SHINGEN MATASA

Wadda Ta Wallafa: MU'ASSASAR AL-BALAGH

Wanda Ya Fassara: MUHAMMAD AWWAL BAUCHI

Gabatarwa

Wannan dan karamin littafi, "Dandalin Matasa" ne ya tsara shi don ya kasance a gefen samari da 'yan mata (matasa) a wannan lokaci mai muhimmanci na rayuwarsu, don ya taimaka musu wajen fahimtar hakikanin wannan lokaci na rayuwa da kuma abubuwan da suka kewaye shi.....

Wannan lokaci da muke magana a kansa kuwa shi ne lokacin da mutum ya kawo shekarun balaga. Wannan lokaci kuwa shi ne wanda ko wane mutum yake bukatuwa da shi don gina kansa da kuma tabbatar da dukkan abin da yake son cimmawa a rayuwarsa.

"Dandalin Matasa" yana dubin wannan lokaci na samartaka ne a matsayin nauyi da kuma amana, kuma ya yi imani da cewa dukkan abin da matashi ko matashiya suka mallaka a wannan lokaci na daga tunani, tausayi, ji-a-jika, karfi, kai da ma dukkan wata ni'ima, taskoki ne da Allah Madaukakin Sarki Ya ba wa dan'Adam don ya yi amfani da su a tafarkin alheri da sa'ada, ban da tafarkin lalacewa da bata.

Don haka wannan littafi "Shingen Matasa", wani kokari ne na daban daga "Dandalin Matasa" a kan maudu'in matasa da kuma abubuwan da suka shafe
su...muna fatan wannan littafin zai kasance mai amfani ga matasa, wadanda su membobi ne na wannan dandali a duk inda suke.

MU'ASSASAR AL-BALAG

Sabbin Canje-Canje

Dukkanmu mun shaidi lokacin bazara, kana kuma mun rayu a cikin yanayinta mai kyaun gaske da kuma kwantar da hankali.....kowane abu a lokacin baraza yakan fara ne daga farko.....furanni sukan budu a kan bishiyoyi su cika ko'ina da kamshin da ke jikinsu..... gonaki kuma su cika da korayen ganyaye.....tsuntsaye kuwa su cika sama suna shawagi cikin farin ciki da annashuwa saboda irin wannan yanani mai dadi..... kwari su ma haka suna ta rawa da yawo tsakanin furran bishiyoyi ..... haka nan sama ma za ta yi kyau.....

Wannan yanayin bazara kenan, motsi, ci gaba da kuma haihuwa.....

Haka Allah Madaukakin Sarki Ya so rayuwar dan'Adam ta kasance kamar fasalin shekara, ya kan fara daga lokacin bazara ya kare a lokacin girbi. Bazarar rayuwar mutum takan fara ne daga lokacin haihuwarsa har zuwa lokacin samartakansa..... wannan lokaci na balaga ko kuma abin da ake ce ma shekarun samartaka suna a matsayin lokacin shuka ne na rayuwa......

A wannan lokaci ne kowane mutum yakan gano sabuwar duniyarsa kamar yadda matafiya suke gano sabuwar kasa, inda zai tafiyar da sauran abin da ya rage na rayuwarsa a gurin......

Misali, tsuntsu, a lokacin da yake karami, bai san komai ba face 'yar shekar da mahaifiyarsa ta shirya masa, yana ci daga abin da mahaifiyar tasa ta kawo masa. Amma idan ya fara girma, fukafukansa suka fara yin karfi, sai ya fara koyon tashi sama yana yawo kan bishiyoyi da koguna, yana mai zaba wa kansa abin da yake so na daga hatsi da 'ya'yan itatuwa.

Kamar yadda kuma tsutsar tsamiya a farkon rayuwarta take samun abincinta a jikin ganyen bishiya; ta yafato ganye daga wannan reshen bishiyar ta yafato daga wancan, kana sai ta rufe kanta cikin dakinta. Bayan wani lokaci kuma sai ta fito da abin da yake daukan ido saboda kyaunsa, to haka rayuwa take ga saurayi ko budurwa a wannan lokaci na rayuwarsu.......

Sannan kuma tsiro yakan fito daga cikin kasa don ya girma a kan kasa, inda daga baya yakan girma ya yi ressa har ya zamanto babbar bishiya mai rassuna da kuma 'ya'ya masu zaki.....

To mu ma muna ganin irin wannan haihuwa da girman jikkunanmu, misali, hakora su kan fasa dasorin jariri don ya sami damar tauna abinci mai tauri, sannan daga baya kuma hakora dawwamam-mu su fito bayan wasu shekaru don su maye gurbin wadancan na farkon.....

Lalle babu makawa abubuwan da suke faruwa garemu na daga canje-canjen samartaka shi ya fi muhimmanci a kan fitowan wadannan kwari ko kuma fitowan wadannan hakora ga jariri.....don haka dole ne mu ba da muhimmancin gaske ga wadannan sabbin canje-canje da suke faruwa a wannan lokaci na rayuwa, don mu kyautata mu'amalarmu kana kuma mu ribanci rayuwarmu kafin mu kai shekarun tsufa.....

Hakika wannan canji yana bukatuwa da fahimta, hakuri, juriya da kuma jin nauyi abin da ke kanmu.

Don kuwa ingantacciyar fahimta ita ce take hada mu da rayuwa kai tsaye, sannan kuma ta nuna mana asalin ni'imomi na hakika......

Shi kuwa jin nauyi yakan ingiza mu zuwa ga abubuwan da muke bukata a wannan rayuwa, ta yadda komai zai kasance mai amfani a gare mu.....

Hakuri da juriya kuwa muna bukatansu don tafiya a kan tafarkin da zai kai mu zuwa ga kofofin shiriya da daukaka......

Lalle duk wani matashin da ya yi kyakkyawan shiri wa rayuwa, zai sami jin dadi da kuma sa'ada a rayuwarsa.....don kuwa kofofin rayuwa a bube suke musamman ma ga wanda yake wannan mataki.

Yadda Za Mu Fahimci Lamurra....
Yadda Zan Dubi Rayuwa Ta Bangaren Tabbaci

"Iyalina ba su kasance tare da ni ba, kuma ba sa damuwa da abin da nake bukata".....

"Na fara kin makarantarmu, ba na son in ci gaba da karatu a cikinta".....

"Yanayin makarantarmu ba ya burge ni, ina burin da ma a ce ba a makarantar nake ba".....

"Wannan aboki nawa ba ya sadaukar da kansa gare ni, ba ya kasancewa tare da ni a dukkan al'amurra".....

Wadannan suna daga cikin maganganun da muke ji daga matasa, samari da 'yanmata, a lokacin da suke tattauna abubuwan da suka shafi cikin gidajensu da kuma wajensu.....

Wadannan suna nuni da irin mahangarsu dangane da yadda rayuwarsu take.....

Matashi, kamar sauran mutane, yana dubi ga hakikanin al'amari ne daidai yadda yake dubin lamarin, to amma a wasu lokuta kurar damuwa da rashin tabbas takan rufe mahangar tasa.....

Don wasu matasan, tun farko sukan zabi karka-cacciyar mahanga, don haka sai su dinga ganin lamurra ba su yi daidai da mahangarsu ba.....ko kuma su dinga ganin makusantansu suna so ne su cutar da su. To a sabili da haka ne irin wadannan samari suke ganin duniya ba kamar yadda suke so su ganta ba.....

Babu wanda yake bugun kirgin cewa dukkan abubuwan da suke kewaye da mu suna da kyau ko kuma sun cancanci yabo, to amma kuma tabbaceccen abu ne cewa ba dukkansu ne abubuwan kyama ba. Face dai akwai abubuwa masu yawan gaske da suke amfanarwa kana kuma suke tabbatar da alheri da sa'ada ga mutum.....abin da yake da muhimmanci shi ne dubinmu ga wadannan al'amurra ko kuma rayuwa a yanayi na gaba daya.....

Shin a matsayina na matashi, zan dubi rayuwa a matsayin mabubbugar alheri ne ko kuma mabubbugar tabewa da sharri.....shin zan ji dadin rayuwa ne, ko kuma zan ji zafi da dacinta ne.....shin ina cikin kwanciyar hankali da nitsuwa ne, ko kuma zan kasance cikin tashin hankali da rashin tabbas ne.....?

Amsar wadannan tambayoyi suna bambanta daga mutum zuwa mutum......mai yiyuwa ne wasu matasa su ce mu muna ganin rayuwa a matsayin cikakkiyar mabubbugar alheri da sa'ada, ko kuma mu ba abin da muke gani in ban da kyau sannan kuma ba ma jin kome in ban da jin dadin da ba mu san yanayinsa ba, mu muna rayuwa ne cikin kwanciyar hankali da nitsuwa.

Sai dai kuma hakikanin lamarin shi ne cewa akwai alheri da sharri cikin abubuwan da suke kewaye da mu, kamar yadda akwai masu amfani da cutarwa, sannan kuma akwai jin dadi da kuma wahala a tattare da su. Haihuwa cikin iyali abu ne mai faranta rai, sannan kuma mutuwar wani babba daga cikin manya abu ne mai zafi da ciwo..... lafiya abu ne mai kyau da kuma amfani, sannan kuma rashin lafiya abin bakin ciki ne. Mai yiyuwa ne abokinmu ya kasance mai sadaukarwa gare mu ko kuma ya watsar da mu lokacin da muke bukatarsa. Sannan mai yiyuwa ne in ci karo da mugun malami ko kuma mai rauni ko kuma sabanin haka.....kana kuma mai yiyuwa ne daya daga cikin mahaifa ya kasance mai tsanani kana dayan kuwa mai tausayi da sassauci.....

Hakika a kowace rana muna ganin irin wadannan abubuwa a kewayenmu, to amma hakan ba wai yana nufin ba mu da sa'a cikin rayuwa kenan ba a duk lokacin da muka ci karo da wani abin da ya sosa mana rai ko kuma ya cutar da mu; don kuwa ita rayuwa a hade take da alheri da kuma sharri. Abin da kawai yake sanya mu mu zamanto ma'abuta sa'a cikin rayuwa shi ne yadda muka fahimci rayuwa da kuma yadda muke kallonta.....

Don haka ya rage min a matsayina na matashi, ko dai in share kurar rashin tabbas daga jikin gilashin da nake gani da shi ko kuma in sake wannan gilashi don ya yi daidai da sabuwar mahangata.....

To amma abin tambaya anan shi ne cewa me wannan magana take nufi?!.....

Tana nufin wajibi ne mu samo sabuwar ka'ida ga mahangarmu......

1- A ko da yaushe mu dinga dubin bangaren kwanonmu da ke cike.....ban da bangaren da babu kome a cikinsa.

Wannan hikima za ta sanya mu dinga ganin alheri da kuma kyawun abubuwa ko kuma mutane, maimaikon sharri da muninsu.....ma'ana idan har ina so in zamanto mutumin kirki, to dole ne da farko kada in zamanto mutumin banza. Don haka ne ma wasu daga cikin wadanda suka fahimci rayuwa suke neman alherin mutum ban da sharrinsa.....

2- Mu yi imani cikin zuciyarmu cewa wannan duniya tana da Mai kula da ita, kuma ba Ya halitta sharri....... mai yiyuwa ne mu kasance cikin damuwa saboda makirci da kaidin Shaidan, to amma mu kan sami kwanciyar hankali da farin ciki a duk lokacin da muka yi galaba a kansa da kuma samun matsayi mai girma a wajen Ubangiji Mahalicci.

3- A ko da yaushe mu dinga neman abubuwan da suke masu amfani a gare mu, da sannu za mu same su a hannayenmu, bayan kokari da kuma juriya..... don kuwa duk wanda ya nema zai samu.....wanda kuwa ya shuka wani abu to lalle zai girbe shi......

Misali mai yiyuwa ne abubuwan da muke tunaninsu wadanda ba mu gansu ba, su kasance masu amfanarwa gare mu a fili ko a boye.....mai yiyuwa ne mu yi amfani da wasu abubuwa masu sauki wajen kirkiro abubuwa masu amfani gare mu, ko mu yi amfani da lokacin da muke lalatawa wajen koyon wani abu mai muhimmanci ko kuma wata sana'a mai amfani. Sannan mai yiyuwa ne mu saurari maganar karamin yaro ko kuma mutumin da ba kome ba, amma mu samu amfanin da zai taimaka mana duk tsawon rayuwarmu.

