma na Muhammad Ri Shahri, juzu'i na 1 / (Hakikat al-Imam), shafi na 395

[4] Al-Kafi na Kulaini / juzu'i na 5/ shafi na 166, Darul Kutub al-Islamiyya.

[5] Al'Ya'akubi / juzu'i na 2 / hudubar ban-kwana /shafi na 110/ Dar Sadr - Beirut.

[6] 1- Nahjul Balagah / hadawar Dr. Subhi Salihi / shafi na 393.