An hakaito cewa wani makeri ya kasance ya kan tara guntattakin ma'adinan da ake zubarwa a juji, bayan da suka taru sai ya dauka ya kai masana'anta don a narka masa su da kuma mayar da su sisin ma'adini, inda daga baya ya sayar da kudi mai yawa. Ta haka ne ya samu kudade masu yawa don kula da rayuwarsa da ta iyalinsa......to ka ga wannan yana nuna mana cewa mai yiyuwa ne wani abin da ake ganinsa a matsayin yashasshen abu ya amfane mu matukar muka gyara shi.

4- Mu kudurta cewa kai da kwakwalanmu ajiya ce da ba za a iya kirgata ba.....abin da kawai ya hau kanmu shi ne gano ta da kuma fitar da ita zuwa duniya ta hakika.....

Idan har ba mu yi imani da wannan lamari ba, to mu karanta tarihin Annabawa, waliyai, masana, ma'abuta tunani da manyan ma'abuta gyara wadan-da ba su mallaki kome na duniya ba in ban da ma'ajiya ta ilimi da masaniya. Sun sami hakan ne kuwa ta hanya fitar da su daga kwakwalansu, ta yadda suka sami damar gyara da kuma kirkiro abubuwa da dama a wannan duniya tamu, kuma ambatonsu ya kasance cikin tarihi har abada.

5- Mu kasance masu tunanin gina al'umma, ba masu ruguzawa ba.....

Idan har dukkanmu muka fara tunanin gina al'umma, hakan yana nufin kenan a ko da yaushe za mu dinga gudanar da wasu ayyuka kana daga baya kuma mu sake gudanar da wani aikin wanda zai cika wanda muka fara, sannan mu sake ci gaba daga inda muka tsaya, da haka sai mu ga mun kai ga manufa, babu makawa kuma za mu sami kwanciyar hankali da annashuwa.

Hakika wannan wata dabi'a ce da Allah Ya sanya ta ga dukkan 'yan'Adam, don shi mutum yana son ya ga ya kirkiro abubuwan amfani ga kansa da kuma sauran al'umma, ta yadda rayuwarsa za ta kasance ma'abuciyar kima da daukaka.....

Amma tunanin ruguza al'amurra, yana nufin ruguza ayyukan da muka riga muka gina ko kuma wadanda wasunmu suka gina; don nuna gaba ko kuma yi musu hassada. Ya dan'uwana! Ta yaya za a yi alheri ya isa ga irin wannan mutum?.

6. Mu so kawukanmu ba tare da ji-ji da kai ko girman kai ba.....

Kuma mu so sauran mutane ba tare da bibiye-bibiye ko wulakanci ba.....

Kaunarmu ga kawukanmu yana nufin muna kaunar alheri gareta ne, don haka ne ba za mu kai ta zuwa ga abin da zai cutar da ita ba. Sannan kuma za mu tanadar mata da abubuwan da za su amfane ta, da suka hada da ilimi, wayewa, kyawawan halaye, lafiya da dai sauran abubuwan da suka yi kama da haka.Kaunarmu ga sauran mutane kuwa shi ne mu yi musu fatan alheri, idan kuwa suka yi kuskure sai mu yafe musu, to amma idan suka ci gaba da hakan sai mu yi kokarin kare kanmu. Koda yake duk da haka bai kamata mu ki wani abu daga gare su ba face munanan ayyukansu; don kuwa soyayyar tana nan cikin zuciyarmu, to amma wannan so da kauna takan gushe idan muka kamu da cutar hassada da kiyayya.

7- Mu kasance masu kokari, don kuwa kokari shi ne tushen dukkan manyan ayyuka da kirkire-kirkire... ku yi kokari zuwa ga alheri ko kwa same shi.....

Muna yin kokari ne don kuwa rayuwa takan bai wa mutum dama mai girman gaske na aiki da samun nasara, kuma Allah Madaukakin Sarki Ya arzurta mu da ni'imomi masu yawa da ba za su iya kirguwa ba. Shi ne Yake ja-gorantarmu zuwa ga alheri da nasara.

Sannan kuma muna kokari don da yawa daga cikin mutane sun fuskanci rashin nasara, to amma suka ci gaba da kokari har sai da suka cimma burinsu da kuma samun nasara.

8- A hankali ake canja abin da ya lalace komai lalacewarsa kuwa.....

Shakka babu, duk da bushewa da kuma taurin da sahara take da shi, to amma digon ruwan sama yakan iya jika ta da kuma huda ta, daga baya kuma ya mai da hujin babban rami, to haka rayuwa take.....masu iya magana su kan ce wai mai hakuri yakan dafa dutse.....

Mu dauki kwayar hatsi, misali, idan muka sanya ta cikin kasa wacce take rayayyiya kana muka bi ta da ruwa, bayan wani lokaci takan iya zama bishiya. Masu iya magana suna cewa: "Sannu ba ta hana zuwa"......

Wani abin kuma shi ne cewa mu a matsayinmu na 'yan'Adam mukan iya tafiya tare da zamani komai wahalar da ke cikinsa kuwa.....mutum yakan iya rayuwa a wuraren da ruwa ke daskarewa saboda tsananin sanyi, kamar yadda kuma yake iya rayuwa a wuraren da suke da tsananin zafi.....ya kan iya rayuwa a kan duwatsu kamar yadda kuma yake iya rayuwa a cikin sahara mai kuna.....

To don haka me yasa muke nuna damuwa, tsoro da kuma fargaba.....

9- Akwai hikima cikin wahalhalu.....

Littafan tarihin magabata da manyan shuwaga-bannin da suka gabata cike suke da wahalhalun da wadannan gwarzaye suka fuskanta a rayuwarsu, da suka hada da mutuwar daya daga cikin makusan-tansu, rashin masoya, hasarar dukiya da kaddarori da dai sauran makamantan hakan.....sai dai kuma wadannan wahalhalu sun sanya su suka kasance mutanen da suka sami nasara wajen fuskantar matsalolin rayuwa, inda suka sami babban rabo a cikinta. Za mu ga sun kasance abin kauna da girmamawan mutane.

10- Ana iya gyara kurakurai da zunubai da kuma chanza su zuwa ayyuka na kwarai.....a lokuta da dama, mukan yi kure ne saboda karancin ilimi da kwarewa, ko kuma ba mu ba wa aikin da muka sa a gaban muhimmanci da kokarin da ya dace da shi ba ne.....lalle idan har muka yi amfani da kwarewa, sannan kuma muka tsara yukanmu kamar yadda ya dace, to da dama daga cikin kura-kuranmu za su ragu sosai.

Haka nan ma zunubai da laifuffukan da muke aikatawa, su ma dai mukan iya canza su, idan muka yi nadama kan ayyukan da muka aikata kana kuma muka biyo su da ayyukan kwarai.....

Ya zo cikin Alkur'ani mai girma cewa: ".....Lalle ne ayyukan kwarai suna kore munanan ayyuka". (Surar Hud, 11:114)

Ma'ana mu zo da kyawawan ayyuka don mu cike gurbin munanan ayyuka da kuma gusar da gurbinsu..... don yada alheri ita ce mafifiyar hanyar gusar da sharri a cikin zukatanmu.

11- Mu ne masu daukan nauyin kawukanmu da kuma ayyukanmu sama da wasunmu.....

Mai yiyuwa ne wasu su taimaka mana cikin wasu ayyuka, ko kuma su kasance tare da mu yayin wata musibar da ta same mu, to amma dai daga karshe mutum shi zai kasance abin tambaya kan ayyukansa kana kuma mai tsara wa kansa tafarkin da ya dace da shi, da kuma tabbatar da nasara cikin al'amurran rayuwarsa ta yau da kullum. Cikin karatu da kuma zaben abokin da ya dace, ko kuma samo girmamawan mutane, ko kuma samun fifiko cikin ayyukansa da dai sauransu.

Masu iya magana sukan ce: "Cire kayarka da hannayenka".

12- Mu san cewa nasara takan samu ta hanyar aiki da kuma juriya.....

Turawa sukan ce wai aiki yafi sautin magana daguwa......

Hakika kome zakin maganarmu ba wani amfanin da za ta yi matukar dai ba mu maisheta ta zamanto aiki ba.....shin fadin dalibi cewa lalle sai na yi nasara a jarrabawata, ya wadatar ya sanya shi samun nasarar, ko kuma karatu da kokari su ne suke sanya shi cimma wannan manufa.....

Lalle nasara ba ta samuwa don maganar fatar baki ko kuma kwadayin hakan, face dai ta kan samu ne ta hanyar aiki, kokari da kuma juriya.

13- Mu yarda da sakamakon ayyuka da kuma kokarinmu ko da kuwa wannan sakamako bai taka kara ya karya ba, don jiran wata damar da za ta zo, babu makawa irin wannan yanayi zai sanya mu cikin kwanciyar hankali a ko da yaushe. Mu dai mun riga mun yi namu kokarin, ko da kuwa ba mu sami wani abin a zo a gani ba, to mu ci gaba da bada kokari da kuma dogaro ga Ubangiji Madau-kakin Sarki har sai mun cimma burinmu da kuma samun nasara cikin ayyukan namu.....

Wadannan 'yan jumloli suna daga cikin ka'idojin da za su sanya tunani da mahangarmu, mu matasa, ta kasance mai kyau cikin rayuwa, kana kuma ma'abuciyar tafiya zuwa ga canji. Sannan kuma ta magance mana musifofin wannan tafiya ta rayuwa, abar tambaya, wacce muka fara ta bayan wuce matsayin yarinta.

Ya Ya Za Mu Amfani Ni'imomin Rayuwa?
Da yawa daga cikin matasa sukan tambayi kansu, me muka mallaka ne na daga dukiya ballan-tana ma mu dinga tunanin yadda za mu ingantata da kuma amfani da ita cikin rayuwarmu ta yau da kullum.....

Me yiyuwa ne wasu su ga kansu a matsayin marasa abin hannu saboda ba sa aikata abin da sauran manyan mutane suke aikatawa.....wannan tunani ne da ke cike da kuskure. Hakan shi ne yake sanya da yawa daga cikin matasa suke ganin rayuwa a matsayin wani duhu, musiba da kuma bala'i.....

Misali, wata matashiya 'yar shekara goma sha shida, yayin da take rubuta tarihin rayuwarta, ta rubuta cewa:

"Ba zan iya bayyana kome ba.....na wayi gari na kusan rasa duk abin da na sani, na kasance mai yawan tunani da fargaba, mara amincewa da kaina. Duk wani aikin da na fara yi sai in fara jin tsoron sakamakonsa, don haka sai in fara kokonton aikata shi, kullum cikin damuwa da bakin ciki nake. Duk lokacin da na dubi fuskata cikin madubi sai in ganta ba kyan gani, don haka sai na fara tsanan kaina, ina mai burin da ma ba a halicce ni ba".

Wani matashi kuma cewa ya yi:

"A duk lokacin da na dubi kaina cikin madubi, ga ni saurayi, sai in tambayi kaina.....shin wai wannan da nake ganinsa yana kama da ni, zai yiyu in so shi da a ce zai fito daga cikin wannan madubi da izinin Allah kana ya rayu da ni?......"

A wasu lokuta matashi yakan mai da alhakin abin da ya same shi ga iyalansa, musamman ma mahaifansa; don kuwa ba shi da wanda zai mai da wannan tuhuma gare shi in ban da su.

Sannan an hakaito cewa wata matashiya 'yar shekara sha biyar ta ziyarci wani likita ma'abucin littattafan kan yara da kuma matasa. Ko da ta shigo wurinsa tare da mahaifiyarta sai ta bukaci da ta tattauna da shi a kebance......

Ko da suka kebance, sai wannan matashiya ta fara sukan mahaifanta da zarginsu da cewa sun hana ta dama, suna takura mata......

To sai wannan hazikin likita ya tafi wurin mahaifiyar yarinyar don ya ji ra'ayinta dangane da wannan 'ya tata, to amma sai ya ji maganarta sabanin na 'yartata. Daga nan sai ya binciki lamarin kana kuma ya yi amfani da dimbin ilimin da yake da shi, sai ya gano cewa wannan yarinya tana tsoron rashin samun nasara ne da kuma rashin damuwa da sauran mutane suka yi da ita a matsayin cikakkiyar 'ya mace. Ta ki yarda ta mai da laifin ga kanta, don haka sai ta mayar da laifin ga mahaifanta daga lokacin da suka hana ta wani abin da take so.

Hakika muna bukatuwa da kulawan iyaye a yanayi na kebance kana da kuma kulawan manyan mutane a yanayi na gaba daya, sai dai mu ba yara ba ne da za mu dogara gaba daya a kansu.....

Iyali shi ne matakin farko na tafiya, kamar yadda matafiyi ya ke fara tafiyarsa, ko kuma kamar yadda mahayin dutse ya ke fara hawa jikin dutsen......

Sannan kuma iyali shi ne mafaka, wanda muke komawa gare shi a duk lokacin da muka bukaci hakan, musamman ma a mataki mafi tsanani na rayuwa don mu sami matsuguni da kwanciyar hankali......

Duk da irin wannan matsayi da muhimmanci da iyali suke da shi, to amma dole ne mu yi shiri a wannan marhala ta rayuwa, wato lokacin samar-taka, don mu dauki wasu nauye-nauye na rayuwa, don a hankali a hankali mu sami damar daukar dukkan nauyin kawukanmu, kai har ma da na iyalanmu gaba daya a nan gaba, ko kuma al'umman da muke rayuwa a cikinta.....

Yana da kyau tun da farko tun kafin mu sanya kafafunmu cikin wannan rayuwa ta duniya, mu tambayi ce wa; wani guzuri ne wannan rayuwa ta tanadar mana na daga dukiya, karfi da iyawa, don mu yi amfani da su a cikin wannan tafiya tamu ta rayuwa? Wani karfi da iko ne Allah Madaukakin Sarki Ya tanadar mana don mu sanya su zama mana uwar kudi ko kuma jari a wannan rayuwa, har mu ba da kokari wajen ci gabantar da su da kuma amfani da su a dukkan rayuwarmu? Don haka ya zama wajibi mu kirga irin abubuwan da muke da su mu gani.

1- Hankali

Wannan shi ne mafi girman dukiya da kuma ma'ajiyar da mu 'yan'Adam muka mallaka kana kuma da shi ne muka bambanta da sauran halit-tu.....kuma shi ne kwanon da yake dauke da ilimi, tunani, masaniyya da kuma kwarewa.....sannan kuma shi ne mai shiryar da mu zuwa ga tafarkin tsira da kuma alheri, wanda kuma yake bambance mana karya da gaskiya, sharri da kuma alheri.....kuma shi ne ke kula da dukkan takun da muka yi don kada mu kauce daga hanya madaidaiciya.....

To amma shin hankali yana iya zama dukiya kana guzuri ga mutumin da ya ki amfani da shi kana kuma ma bai san girma da kimarsa ba?

Masu iya magana sukan ce hankali shi ne matai-maki (waziri) mai yin nasiha; don kuwa shawarar waziri tana amfani ne a lokacin da sarki ya mai da shi mai ba shi shawarar.....to shin za mu sanya hankalinmu a matsayin wazirinmu?

2- Iko

Shi ne wanda a wasu lokuta ake kiransa da 'yancin zaben abin da mutum yake so..... dukkanmu muna da 'yancin yin wani aiki ko kuma barinsa. Iko a wajen mutum yakan sanya shi ya zamanto sama da dukkan halittu wajen aikata abin da yake so, ko kuma barin aikata wani abin da yake bukatuwa da shi, kamar barci, hutu, ci da sha, saboda wata manufa da take sama da wadannan abubuwa.....

Da dama daga cikin magabata sun rage lokutan barci da hutawansu don bincike da kuma karatu, ta yadda suka sami ilimi mai yawan gaske kana kuma suka sami matsayi a wajen al'umma, duk kuwa da cewa ba sa tare da su......

Haka nan ma muminai sukan nisanci ci da sha yayin da suke yin azumi don su bauta wa Ubangijinsu da kuma koyon hakuri da kuma daidaita kansu da marasa abin hannu. Idan har hakuri ya kasance al'ada a gare su, to babu makawa zai iya jure wa da yawa daga cikin wahalhalun rayuwa.

Babu shakka, iko, hakuri da juriya su ne hanyo-yin nasara ga dan'Adam cikin mafi yawan ayyukansa.

3- Tausayi

Sanannen abu ne cewa tausayi yafi kasantuwa a wajen matasa, musamman ma a wajen budurwaye don kuwa su ne iyayen gobe..... muna iya ganin yanayinsu na kuka da kuma irin alaka mai tsanani da ke tsakaninsu da kawayensu ko kuma malamansu.......

Hakika ana kirga tausayi a matsayin dukiyar dan'Adam, yakan yi mu'amala da abubuwan da suke kewaye da shi (tausayi), ya so wasu kana ya ki wasu, ya yarda da wasu kana kuma ya ki yarda da wasu, ya yi fatan samun wasu kana kuma ya wofantar da wasu.....

Tausayi shi yake hada mutum da sauran mutane 'yan'uwansa, kana kuma ya dada kara masa kauna da kusanci ga masoya da kuma iyalansa da kuma damuwa da abubuwan da suke damunsu.....

Tausayi da ji a jiki sukan girma a rayuwar matashi ta yadda zai wayi gari yana mu'amala da abubuwan da suke tare da shi cikin tausayi. Za ka gan shi yana komawa karanta wakoki da labarai, kuma yana kaunar zane-zane da abubuwa masu kyau, da kuma kokarin bayyana abubuwan da yake ji a jikinsa ta hanyar zane-zane ko kuma ta hanyar baitocin wake da dai sauran hanyoyi.....

Babu shakka tausayi da ji a jiki dukiyoyi masu muhimmanci ga mutum matukar dai ya san yadda zai yi amfani da su a rayuwarsa.

4- Riyawa

Hakan ba kamar yadda wasu suke tunanin cewa yakan kawar da matashi daga hakika, ko kuma ya sanya shi ya dinga iyo cikin wata duniya ta daban, ta yadda daga baya zai lalata iko da karfinsa. To amma riyawa (wato mutum ya riya wani abu a zuiyarsa) abu ne mai kyau da kuma amfani, don kuwa tana da gudummawa mai girman gaske a
rayuwar dan'Adam.....

Mai yiyuwa ne mutum ya gudu da abin da yake riyawa daga hakikanin al'amari mai daci, to amma a lokuta da dama mutum yakan koma ga riyawa da kuma jirinjiritsi, ta haka sai ya sami tsammanin faruwar alheri gare shi don kuwa yana so ya zamanto abin koyi ga saura. Kana kuma yana so ya zamanto mutum tsarkakakke marar aibi, don shi kamar yadda mai bincike ko matafiyin da yake tunanin inda zai je ko kuma abin da zai binciko tun ma kafin ya fara tafiyar ko kuma binciken yake ji, to haka shi ma yake ji......

Hakika wannan riyawa abu ne mai kyau ga wannan matafiyin ko kuma mai binciken don kuwa yana da alaka da duniyar hakika......

Riyawa dukiya ce ta hakika gare mu matukar dai mun sami damar hada ta da rayuwarmu ta hanyoyi daban-daban. Kada mu bar riyawa tayi galaba a kan hakikanin al'amurranmu ta yadda za mu ci gaba da zama cikin kogin fata da buri, haka nan kuma kada mu bari hakika ta galabci riyawa, don kada burace-burace da fatanmu su kasance a takure. Ya kamata mu bar wa riyawa gudummawarta ta fata da buri, sannan kuma mu yi riko da hakika wajen cimma wadannan burace-burace da kuma fata.

5- Lafiya...Kaddara Ce Da Ba 'a Kwatantata Da Dukiya...

Ya zo cikin hadisi cewa wajibi ne mu ribanci abubuwa biyar kafin faruwar wasu abubuwan biyar:
samartaka kafin tsufa, faraga kafin ayyuka su yi yawa, karfi kafin rauni, rashin lafiya kafin ciwo.....

Ya rage mana mu dakata mu dan yi tunani kan wannan dukiya da Allah Ya arzurtamu da ita.....yaya za mu yi idan muka rasa ta ba tare da mun shirya ba.....

Da dama daga cikin marasa lafiya sukan yi burin ina ma da suna da lafiya, don su ci gaba da ayyukansu na rayuwa.......

Hakika lafiya kaddara ce wacce dole ne mu kula da kuma kare ta ta hanyar ba ta abincin da ya dace, tsabta da kuma wasannin motsa jiki.....sannan kuma dole ne mu ba da muhimmanci ga daya bangaren kiwon lafiyan, shi ne kuwa tsabtace kawukanmu daga munanan ayyuka, keta, hassada, kiyayya da kuma canza su da kyawawan ayyuka, kamar yadda muke kula da tsabtar jikinmu.

Bayan samuwar wadannan kaddarorin, shin a matsayina na matashi zan ji cewa ni fakiri, marar abin hannu ne, musamman ma cewa wadannan ni'imomi ba wai sun kare a kan ni'imomin da na hadu da wanina a kansu ba ne, a'a akwai wadansu ni'imomin da suka kebanta da ni kawai. Don ko wane mutum akwai ni'imomin da ya kebantu da su shi kadai.....ba abin da ya rage masa face kawai ya yi amfani da kuma daukaka su kamar yadda dan kasuwa yake amfani da uwar kudinsa wajen nemo riba da hada su da uwar kudin nasa don ya ci gaba da jujjuya su.....
Bayan dukkan hakan, akwai wadansu ni'imomin da muna iya sanya su cikin rayuwarmu, kuma su haifar mana da canje-canje masu girman gaske cikin rayuwarmu sannan kuma su sanya mu mu zamanto masu iya kirkiro muhimman ayyuka da za su kai mu ga manufofi da kuma hadafofinmu na rayuwa. Wadannan ni'imomi kuwa suna nan a cikin rayuwarmu, musamman ma a shekarun samartaka, da za su iya tabbatar mana da wadansu abubuwan da ba za mu taba tunanin afkuwarsu ba.....daga cikinsu, akwai:

1- Kirkira: ita ce karfi, shiri da kuma iyawan da mutum yakan samu ta hanyar hankali, ilimin da kuma masaniyar da yake da shi......

Kirkira tana daga cikin sirrorin da suke haifar da daukaka a rayuwa, kuma takan sa ma'abucinta ya sami daman gano sabbin hanyoyin canza duniya da kuma tsira daga rashin ci gaba.....

Idan har muna son binciko irin wadannan iyawa a cikin rayuwarmu, dole ne mu sanya wadansu alamomi a gabanmu, mu bi hanyar kirkira tare da su. Wadannan alamomi kuwa su ne:

2- Imani: Karfi ne mai girman gaske wanda muke samunsa ta hanyar ingantacciyar akida da yarda da Mahaliccin duniya kana kuma Mai jujjuya ta, bugu da kari kan ganin girma da kamalarSa cikin dukkan halittu, manya da kananansu da kuma jin rahamarSa wacce ta mamaye dukkan kome. Sannan kuma ta hanyar bauta maSa, wacce take kawata mutum da karfin ruhi, mutum yakan zama mai karfi da juriya yayin wahalhalu.....

Imani ni'ima ce wacce matashi yakan same ta cikin sauki sama da waninsa saboda zuciyarsa a bude take wajen karbar yanayin rayuwa, shin wannan yanayi na madda (duniya) ne ko kuma na ma'anawiyya (na ruhi da lamurra lahira).

3- Madaukakiyar Himma: Wannan wata ni'ima ce da kuma karfi mai girman gaske da ke kai mutum zuwa ga manufarsa da kuma nesantar da shi daga fargaba da kuma yanke kauna.

An ruwaito wani hadisi yana cewa mutum yana tashi da himmarsa kamar yadda tsuntsu yake tashi da fuka-fukansa.....don haka mutum yana bukatuwa da himma madaukakiya a hanyarsa ta isa ga sa'ada da kuma ci gaba.....wannan hanya da take tabbatar masa da manufarsa ta rayuwa.....

Lalle babu makawa muna iya isa ga wannan babbar ni'ima idan muka yi riko da wasu ka'idoji a rayuwarmu, su ne kuwa:

  1. Mu dinga tuna cewa mu mutane ne kuma za mu iya kaiwa zuwa ga kamalar da muke so.
  2. Mu daure taragonmu zuwa ga tauraro (sama), kamar yadda masu iya magana su kan ce wai: himma bata ga rago.
  3. Kada mu shagaltar da kanmu da kananan al'amurra marasa muhimmanci.
  4. Mu kyautata alakarmu da sauran mutane, kada mu bari maslaharmu ta kewaye mu.
  5. Mu kasance masu kula da ka'ida hatta cikin zaben manufofi da hanyoyin da za mu isa gare su.
  6. Mu ba da muhimmanci ga kyawun badini kamar yadda muke kula da kyawun zahiri.
  7. Mu zabi abokai masu madaukakiyar himma.

Abubuwan da muka ambata a wannan fasali su ne mafi muhimmancin ni'ima da kyautar da muka mallaka mu matasa, ko kuma abubuwan da muke da damar samo su ta hanyar karfi da kuma shirin da muke da shi. Lalle ya kamata mu yi imani da cewa rayuwa da kuma Mahaliccinta Suna iya kara mana wadannan ni'imomi, matukar dai muka ci gaba da bincike da kuma bahasi, don kuwa ajiyoyin rayuwa ba sa da iyaka "....kuma idan kun kidaya ni'imar Allah ba za ku lissafe ta ba.....".

Ya Ya Za Mu Iya Guje Wa Sharrin Rayuwa?

Hakika dan'Adam ma'abucin manufa da sako ne, to amma abin tambaya a nan shi ne mene ne sakonsa a wannan duniya?

An halicci dan'Adam ne don neman alheri da kuma sa'ada a rayuwa, kana kuma ya guje wa sharrori da kuma abubuwan da za su kai shi zuwa ga halaka. Don haka cikin rayuwa akwai alheri da kuma sharri, dan'Adam shi ne mai zaba wa kansa abin da ya dace da shi na daga alheri da kuma nesantar abubuwan sharri wadanda ba su dace da shi ba.

Ya 'yan'uwa, idan da a ce wani mutumin da ba mu san shi ba zai ba mu abinci ko kuma halawa, shin za mu kama ci ko sha ne haka kawai daga ya ba mu, ko kuma za mu tsaya mu gani cewa wannan abinci ko kuma halawar suna da tsabta alal akalla?

Lalle mu mukan zabi tsabta cikin dukkan abin da za mu ci ko kuma za mu yi amfani da shi don kiyaye kanmu daga kwayoyin cutar da za su janyo mana cututtuka da kuma sanya lafiyarmu cikin hatsari. Don haka wajibi ne mu aikata haka ga munanan ayyukan da suke lalata mana dabi'u da kuma mutumci.

Sannan kuma a duk lokacin da mutum ya kamu da wata cuta yakan tafi wajen likita don neman maganin wannan cuta, sai dai kuma a wasu lokuta yakan kamu da cutar ruhi, to amma sai ya ki zuwa neman magani; don kuwa ba ya ganinta a fili, amma kuwa tana iya lalata masa al'amurra daga karshe.

Dukkanmu, baya ga jiki, muna da ruhi da kuma hankali, don haka mafi munin sharrin rayuwa shi ne abin da yake damun ruhinmu da kuma lalata mana tsare-tsarenmu mu na kyawawan halaye.

Wadannan tsare-tsare na kyawawan halaye su ne suke nuni da daukakar dan'Adam da kuma ruhinsa, don haka idan dan'Adam ya rasa wadannan tsare-tsare, to babu abin da ya saura masa in ban da kawai abubuwa marasa amfani a rayuwarsa kuma zai yi rayuwa ce irin ta dabbobi da tsirrai.

Siffofin daukaka da alheri sukan arzurta mutum da abubuwan da za su taimaka masa da kuma sanya shi ya zamanto mabubbugar alheri ga kansa da kuma sauran mutanen da yake tare da su.

Baya ga haka kuma, akwai wata hakikar, ita ce kuwa cewa, mutum a wannan rayuwa yana nan ne tsakanin tuddan alheri da kuma na sharri.....don haka duk lokacin da ya kusanci tudun alheri, da hakan ne kuma zai nesanci tudun sharri.....

Idan waninmu yana da wani aboki da yake sadaukar da kansa dominsa a duk lokacin da yake fuskantar wata matsala, to a hakikanin gaskiya babu yadda za a yi ya cuce shi ko kuma ha'ince shi.....don haka sakamakon hakan shi ne son abokanmu da kuma fahimtar abubuwan da suke kewaye da mu.

Haka nan kuma idan wani daga cikinmu ya kasance mai biyayya ga mahaifansa, hakan yana nuni da cewa kenan ba za mu saba musu ba, kuma babu makawa abin da za mu samu shi ne kauna da kuma girmamawarsu gare mu, ko kuma kaunar sauran mutane da kuma girmamawarsu gare mu. Sannan kuma sama da hakan shi ne kauna da kuma yardar Ubangiji Madaukakin Sarki gare mu.

Wadansu mutane suna kokarin nuna mana cewa ma'anar alheri shi ne nisantar dadin duniya da kuma kaurace musu. To amma a gaskiya ma'anar alheri shi ne kyautata mu'amala da ni'imomi da iyawan da aka arzurtamu da su. Shi ne kuwa amfani da wadannan abubuwan jin dadi ta hanyar da ta dace.

Don kuwa Wanda Ya arzurtamu da wadannan ni'imomi da kuma iyawa ba Ya so ya haramta mana dadinsu, face dai so Yake mu yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace da za su sanya mu a kan tafarkin alheri har abada.

Saboda haka sharri shi ne mu gagara amfani da wadannan ni'imomi ta hanyar da ta dace da kuma mance manufofin da suka sa aka arzurtamu da su. To amma tambayar da take da muhimmanci a nan ita ce, mene ne yake sanya mu a wasu lokuta mukan zabi sharri duk kuwa da irin bala'in da ke tattare da shi ko kuma muke ba shi damar ya shiga cikin rayuwarmu ta samartaka mai kyawun fuska?!

Amsa wannan tambaya tana bukatuwa da gabatar da wasu tambayoyin na daban.

Shin muna daga cikin mutanen da suke kaskantar da kansu da cin mutumcin kansu ne? idan kuwa har haka ne, to sharri zai mamaye mu.......

Babu wani daga cikinmu da zai yarda a ce masa wani shugaba daga cikin shuwagabannin kasashe ko kuma ja-gora daga cikin ja-gorori zai sunkuya kasa don daukan wani abu maras amfani.

Mai yiyuwa ne wannan abu yana da girma da muhimmanci ga wasu, to amma irin girman shugaba ko kuma ja-gora zai hana shi damuwa da wannan abu, kuma bai kamance shi yayi hakan ba. Hakan nan ma, bai dace da mu 'yan'Adam ba mu bar kawukanmu su zamanto wajajen gwajin munanan ayyuka, hassada, zalunci, karya, sata, da dai zunubai da sharrori.

Shin muna daga cikin masu wasa da abokan gaba?

To alal akalla kada mu yi haka da abokan gabanmu na daga kwayoyin cuta.....shin za mu yi haka da sauran nau'in kwayoyin cuta, wato kwayoyin cutar munanan ayyuka?.

Akwai wata kissa ta sahabban Annabi (s.a.w.a.) lokacin da suke tare da shi a wani bushasshen guri kuma ga shi ana tsananin sanyi. Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya tambaye su ko za su iya tattaro itatuwa don su kunna wuta da kuma jin dumi?

Sai dukkan sahabban suka ce: babu tsiro ko bishiya a wannan wuri ya ya za su iya hado itatuwa?

Sai Annabi (s.a.w.a.) ya ce musu: to kowannen-ku ya tafi ya nemo abin da ya sawwaka.

Sai sahabbai suka bazama don nemo duk wani abin da suka gani na daga kayoyi da busassun tsirrai, daga nan sai suka zo wajen Manzon Allah (s.a.w.a.) tare da itatuwa masu yawan gaske.

Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) yace musu, da haka ne kananan zunubai suke taruwa da yawa kamar yadda kuka tattaro wadannan itatuwa. Sannan kuma ya ce musu: ina gargadinku da kananan zunubai.

Shin muna daga cikin wadanda ba sa gani face abubuwan da suke gaban kafufunsu, kuma ba sa ganin abubuwan da za su faru nan gaba sannan kuma suke jahiltar karshen al'amurra?

Da wuya ace dokin da ke daure a jikin injin tatsan rake don jujjuya shi, kamar yadda ake yi a da ko kuma a halin yanzu a wasu wurare, zai nuna bacin rai kan wannan aiki ga shi kuwa yana tafiyar dubban mila-milai ba tare da ya bar inda yake ba.....

Mai yiyuwa ne hakan ya faru saboda shi abin da ke gaban kafafuwansa kawai yake gani, to amma wanda yake ganinsa daga nesa da kuma wajen injin zai tausaya masa halin da yake ciki.....

Shin muna daga cikin wadanda suke ba da muhimmanci ga harkokinsu ne kawai?
Idan har al'amarin haka ne, to mun kasance kamar kwadon da ke cikin rijiya kuma ba ya so ya bar cikinta, amma yana ganin duniya kawai ita ce abin da ke kewaye da wannan rijiya, bai san abin da ke wajen wannan rijiya ba da suka hada gonaki da sauran ruwayen da suke gudu a wajen rijiyar.

Shin muna daga cikin mutanen da suke fara tafiya ba tare da sun duba kawukansu ba?

Hakan shi ne yanayin matafiyin da ya zabi batacciyar hanya ba tare da kula da alamomin da suke gefen hanyar ba, sannan kuma bai tambayi kowa ba...to matukar dai wannan matafiyi ya ci gaba a irin wannan yanayi, to babu yadda za a yi ya kai ga inda yake son zuwa ko da kuwa ya kara saurin tafiyarsa don saboda karin nisan inda zai je din.

Shin muna daga cikin mutanen da suke barin aikata ayyukan alheri har zuwa wani lokaci?

Alal misali, mu ce akwai isasshen lokaci a nan gaba da za mu aikata alheri.....ko kuma mu ce mu har yanzu yara ne da ba mu da wani nauyi a kanmu, da dai makamantan irin wadannan maganganu da kuma tunani.....

Hakan kuwa yana nufin kenan muna son mu bar kofofin sharri a bude ba tare da mun bude na alheri ba.....bayan dan wani lokaci sai mu ga ma'ajiyar zuciyarmu ta cika da sharri; don kuwa mun riga mun rufe kofofin alheri ba tare da mun ba shi daman cika zukatanmu da kuma kawata rayuwarmu ba.

Shin muna abota da ashararai ma'abuta munanan ayyuka ne?

Shin a shirye muke mu kulla alaka da irin wadannan mutane?

Idan haka ne kuwa, to za mu karfafa hannayen sharri a tattare da mu kenan ta yadda a sannu-sannu za mu fada cikin rijiyar bala'insa; don kuwa kusanta hannun sharri da kuma misaltuwa da shi yana nesanta mu daga hannayen alheri ne.

Shin za mu yi amfani kwakwalwarmu da kuma ci gaba da shirye-shiryenmu na kyawawan dabi'u?

Idan har muka bari kwayoyin cutar sharri suka shiga cikin wadannan shirye-shirye namu, shin muna neman wata hanya mafi saurin da za mu fitar da su? Kamar yadda muke yi ga kwamfutocinmu da suke cikin gidaje, ko kuma kamar yadda muke yi a makarantu da kuma wuraren ayyukanmu.....

Akwai tambayoyi da yawan gaske da muke tam-baya don sanin hanyoyin da sharri yake bi wajen shiga rayuwarmu. Misali, muna iya tambaya, shin muna daga cikin mutanen da suke damuwa da adon zahiri da kuma adon tufafi da dai sauransu? Ko kuma muna damuwa da kawan badini da kuma kyawawan dabi'u?

Kana kuma, shin muna iya bambance alheri da sharri?

Mai yiyuwa ne sharri ba zai bayyana mana a matsayi mai muni ba, face dai zai zo mana ne da yanayi mai kyau yana hade da guba da kuma zuma.....

Don haka mu kula da sharri dukkan kula musam-man ma idan ya sanya tufafin alheri.

Hakika mafi kyawun tafarkin gano sharri ko kuma hakikanin ayyukan da ake kiransu da sharri da munanan ayyuka ko kuma zunubai shi ne mu yi dubi cikin karshe da kuma sakamakonsu.

To daga cikin sakamako da kuma karshen wadannan ayyuka akwai, tabewa, shaye-shaye, aikata muggan laifuffuka, shiga gidan yari da dai sauransu.....

Daga karshe muna iya cewa alheri shi ne yada kyawawan siffofi cikin rayuwarmu da kuma rayuwar wadanda suke kewaye da mu.....hakan kuwa yana nufin amfani da kuma jin dadin ni'imomin rayuwa da kuma kyawunta tare da kwanciyar hankali, daidaituwa da kuma sa'ada.

Sannan kuma ba makawa sharri ba zai samar mana da hakan ba, face dai zai bayyana cewa zai samar mana da hakan ne, amma karya ce kawai.

Shin rayuwar son kai ba tare da kula da sauran mutane ba yana daga cikin alheri? Shin yana daga cikin alheri mutum ya dinga wasa da abinci alhali kuwa miliyoyin yara suna mutuwa da yunwa?

Irin wadannan tambayoyi sukan samu yin tunani don zaban rayuwar da za mu yi don kada mu fada cikin sharrin da wasunmu suka fada. Sannan kuma mu yi amfani da damar rayuwa wajen tafarkin kiyaye mutum da al'ummarsa daga hatsarori da kuma matsalolin rayuwa.

Daga Karshe....

Ba abin da za mu ce a karshen wannan dan karamin littafi, "Shingen Matasa", face dai muna kira ga masu karatu, membobin "Dandalin Matasa", samari da 'yan mata da su rubuta mana ra'ayoyinsu kan wannan littafi da kuma abin da ya kumsa.....

Muna maraba da duk wanda yake ko take son ya/ta aiko da ra'ayinsa/ta a wannan dandali, kana kuma muna maraba da duk wanda yake ko kuma take son taimakawa da ra'ayinsa/ta wanda zai taimaki matasa..

Hakika duk wani taimako daga gare ku zai kasance abin alfahari gare mu.

Gabatarwa

Wannan dan karamin littafi, "Dandalin Matasa" ne ya tsara shi don ya kasance a gefen samari da 'yan mata (matasa) a wannan lokaci mai muhimmanci na rayuwarsu, don ya taimaka musu wajen fahimtar hakikanin wannan lokaci na rayuwa da kuma abubuwan da suka kewaye shi.....

Wannan lokaci da muke magana a kansa kuwa shi ne lokacin da mutum ya kawo shekarun balaga. Wannan lokaci kuwa shi ne wanda ko wane mutum yake bukatuwa da shi don gina kansa da kuma tabbatar da dukkan abin da yake son cimmawa a rayuwarsa.

"Dandalin Matasa" yana dubin wannan lokaci na samartaka ne a matsayin nauyi da kuma amana, kuma ya yi imani da cewa dukkan abin da matashi ko matashiya suka mallaka a wannan lokaci na daga tunani, tausayi, ji-a-jika, karfi, kai da ma dukkan wata ni'ima, taskoki ne da Allah Madaukakin Sarki Ya ba wa dan'Adam don ya yi amfani da su a tafarkin alheri da sa'ada, ban da tafarkin lalacewa da bata.

Don haka wannan littafi "Shingen Matasa", wani kokari ne na daban daga "Dandalin Matasa" a kan maudu'in matasa da kuma abubuwan da suka shafe

su...muna fatan wannan littafin zai kasance mai amfani ga matasa, wadanda su membobi ne na wannan dandali a duk inda suke.

MU'ASSASAR AL-BALAGH

Sabbin Canje-Canje

Dukkanmu mun shaidi lokacin bazara, kana kuma mun rayu a cikin yanayinta mai kyaun gaske da kuma kwantar da hankali.....kowane abu a lokacin baraza yakan fara ne daga farko.....furanni sukan budu a kan bishiyoyi su cika ko'ina da kamshin da ke jikinsu..... gonaki kuma su cika da korayen ganyaye.....tsuntsaye kuwa su cika sama suna shawagi cikin farin ciki da annashuwa saboda irin wannan yanani mai dadi..... kwari su ma haka suna ta rawa da yawo tsakanin furran bishiyoyi ..... haka nan sama ma za ta yi kyau.....

Wannan yanayin bazara kenan, motsi, ci gaba da kuma haihuwa.....

Haka Allah Madaukakin Sarki Ya so rayuwar dan'Adam ta kasance kamar fasalin shekara, ya kan fara daga lokacin bazara ya kare a lokacin girbi. Bazarar rayuwar mutum takan fara ne daga lokacin haihuwarsa har zuwa lokacin samartakansa..... wannan lokaci na balaga ko kuma abin da ake ce ma shekarun samartaka suna a matsayin lokacin shuka ne na rayuwa......

A wannan lokaci ne kowane mutum yakan gano sabuwar duniyarsa kamar yadda matafiya suke gano sabuwar kasa, inda zai tafiyar da sauran abin

da ya rage na rayuwarsa a gurin......

Misali, tsuntsu, a lokacin da yake karami, bai san komai ba face 'yar shekar da mahaifiyarsa ta shirya masa, yana ci daga abin da mahaifiyar tasa ta kawo masa. Amma idan ya fara girma, fukafukansa suka fara yin karfi, sai ya fara koyon tashi sama yana yawo kan bishiyoyi da koguna, yana mai zaba wa kansa abin da yake so na daga hatsi da 'ya'yan itatuwa.

Kamar yadda kuma tsutsar tsamiya a farkon rayuwarta take samun abincinta a jikin ganyen bishiya; ta yafato ganye daga wannan reshen bishiyar ta yafato daga wancan, kana sai ta rufe kanta cikin dakinta. Bayan wani lokaci kuma sai ta fito da abin da yake daukan ido saboda kyaunsa, to haka rayuwa take ga saurayi ko budurwa a wannan lokaci na rayuwarsu.......

Sannan kuma tsiro yakan fito daga cikin kasa don ya girma a kan kasa, inda daga baya yakan girma ya yi ressa har ya zamanto babbar bishiya mai rassuna da kuma 'ya'ya masu zaki.....

To mu ma muna ganin irin wannan haihuwa da girman jikkunanmu, misali, hakora su kan fasa dasorin jariri don ya sami damar tauna abinci mai tauri, sannan daga baya kuma hakora dawwamam-mu su fito bayan wasu shekaru don su maye gurbin wadancan na farkon.....

Lalle babu makawa abubuwan da suke faruwa garemu na daga canje-canjen samartaka shi ya fi muhimmanci a kan fitowan wadannan kwari ko kuma fitowan wadannan hakora ga jariri.....don haka dole ne mu ba da muhimmancin gaske ga wadannan sabbin canje-canje da suke faruwa a wannan lokaci na rayuwa, don mu kyautata mu'amalarmu kana kuma mu ribanci rayuwarmu kafin mu kai shekarun tsufa.....

Hakika wannan canji yana bukatuwa da fahimta, hakuri, juriya da kuma jin nauyi abin da ke kanmu.

Don kuwa ingantacciyar fahimta ita ce take hada mu da rayuwa kai tsaye, sannan kuma ta nuna mana asalin ni'imomi na hakika......

Shi kuwa jin nauyi yakan ingiza mu zuwa ga abubuwan da muke bukata a wannan rayuwa, ta yadda komai zai kasance mai amfani a gare mu.....

Hakuri da juriya kuwa muna bukatansu don tafiya a kan tafarkin da zai kai mu zuwa ga kofofin shiriya da daukaka......

Lalle duk wani matashin da ya yi kyakkyawan shiri wa rayuwa, zai sami jin dadi da kuma sa'ada a rayuwarsa.....don kuwa kofofin rayuwa a bube suke musamman ma ga wanda yake wannan mataki.

Yadda Za Mu Fahimci Lamurra....
Yadda Zan Dubi Rayuwa Ta Bangaren Tabbaci

"Iyalina ba su kasance tare da ni ba, kuma ba sa damuwa da abin da nake bukata".....

"Na fara kin makarantarmu, ba na son in ci gaba da karatu a cikinta".....

"Yanayin makarantarmu ba ya burge ni, ina burin da ma a ce ba a makarantar nake ba".....

"Wannan aboki nawa ba ya sadaukar da kansa gare ni, ba ya kasancewa tare da ni a dukkan al'amurra".....

Wadannan suna daga cikin maganganun da muke ji daga matasa, samari da 'yanmata, a lokacin da suke tattauna abubuwan da suka shafi cikin gidajensu da kuma wajensu.....

Wadannan suna nuni da irin mahangarsu dangane da yadda rayuwarsu take.....

Matashi, kamar sauran mutane, yana dubi ga hakikanin al'amari ne daidai yadda yake dubin lamarin, to amma a wasu lokuta kurar damuwa da rashin tabbas takan rufe mahangar tasa.....

Don wasu matasan, tun farko sukan zabi karka-cacciyar mahanga, don haka sai su dinga ganin lamurra ba su yi daidai da mahangarsu ba.....ko kuma su dinga ganin makusantansu suna so ne su cutar da su. To a sabili da haka ne irin wadannan samari suke ganin duniya ba kamar yadda suke so su ganta ba.....

Babu wanda yake bugun kirgin cewa dukkan abubuwan da suke kewaye da mu suna da kyau ko kuma sun cancanci yabo, to amma kuma tabbaceccen abu ne cewa ba dukkansu ne abubuwan kyama ba. Face dai akwai abubuwa masu yawan gaske da suke amfanarwa kana kuma suke tabbatar da alheri da sa'ada ga mutum.....abin da yake da muhimmanci shi ne dubinmu ga wadannan al'amurra ko kuma rayuwa a yanayi na gaba daya.....

Shin a matsayina na matashi, zan dubi rayuwa a matsayin mabubbugar alheri ne ko kuma mabubbugar tabewa da sharri.....shin zan ji dadin rayuwa ne, ko kuma zan ji zafi da dacinta ne.....shin ina cikin kwanciyar hankali da nitsuwa ne, ko kuma zan kasance cikin tashin hankali da rashin tabbas ne.....?

Amsar wadannan tambayoyi suna bambanta daga mutum zuwa mutum......mai yiyuwa ne wasu matasa su ce mu muna ganin rayuwa a matsayin cikakkiyar mabubbugar alheri da sa'ada, ko kuma mu ba abin da muke gani in ban da kyau sannan kuma ba ma jin kome in ban da jin dadin da ba mu san yanayinsa ba, mu muna rayuwa ne cikin kwanciyar hankali da nitsuwa.

Sai dai kuma hakikanin lamarin shi ne cewa akwai alheri da sharri cikin abubuwan da suke kewaye da mu, kamar yadda akwai masu amfani da cutarwa, sannan kuma akwai jin dadi da kuma wahala a tattare da su. Haihuwa cikin iyali abu ne mai faranta rai, sannan kuma mutuwar wani babba daga cikin manya abu ne mai zafi da ciwo..... lafiya abu ne mai kyau da kuma amfani, sannan kuma rashin lafiya abin bakin ciki ne. Mai yiyuwa ne abokinmu ya kasance mai sadaukarwa gare mu ko kuma ya watsar da mu lokacin da muke bukatarsa. Sannan mai yiyuwa ne in ci karo da mugun malami ko kuma mai rauni ko kuma sabanin haka.....kana kuma mai yiyuwa ne daya daga cikin mahaifa ya kasance mai tsanani kana dayan kuwa mai tausayi da sassauci.....

Hakika a kowace rana muna ganin irin wadannan abubuwa a kewayenmu, to amma hakan ba wai yana nufin ba mu da sa'a cikin rayuwa kenan ba a duk lokacin da muka ci karo da wani abin da ya sosa mana rai ko kuma ya cutar da mu; don kuwa ita rayuwa a hade take da alheri da kuma sharri. Abin da kawai yake sanya mu mu zamanto ma'abuta sa'a cikin rayuwa shi ne yadda muka fahimci rayuwa da kuma yadda muke kallonta.....

Don haka ya rage min a matsayina na matashi, ko dai in share kurar rashin tabbas daga jikin gilashin da nake gani da shi ko kuma in sake wannan gilashi don ya yi daidai da sabuwar mahangata.....

To amma abin tambaya anan shi ne cewa me wannan magana take nufi?!.....

Tana nufin wajibi ne mu samo sabuwar ka'ida ga mahangarmu......

1- A ko da yaushe mu dinga dubin bangaren kwanonmu da ke cike.....ban da bangaren da babu kome a cikinsa.

Wannan hikima za ta sanya mu dinga ganin alheri da kuma kyawun abubuwa ko kuma mutane, maimaikon sharri da muninsu.....ma'ana idan har ina so in zamanto mutumin kirki, to dole ne da farko kada in zamanto mutumin banza. Don haka ne ma wasu daga cikin wadanda suka fahimci rayuwa suke neman alherin mutum ban da sharrinsa.....

2- Mu yi imani cikin zuciyarmu cewa wannan duniya tana da Mai kula da ita, kuma ba Ya halitta sharri....... mai yiyuwa ne mu kasance cikin damuwa saboda makirci da kaidin Shaidan, to amma mu kan sami kwanciyar hankali da farin ciki a duk lokacin da muka yi galaba a kansa da kuma samun matsayi mai girma a wajen Ubangiji Mahalicci.

3- A ko da yaushe mu dinga neman abubuwan da suke masu amfani a gare mu, da sannu za mu same su a hannayenmu, bayan kokari da kuma juriya..... don kuwa duk wanda ya nema zai samu.....wanda kuwa ya shuka wani abu to lalle zai girbe shi......

Misali mai yiyuwa ne abubuwan da muke tunaninsu wadanda ba mu gansu ba, su kasance masu amfanarwa gare mu a fili ko a boye.....mai yiyuwa ne mu yi amfani da wasu abubuwa masu

sauki wajen kirkiro abubuwa masu amfani gare mu, ko mu yi amfani da lokacin da muke lalatawa wajen koyon wani abu mai muhimmanci ko kuma wata sana'a mai amfani. Sannan mai yiyuwa ne mu saurari maganar karamin yaro ko kuma mutumin da ba kome ba, amma mu samu amfanin da zai taimaka mana duk tsawon rayuwarmu.

An hakaito cewa wani makeri ya kasance ya kan tara guntattakin ma'adinan da ake zubarwa a juji, bayan da suka taru sai ya dauka ya kai masana'anta don a narka masa su da kuma mayar da su sisin ma'adini, inda daga baya ya sayar da kudi mai yawa. Ta haka ne ya samu kudade masu yawa don kula da rayuwarsa da ta iyalinsa......to ka ga wannan yana nuna mana cewa mai yiyuwa ne wani abin da ake ganinsa a matsayin yashasshen abu ya amfane mu matukar muka gyara shi.

4- Mu kudurta cewa kai da kwakwalanmu ajiya ce da ba za a iya kirgata ba.....abin da kawai ya hau kanmu shi ne gano ta da kuma fitar da ita zuwa duniya ta hakika.....

Idan har ba mu yi imani da wannan lamari ba, to mu karanta tarihin Annabawa, waliyai, masana, ma'abuta tunani da manyan ma'abuta gyara wadan-da ba su mallaki kome na duniya ba in ban da ma'ajiya ta ilimi da masaniya. Sun sami hakan ne kuwa ta hanya fitar da su daga kwakwalansu, ta yadda suka sami damar gyara da kuma kirkiro abubuwa da dama a wannan duniya tamu, kuma

ambatonsu ya kasance cikin tarihi har abada.

5- Mu kasance masu tunanin gina al'umma, ba masu ruguzawa ba.....

Idan har dukkanmu muka fara tunanin gina al'umma, hakan yana nufin kenan a ko da yaushe za mu dinga gudanar da wasu ayyuka kana daga baya kuma mu sake gudanar da wani aikin wanda zai cika wanda muka fara, sannan mu sake ci gaba daga inda muka tsaya, da haka sai mu ga mun kai ga manufa, babu makawa kuma za mu sami kwanciyar hankali da annashuwa.

Hakika wannan wata dabi'a ce da Allah Ya sanya ta ga dukkan 'yan'Adam, don shi mutum yana son ya ga ya kirkiro abubuwan amfani ga kansa da kuma sauran al'umma, ta yadda rayuwarsa za ta kasance ma'abuciyar kima da daukaka.....

Amma tunanin ruguza al'amurra, yana nufin ruguza ayyukan da muka riga muka gina ko kuma wadanda wasunmu suka gina; don nuna gaba ko kuma yi musu hassada. Ya dan'uwana! Ta yaya za a yi alheri ya isa ga irin wannan mutum?.

6. Mu so kawukanmu ba tare da ji-ji da kai ko girman kai ba.....

Kuma mu so sauran mutane ba tare da bibiye-bibiye ko wulakanci ba.....

Kaunarmu ga kawukanmu yana nufin muna kaunar alheri gareta ne, don haka ne ba za mu kai ta zuwa ga abin da zai cutar da ita ba. Sannan kuma za mu tanadar mata da abubuwan da za su amfane ta,

da suka hada da ilimi, wayewa, kyawawan halaye, lafiya da dai sauran abubuwan da suka yi kama da haka.

Kaunarmu ga sauran mutane kuwa shi ne mu yi musu fatan alheri, idan kuwa suka yi kuskure sai mu yafe musu, to amma idan suka ci gaba da hakan sai mu yi kokarin kare kanmu. Koda yake duk da haka bai kamata mu ki wani abu daga gare su ba face munanan ayyukansu; don kuwa soyayyar tana nan cikin zuciyarmu, to amma wannan so da kauna takan gushe idan muka kamu da cutar hassada da kiyayya.

7- Mu kasance masu kokari, don kuwa kokari shi ne tushen dukkan manyan ayyuka da kirkire-kirkire... ku yi kokari zuwa ga alheri ko kwa same shi.....

Muna yin kokari ne don kuwa rayuwa takan bai wa mutum dama mai girman gaske na aiki da samun nasara, kuma Allah Madaukakin Sarki Ya arzurta mu da ni'imomi masu yawa da ba za su iya kirguwa ba. Shi ne Yake ja-gorantarmu zuwa ga alheri da nasara.

Sannan kuma muna kokari don da yawa daga cikin mutane sun fuskanci rashin nasara, to amma suka ci gaba da kokari har sai da suka cimma burinsu da kuma samun nasara.

8- A hankali ake canja abin da ya lalace komai lalacewarsa kuwa.....

Shakka babu, duk da bushewa da kuma taurin da sahara take da shi, to amma digon ruwan sama yakan iya jika ta da kuma huda ta, daga baya kuma ya mai da hujin babban rami, to haka rayuwa

take.....masu iya magana su kan ce wai mai hakuri yakan dafa dutse.....

Mu dauki kwayar hatsi, misali, idan muka sanya ta cikin kasa wacce take rayayyiya kana muka bi ta da ruwa, bayan wani lokaci takan iya zama bishiya. Masu iya magana suna cewa: "Sannu ba ta hana zuwa"......

Wani abin kuma shi ne cewa mu a matsayinmu na 'yan'Adam mukan iya tafiya tare da zamani komai wahalar da ke cikinsa kuwa.....mutum yakan iya rayuwa a wuraren da ruwa ke daskarewa saboda tsananin sanyi, kamar yadda kuma yake iya rayuwa a wuraren da suke da tsananin zafi.....ya kan iya rayuwa a kan duwatsu kamar yadda kuma yake iya rayuwa a cikin sahara mai kuna.....

To don haka me yasa muke nuna damuwa, tsoro da kuma fargaba.....

9- Akwai hikima cikin wahalhalu.....

Littafan tarihin magabata da manyan shuwaga-bannin da suka gabata cike suke da wahalhalun da wadannan gwarzaye suka fuskanta a rayuwarsu, da suka hada da mutuwar daya daga cikin makusan-tansu, rashin masoya, hasarar dukiya da kaddarori da dai sauran makamantan hakan.....sai dai kuma wadannan wahalhalu sun sanya su suka kasance mutanen da suka sami nasara wajen fuskantar matsalolin rayuwa, inda suka sami babban rabo a cikinta. Za mu ga sun kasance abin kauna da girmamawan mutane.

10- Ana iya gyara kurakurai da zunubai da kuma chanza su zuwa ayyuka na kwarai.....a lokuta da dama, mukan yi kure ne saboda karancin ilimi da kwarewa, ko kuma ba mu ba wa aikin da muka sa a

gaban muhimmanci da kokarin da ya dace da shi ba ne.....lalle idan har muka yi amfani da kwarewa, sannan kuma muka tsara ayyukanmu kamar yadda ya dace, to da dama daga cikin kura-kuranmu za su ragu sosai.

Haka nan ma zunubai da laifuffukan da muke aikatawa, su ma dai mukan iya canza su, idan muka yi nadama kan ayyukan da muka aikata kana kuma muka biyo su da ayyukan kwarai.....

Ya zo cikin Alkur'ani mai girma cewa: ".....Lalle ne ayyukan kwarai suna kore munanan ayyuka". (Surar Hud, 11:114)

Ma'ana mu zo da kyawawan ayyuka don mu cike gurbin munanan ayyuka da kuma gusar da gurbinsu..... don yada alheri ita ce mafifiyar hanyar gusar da sharri a cikin zukatanmu.

11- Mu ne masu daukan nauyin kawukanmu da kuma ayyukanmu sama da wasunmu.....

Mai yiyuwa ne wasu su taimaka mana cikin wasu ayyuka, ko kuma su kasance tare da mu yayin wata musibar da ta same mu, to amma dai daga karshe mutum shi zai kasance abin tambaya kan ayyukansa kana kuma mai tsara wa kansa tafarkin da ya dace da shi, da kuma tabbatar da nasara cikin al'amurran rayuwarsa ta yau da kullum. Cikin karatu da kuma zaben abokin da ya dace, ko kuma samo girmamawan mutane, ko kuma samun fifiko cikin ayyukansa da dai sauransu.

Masu iya magana sukan ce: "Cire kayarka da hannayenka".

12- Mu san cewa nasara takan samu ta hanyar aiki da kuma juriya.....

Turawa sukan ce wai aiki yafi sautin magana daguwa......

Hakika kome zakin maganarmu ba wani amfanin da za ta yi matukar dai ba mu maisheta ta zamanto aiki ba.....shin fadin dalibi cewa lalle sai na yi nasara a jarrabawata, ya wadatar ya sanya shi samun nasarar, ko kuma karatu da kokari su ne suke sanya shi cimma wannan manufa.....

Lalle nasara ba ta samuwa don maganar fatar baki ko kuma kwadayin hakan, face dai ta kan samu ne ta hanyar aiki, kokari da kuma juriya.

13- Mu yarda da sakamakon ayyuka da kuma kokarinmu ko da kuwa wannan sakamako bai taka kara ya karya ba, don jiran wata damar da za ta zo, babu makawa irin wannan yanayi zai sanya mu cikin kwanciyar hankali a ko da yaushe. Mu dai mun riga mun yi namu kokarin, ko da kuwa ba mu sami wani abin a zo a gani ba, to mu ci gaba da bada kokari da kuma dogaro ga Ubangiji Madau-kakin Sarki har sai mun cimma burinmu da kuma samun nasara cikin ayyukan namu.....

Wadannan 'yan jumloli suna daga cikin ka'idojin da za su sanya tunani da mahangarmu, mu matasa, ta kasance mai kyau cikin rayuwa, kana kuma ma'abuciyar tafiya zuwa ga canji. Sannan kuma ta magance mana musifofin wannan tafiya ta rayuwa, abar tambaya, wacce muka fara ta bayan wuce matsayin yarinta.

Ya Ya Za Mu Amfani Ni'imomin Rayuwa?

Da yawa daga cikin matasa sukan tambayi kansu, me muka mallaka ne na daga dukiya ballan-tana ma mu dinga tunanin yadda za mu ingantata da kuma amfani da ita cikin rayuwarmu ta yau da kullum.....

Me yiyuwa ne wasu su ga kansu a matsayin marasa abin hannu saboda ba sa aikata abin da sauran manyan mutane suke aikatawa.....wannan tunani ne da ke cike da kuskure. Hakan shi ne yake sanya da yawa daga cikin matasa suke ganin rayuwa a matsayin wani duhu, musiba da kuma bala'i.....

Misali, wata matashiya 'yar shekara goma sha shida, yayin da take rubuta tarihin rayuwarta, ta rubuta cewa:

"Ba zan iya bayyana kome ba.....na wayi gari na kusan rasa duk abin da na sani, na kasance mai yawan tunani da fargaba, mara amincewa da kaina. Duk wani aikin da na fara yi sai in fara jin tsoron sakamakonsa, don haka sai in fara kokonton aikata shi, kullum cikin damuwa da bakin ciki nake. Duk lokacin da na dubi fuskata cikin madubi sai in ganta ba kyan gani, don haka sai na fara tsanan kaina, ina

mai burin da ma ba a halicce ni ba".

Wani matashi kuma cewa ya yi:

"A duk lokacin da na dubi kaina cikin madubi, ga ni saurayi, sai in tambayi kaina.....shin wai wannan da nake ganinsa yana kama da ni, zai yiyu in so shi da a ce zai fito daga cikin wannan madubi da izinin Allah kana ya rayu da ni?......"

A wasu lokuta matashi yakan mai da alhakin abin da ya same shi ga iyalansa, musamman ma mahaifansa; don kuwa ba shi da wanda zai mai da wannan tuhuma gare shi in ban da su.

Sannan an hakaito cewa wata matashiya 'yar shekara sha biyar ta ziyarci wani likita ma'abucin littattafan kan yara da kuma matasa. Ko da ta shigo wurinsa tare da mahaifiyarta sai ta bukaci da ta tattauna da shi a kebance......

Ko da suka kebance, sai wannan matashiya ta fara sukan mahaifanta da zarginsu da cewa sun hana ta dama, suna takura mata......

To sai wannan hazikin likita ya tafi wurin mahaifiyar yarinyar don ya ji ra'ayinta dangane da wannan 'ya tata, to amma sai ya ji maganarta sabanin na 'yartata. Daga nan sai ya binciki lamarin kana kuma ya yi amfani da dimbin ilimin da yake da shi, sai ya gano cewa wannan yarinya tana tsoron rashin samun nasara ne da kuma rashin damuwa da sauran mutane suka yi da ita a matsayin cikakkiyar 'ya mace. Ta ki yarda ta mai da laifin ga kanta, don haka sai ta mayar da laifin ga mahaifanta daga lokacin da suka hana ta wani abin da take so.

Hakika muna bukatuwa da kulawan iyaye a yanayi na kebance kana da kuma kulawan manyan mutane a yanayi na gaba daya, sai dai mu ba yara ba ne da za mu dogara gaba daya a kansu.....

Iyali shi ne matakin farko na tafiya, kamar yadda matafiyi ya ke fara tafiyarsa, ko kuma kamar yadda mahayin dutse ya ke fara hawa jikin dutsen......

Sannan kuma iyali shi ne mafaka, wanda muke komawa gare shi a duk lokacin da muka bukaci hakan, musamman ma a mataki mafi tsanani na rayuwa don mu sami matsuguni da kwanciyar hankali......

Duk da irin wannan matsayi da muhimmanci da iyali suke da shi, to amma dole ne mu yi shiri a wannan marhala ta rayuwa, wato lokacin samar-taka, don mu dauki wasu nauye-nauye na rayuwa, don a hankali a hankali mu sami damar daukar dukkan nauyin kawukanmu, kai har ma da na iyalanmu gaba daya a nan gaba, ko kuma al'umman da muke rayuwa a cikinta.....

Yana da kyau tun da farko tun kafin mu sanya kafafunmu cikin wannan rayuwa ta duniya, mu tambayi ce wa; wani guzuri ne wannan rayuwa ta tanadar mana na daga dukiya, karfi da iyawa, don mu yi amfani da su a cikin wannan tafiya tamu ta rayuwa? Wani karfi da iko ne Allah Madaukakin Sarki Ya tanadar mana don mu sanya su zama mana uwar kudi ko kuma jari a wannan rayuwa, har mu ba da kokari wajen ci gabantar da su da kuma amfani da su a dukkan rayuwarmu? Don haka ya zama wajibi mu kirga irin abubuwan da muke da su mu gani.

1- Hankali

Wannan shi ne mafi girman dukiya da kuma ma'ajiyar da mu 'yan'Adam muka mallaka kana kuma da shi ne muka bambanta da sauran halit-tu.....kuma shi ne kwanon da yake dauke da ilimi, tunani, masaniyya da kuma kwarewa.....sannan kuma shi ne mai shiryar da mu zuwa ga tafarkin tsira da kuma alheri, wanda kuma yake bambance mana karya da gaskiya, sharri da kuma alheri.....kuma shi ne ke kula da dukkan takun da muka yi don kada mu kauce daga hanya madaidaiciya.....

To amma shin hankali yana iya zama dukiya kana guzuri ga mutumin da ya ki amfani da shi kana kuma ma bai san girma da kimarsa ba?

Masu iya magana sukan ce hankali shi ne matai-maki (waziri) mai yin nasiha; don kuwa shawarar waziri tana amfani ne a lokacin da sarki ya mai da shi mai ba shi shawarar.....to shin za mu sanya hankalinmu a matsayin wazirinmu?

2- Iko

Shi ne wanda a wasu lokuta ake kiransa da 'yancin zaben abin da mutum yake so..... dukkanmu muna da 'yancin yin wani aiki ko kuma barinsa. Iko a wajen mutum yakan sanya shi ya zamanto sama da dukkan halittu wajen aikata abin da yake so, ko kuma barin aikata wani abin da yake bukatuwa da shi, kamar barci, hutu, ci da sha, saboda wata manufa da take sama da wadannan abubuwa.....

Da dama daga cikin magabata sun rage lokutan barci da hutawansu don bincike da kuma karatu, ta yadda suka sami ilimi mai yawan gaske kana kuma suka sami matsayi a wajen al'umma, duk kuwa da cewa ba sa tare da su......

Haka nan ma muminai sukan nisanci ci da sha yayin da suke yin azumi don su bauta wa Ubangijinsu da kuma koyon hakuri da kuma daidaita kansu da marasa abin hannu. Idan har hakuri ya kasance al'ada a gare su, to babu makawa zai iya jure wa da yawa daga cikin wahalhalun rayuwa.

Babu shakka, iko, hakuri da juriya su ne hanyo-yin nasara ga dan'Adam cikin mafi yawan ayyukansa.

3- Tausayi

Sanannen abu ne cewa tausayi yafi kasantuwa a wajen matasa, musamman ma a wajen budurwaye don kuwa su ne iyayen gobe..... muna iya ganin yanayinsu na kuka da kuma irin alaka mai tsanani da ke tsakaninsu da kawayensu ko kuma malamansu.......

Hakika ana kirga tausayi a matsayin dukiyar dan'Adam, yakan yi mu'amala da abubuwan da suke kewaye da shi (tausayi), ya so wasu kana ya ki wasu, ya yarda da wasu kana kuma ya ki yarda da wasu, ya yi fatan samun wasu kana kuma ya wofantar da wasu.....

Tausayi shi yake hada mutum da sauran mutane 'yan'uwansa, kana kuma ya dada kara masa kauna da kusanci ga masoya da kuma iyalansa da kuma damuwa da abubuwan da suke damunsu.....

Tausayi da ji a jiki sukan girma a rayuwar matashi ta yadda zai wayi gari yana mu'amala da abubuwan da suke tare da shi cikin tausayi. Za ka gan shi yana komawa karanta wakoki da labarai, kuma yana kaunar zane-zane da abubuwa masu kyau, da kuma kokarin bayyana abubuwan da yake ji a jikinsa ta hanyar zane-zane ko kuma ta hanyar baitocin wake da dai sauran hanyoyi.....

Babu shakka tausayi da ji a jiki dukiyoyi masu muhimmanci ga mutum matukar dai ya san yadda zai yi amfani da su a rayuwarsa.

4- Riyawa

Hakan ba kamar yadda wasu suke tunanin cewa yakan kawar da matashi daga hakika, ko kuma ya sanya shi ya dinga iyo cikin wata duniya ta daban, ta yadda daga baya zai lalata iko da karfinsa. To amma riyawa (wato mutum ya riya wani abu a zuiyarsa) abu ne mai kyau da kuma amfani, don kuwa tana da gudummawa mai girman gaske a rayuwar dan'Adam.....

Mai yiyuwa ne mutum ya gudu da abin da yake riyawa daga hakikanin al'amari mai daci, to amma a lokuta da dama mutum yakan koma ga riyawa da kuma jirinjiritsi, ta haka sai ya sami tsammanin faruwar alheri gare shi don kuwa yana so ya zamanto abin koyi ga saura. Kana kuma yana so ya zamanto mutum tsarkakakke marar aibi, don shi kamar yadda mai bincike ko matafiyin da yake tunanin inda zai je ko kuma abin da zai binciko tun ma kafin ya fara tafiyar ko kuma binciken yake ji, to haka shi ma yake ji......

Hakika wannan riyawa abu ne mai kyau ga wannan matafiyin ko kuma mai binciken don kuwa yana da alaka da duniyar hakika......

Riyawa dukiya ce ta hakika gare mu matukar dai mun sami damar hada ta da rayuwarmu ta hanyoyi daban-daban. Kada mu bar riyawa tayi galaba a kan hakikanin al'amurranmu ta yadda za mu ci gaba da zama cikin kogin fata da buri, haka nan kuma kada mu bari hakika ta galabci riyawa, don kada burace-burace da fatanmu su kasance a takure. Ya kamata mu bar wa riyawa gudummawarta ta fata da buri, sannan kuma mu yi riko da hakika wajen cimma wadannan burace-burace da kuma fata.

5- Lafiya...Kaddara Ce Da Ba 'a Kwatantata Da Dukiya...

Ya zo cikin hadisi cewa wajibi ne mu ribanci abubuwa biyar kafin faruwar wasu abubuwan biyar:
samartaka kafin tsufa, faraga kafin ayyuka su yi yawa, karfi kafin rauni, rashin lafiya kafin ciwo.....

Ya rage mana mu dakata mu dan yi tunani kan wannan dukiya da Allah Ya arzurtamu da ita.....yaya za mu yi idan muka rasa ta ba tare da mun shirya ba.....

Da dama daga cikin marasa lafiya sukan yi burin ina ma da suna da lafiya, don su ci gaba da ayyukansu na rayuwa.......

Hakika lafiya kaddara ce wacce dole ne mu kula da kuma kare ta ta hanyar ba ta abincin da ya dace, tsabta da kuma wasannin motsa jiki.....sannan kuma dole ne mu ba da muhimmanci ga daya bangaren kiwon lafiyan, shi ne kuwa tsabtace kawukanmu daga munanan ayyuka, keta, hassada, kiyayya da kuma canza su da kyawawan ayyuka, kamar yadda muke kula da tsabtar jikinmu.

Bayan samuwar wadannan kaddarorin, shin a matsayina na matashi zan ji cewa ni fakiri, marar abin hannu ne, musamman ma cewa wadannan ni'imomi ba wai sun kare a kan ni'imomin da na hadu da wanina a kansu ba ne, a'a akwai wadansu ni'imomin da suka kebanta da ni kawai. Don ko wane mutum akwai ni'imomin da ya kebantu da su shi kadai.....ba abin da ya rage masa face kawai ya yi amfani da kuma daukaka su kamar yadda dan kasuwa yake amfani da uwar kudinsa wajen nemo riba da hada su da uwar kudin nasa don ya ci gaba da jujjuya su.....
Bayan dukkan hakan, akwai wadansu ni'imomin da muna iya sanya su cikin rayuwarmu, kuma su haifar mana da canje-canje masu girman gaske cikin rayuwarmu sannan kuma su sanya mu mu zamanto masu iya kirkiro muhimman ayyuka da za su kai mu ga manufofi da kuma hadafofinmu na rayuwa. Wadannan ni'imomi kuwa suna nan a cikin rayuwarmu, musamman ma a shekarun samartaka, da za su iya tabbatar mana da wadansu abubuwan da ba za mu taba tunanin afkuwarsu ba.....daga cikinsu, akwai:

1- Kirkira: ita ce karfi, shiri da kuma iyawan da mutum yakan samu ta hanyar hankali, ilimin da kuma masaniyar da yake da shi......

Kirkira tana daga cikin sirrorin da suke haifar da daukaka a rayuwa, kuma takan sa ma'abucinta ya sami daman gano sabbin hanyoyin canza duniya da kuma tsira daga rashin ci gaba.....

Idan har muna son binciko irin wadannan iyawa a cikin rayuwarmu, dole ne mu sanya wadansu alamomi a gabanmu, mu bi hanyar kirkira tare da su. Wadannan alamomi kuwa su ne:

2- Imani: Karfi ne mai girman gaske wanda muke samunsa ta hanyar ingantacciyar akida da yarda da Mahaliccin duniya kana kuma Mai jujjuya ta, bugu da kari kan ganin girma da kamalarSa cikin dukkan halittu, manya da kananansu da kuma jin rahamarSa wacce ta mamaye dukkan kome. Sannan kuma ta hanyar bauta maSa, wacce take kawata mutum da karfin ruhi, mutum yakan zama mai karfi da juriya yayin wahalhalu.....

Imani ni'ima ce wacce matashi yakan same ta cikin sauki sama da waninsa saboda zuciyarsa a bude take wajen karbar yanayin rayuwa, shin wannan yanayi na madda (duniya) ne ko kuma na ma'anawiyya (na ruhi da lamurra lahira).

3- Madaukakiyar Himma: Wannan wata ni'ima ce da kuma karfi mai girman gaske da ke kai mutum zuwa ga manufarsa da kuma nesantar da shi daga fargaba da kuma yanke kauna.

An ruwaito wani hadisi yana cewa mutum yana tashi da himmarsa kamar yadda tsuntsu yake tashi da fuka-fukansa.....don haka mutum yana bukatuwa da himma madaukakiya a hanyarsa ta isa ga sa'ada da kuma ci gaba.....wannan hanya da take tabbatar masa da manufarsa ta rayuwa.....

Lalle babu makawa muna iya isa ga wannan babbar ni'ima idan muka yi riko da wasu ka'idoji a rayuwarmu, su ne kuwa:

  1. Mu dinga tuna cewa mu mutane ne kuma za mu iya kaiwa zuwa ga kamalar da muke so.
  2. Mu daure taragonmu zuwa ga tauraro (sama), kamar yadda masu iya magana su kan ce wai: himma bata ga rago.
  3. Kada mu shagaltar da kanmu da kananan al'amurra marasa muhimmanci.
  4. Mu kyautata alakarmu da sauran mutane, kada mu bari maslaharmu ta kewaye mu.
  5. Mu kasance masu kula da ka'ida hatta cikin zaben manufofi da hanyoyin da za mu isa gare su.
  6. Mu ba da muhimmanci ga kyawun badini kamar yadda muke kula da kyawun zahiri.
  7. Mu zabi abokai masu madaukakiyar himma.

Abubuwan da muka ambata a wannan fasali su ne mafi muhimmancin ni'ima da kyautar da muka mallaka mu matasa, ko kuma abubuwan da muke da damar samo su ta hanyar karfi da kuma shirin da muke da shi. Lalle ya kamata mu yi imani da cewa rayuwa da kuma Mahaliccinta Suna iya kara mana wadannan ni'imomi, matukar dai muka ci gaba da bincike da kuma bahasi, don kuwa ajiyoyin rayuwa ba sa da iyaka "....kuma idan kun kidaya ni'imar Allah ba za ku lissafe ta ba.....".

Ya Ya Za Mu Iya Guje Wa Sharrin Rayuwa?

Hakika dan'Adam ma'abucin manufa da sako ne, to amma abin tambaya a nan shi ne mene ne sakonsa a wannan duniya?

An halicci dan'Adam ne don neman alheri da kuma sa'ada a rayuwa, kana kuma ya guje wa sharrori da kuma abubuwan da za su kai shi zuwa ga halaka. Don haka cikin rayuwa akwai alheri da kuma sharri, dan'Adam shi ne mai zaba wa kansa abin da ya dace da shi na daga alheri da kuma nesantar abubuwan sharri wadanda ba su dace da shi ba.

Ya 'yan'uwa, idan da a ce wani mutumin da ba mu san shi ba zai ba mu abinci ko kuma halawa, shin za mu kama ci ko sha ne haka kawai daga ya ba mu, ko kuma za mu tsaya mu gani cewa wannan abinci ko kuma halawar suna da tsabta alal akalla?

Lalle mu mukan zabi tsabta cikin dukkan abin da za mu ci ko kuma za mu yi amfani da shi don kiyaye kanmu daga kwayoyin cutar da za su janyo mana cututtuka da kuma sanya lafiyarmu cikin hatsari. Don haka wajibi ne mu aikata haka ga munanan ayyukan da suke lalata mana dabi'u da kuma mutumci.

Sannan kuma a duk lokacin da mutum ya kamu da wata cuta yakan tafi wajen likita don neman maganin wannan cuta, sai dai kuma a wasu lokuta yakan kamu da cutar ruhi, to amma sai ya ki zuwa neman magani; don kuwa ba ya ganinta a fili, amma kuwa tana iya lalata masa al'amurra daga karshe.

Dukkanmu, baya ga jiki, muna da ruhi da kuma hankali, don haka mafi munin sharrin rayuwa shi ne abin da yake damun ruhinmu da kuma lalata mana tsare-tsarenmu mu na kyawawan halaye.

Wadannan tsare-tsare na kyawawan halaye su ne suke nuni da daukakar dan'Adam da kuma ruhinsa, don haka idan dan'Adam ya rasa wadannan tsare-tsare, to babu abin da ya saura masa in ban da kawai abubuwa marasa amfani a rayuwarsa kuma zai yi rayuwa ce irin ta dabbobi da tsirrai.

Siffofin daukaka da alheri sukan arzurta mutum da abubuwan da za su taimaka masa da kuma sanya shi ya zamanto mabubbugar alheri ga kansa da kuma sauran mutanen da yake tare da su.

Baya ga haka kuma, akwai wata hakikar, ita ce kuwa cewa, mutum a wannan rayuwa yana nan ne tsakanin tuddan alheri da kuma na sharri.....don haka duk lokacin da ya kusanci tudun alheri, da hakan ne kuma zai nesanci tudun sharri.....

Idan waninmu yana da wani aboki da yake sadaukar da kansa dominsa a duk lokacin da yake fuskantar wata matsala, to a hakikanin gaskiya babu yadda za a yi ya cuce shi ko kuma ha'ince shi.....don haka sakamakon hakan shi ne son abokanmu da kuma fahimtar abubuwan da suke kewaye da mu.

Haka nan kuma idan wani daga cikinmu ya kasance mai biyayya ga mahaifansa, hakan yana nuni da cewa kenan ba za mu saba musu ba, kuma babu makawa abin da za mu samu shi ne kauna da kuma girmamawarsu gare mu, ko kuma kaunar sauran mutane da kuma girmamawarsu gare mu. Sannan kuma sama da hakan shi ne kauna da kuma yardar Ubangiji Madaukakin Sarki gare mu.

Wadansu mutane suna kokarin nuna mana cewa ma'anar alheri shi ne nisantar dadin duniya da kuma kaurace musu. To amma a gaskiya ma'anar alheri shi ne kyautata mu'amala da ni'imomi da iyawan da aka arzurtamu da su. Shi ne kuwa amfani da wadannan abubuwan jin dadi ta hanyar da ta dace.

Don kuwa Wanda Ya arzurtamu da wadannan ni'imomi da kuma iyawa ba Ya so ya haramta mana dadinsu, face dai so Yake mu yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace da za su sanya mu a kan tafarkin alheri har abada.

Saboda haka sharri shi ne mu gagara amfani da wadannan ni'imomi ta hanyar da ta dace da kuma mance manufofin da suka sa aka arzurtamu da su. To amma tambayar da take da muhimmanci a nan ita ce, mene ne yake sanya mu a wasu lokuta mukan zabi sharri duk kuwa da irin bala'in da ke tattare da shi ko kuma muke ba shi damar ya shiga cikin rayuwarmu ta samartaka mai kyawun fuska?!

Amsa wannan tambaya tana bukatuwa da gabatar da wasu tambayoyin na daban.

Shin muna daga cikin mutanen da suke kaskantar da kansu da cin mutumcin kansu ne? idan kuwa har haka ne, to sharri zai mamaye mu.......

Babu wani daga cikinmu da zai yarda a ce masa wani shugaba daga cikin shuwagabannin kasashe ko kuma ja-gora daga cikin ja-gorori zai sunkuya kasa don daukan wani abu maras amfani.

Mai yiyuwa ne wannan abu yana da girma da muhimmanci ga wasu, to amma irin girman shugaba ko kuma ja-gora zai hana shi damuwa da wannan abu, kuma bai kamance shi yayi hakan ba. Hakan nan ma, bai dace da mu 'yan'Adam ba mu bar kawukanmu su zamanto wajajen gwajin munanan ayyuka, hassada, zalunci, karya, sata, da dai zunubai da sharrori.

Shin muna daga cikin masu wasa da abokan gaba?

To alal akalla kada mu yi haka da abokan gabanmu na daga kwayoyin cuta.....shin za mu yi haka da sauran nau'in kwayoyin cuta, wato kwayoyin cutar munanan ayyuka?.

Akwai wata kissa ta sahabban Annabi (s.a.w.a.) lokacin da suke tare da shi a wani bushasshen guri kuma ga shi ana tsananin sanyi. Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya tambaye su ko za su iya tattaro itatuwa don su kunna wuta da kuma jin dumi?

Sai dukkan sahabban suka ce: babu tsiro ko bishiya a wannan wuri ya ya za su iya hado itatuwa?

Sai Annabi (s.a.w.a.) ya ce musu: to kowannen-ku ya tafi ya nemo abin da ya sawwaka.

Sai sahabbai suka bazama don nemo duk wani abin da suka gani na daga kayoyi da busassun tsirrai, daga nan sai suka zo wajen Manzon Allah (s.a.w.a.) tare da itatuwa masu yawan gaske.

Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) yace musu, da haka ne kananan zunubai suke taruwa da yawa kamar yadda kuka tattaro wadannan itatuwa. Sannan kuma ya ce musu: ina gargadinku da kananan zunubai.

Shin muna daga cikin wadanda ba sa gani face abubuwan da suke gaban kafufunsu, kuma ba sa ganin abubuwan da za su faru nan gaba sannan kuma suke jahiltar karshen al'amurra?

Da wuya ace dokin da ke daure a jikin injin tatsan rake don jujjuya shi, kamar yadda ake yi a da ko kuma a halin yanzu a wasu wurare, zai nuna bacin rai kan wannan aiki ga shi kuwa yana tafiyar dubban mila-milai ba tare da ya bar inda yake ba.....

Mai yiyuwa ne hakan ya faru saboda shi abin da ke gaban kafafuwansa kawai yake gani, to amma wanda yake ganinsa daga nesa da kuma wajen injin zai tausaya masa halin da yake ciki.....

Shin muna daga cikin wadanda suke ba da muhimmanci ga harkokinsu ne kawai? Idan har al'amarin haka ne, to mun kasance kamar kwadon da ke cikin rijiya kuma ba ya so ya bar cikinta, amma yana ganin duniya kawai ita ce abin da ke kewaye da wannan rijiya, bai san abin da ke wajen wannan rijiya ba da suka hada gonaki da sauran ruwayen da suke gudu a wajen rijiyar.