Annabin Allah Adam (A.S)

 Dalilin halittar Adam a.s.

An ruwaito cewa, Kafin halittar Adam  tsira da aminci Allah su tabbata garesa Duniya ta kasance cike take da aljannu da dabbobi masu fada da makamantansu. Sannan kuma ya kasance Allah madaukaki yana da wakilai a bayan kasa wadan da suke umurni da aiki kyakkyawa kuma suna hani da mummunan aiki.

 Har zuwa lokacin da aljannu suka kangarewa Allah suka yi taurin kai, sannan suka saba wa Allah  madaukaki. Suka canza suka kirkiro bidi'o da ayyukan assha. Sai Allah ya umurci mala'iku da su  duba zuwa ga halittar kasa wadda ke cikin fadin Duniya, sanna su kalli abin da suke aikatawa na daga ayyukan assha, sai ya umurce da su canza wadannan halittu su halitta wadansunsu wadan da zasu zama wakilan Allah kuma suna bauta masa. Sannan sai Allah madaukai ya ce musu :"zan sanya khalifana a bayan kasa", sa suka ce masa:"  tsarki da daukaka sun tabbata a gareka ya ubangijinmu, Yanzu ka sa wanda zai rika barna da zubar da jini a bayan kasa?" kamar yadda aljannu suka rika yi, ka sanya mu a bayan kasa matsayin khalifofinka ta yadda zamu rika tasbihi da godiyarka, sannan muna tsarkake sunanka. Sannan muna yin biyayya ga abin ka umurce mu da shi. Sai Allah madaukakin sarki ya ce musu:" Ni nasan abin da ba ku sani ba".

 Sai Allah ya tayar da Mala'ika Jabra'il, ya aika sa ya debo kasa ya mayar da ita yumbu sai ya halitta Adam daga wannan  yumbu ya dai-daita halittarsa ya hura masa rai.

Halittar Hauwa'u Matar Adam A.s.

Allah madaukaki ya sa wa sabuwar halittarsa suna Adam, sannan sai Allah ya halicci Hauwa'u matarsa daga sauran yumbun da ya yi saura daga halittar Adam a.s.

  Sai Adam a.s ya kalli hauwa'u ya ganta halitta makamanciyarsa, sai dai  kawai ita mace ce. Sai ya yi mata magana kuma ta ba shi amsa da  harshensa. Sai Adam ya tambaye ta wace ce ita? sai ta ce masa: Ni  halitta ce da Allah ya halitta ni.

 Sai Allah ya sanar da Adam dukkan sunayen abubuwa kuma ya sanya tausayi da kauna a tsakaninsa da  Hauwa'u. Don haka sai ya yi kwadayin kallonta da magana da ita sai ya je kusa da ita, sannan sai ya tambayi Allah cewa wace ce wannan halitta mai kyau haka wadda nake kwadayin kallonta da kuma  kusanci zuwa gareta? Sai jawabi ya zo masa da cewa: ya Adam wannan Hauwa'u ce kana so ta kasance tare da kai  da kauna, kuma kuna masu Magana tare? Sai Adam ya ce: E ya Ubangiji godiya ta tabbata gareka.Sai Allah ya ce masa to baiwata ce ka neme ta daga gare ni, sai ya ce to ina nema ya ubangiji ka yarda? Sai Allah madaukaki ya ce yardata ita ce ka koyar da ita ilimin addinina. Sai Adam ya ce wannan yana gareka ya ubangiji idan ka so zai yiwu.sai Allah ya ce lallai na so hakan kuma na aura maka ita. Sai Adam ya yarda kuma Hauwa'u ta zama matarsa.

Girmama Adam da kin sujjar iblis ga Adam

Allah madaukaki ya yi nufi a bauta masa ta hanyar sabuwar halittarsa Adam, don haka sai ya umurci mala'iku da su yi masa sujjada don girmamasa, sai dukkan mala'iku suka fadi suka yi gaisuwa ga Adam a.s.

 Amma Iblis ya kasance daga aljannu ya kansa ce tare da mala'iku lokacin da Allah ya umurce su da su yi  wa  Adam sujjada a matsayin girmamawa, Iblis ya kasance an halitta shi ne daga wuta kuma mai tsananin biyayya ga ubangijinsa don haka ne ya samu damar kusantar Ubangiji, sannan ya san shi cikin sahun mala'iku. Amma sai Iblis ya sabawa ubangiji a wannan karo ya ki yin sujjada ga Adam a.s. ya kasance mai girman kai yana neman uzri akan umurnin Allah na yin sujjada ga Adam.Don haka ne ya kasance duk ibadar da ya yi ta tafi a banza, duk da cewa babu wanda ya yi ibada kamarsa a cikin mala'iku ko Annabawa. Sai ya cigaba da neman uzri akan cewa wai Allah ya halicce shi da wuta al halin Allah ya halicci Adam da yumbu, domin yana ganin cewa lallai ai wuta tafi yumbu, ya za'a yi ya girmama wanda aka yi da yumbu alhalin ya fi shi.

 Allah madaukakin sarki yana so ne a bauta masa kamar yadda yake so ba yadda shaidan yake bukata ba, don haka ne Allah ya la'ance shi kuma ya  kore shi daga rahamarsa.sannan Allah ya haramta masa wasu karamomi da yake da su kamar yadda mala'iku suke da su, ya kasance tababbe har zuwa ranar kiyama kuma zai kasance tare da wadan da suka bi shi a cikin  matsananciyar azaba.

Lokacin da Iblis ya ga hushin Ubangiji ya tabbata gare shi ya sai nemi ladar ibadar da ya yi a sheka da shekaru a wajen Ubangiji, abin da ya nema kuwa shi ne Allah ya ba shi damar ya rayu har zuwa ranar kiyama. Sai kuwa Allah ya ba shi wannan dama. Ya nemi wannan dama ne kuwa domin ya yi ramuwar gayya ga Adam wanda ya sa aka nesantar da shi daga rahamar Allah. Sannan kuma ya nemi damar ya samu dama akan Adam da 'ya'yansa wato dukkan mutane. Don haka sai shaidan ya cigaba da girman kai yana da'awar cewa wai ya fi karfin Adam da zuriyarsa. Don haka ne ya ke cewa ai sai  ya batar da duk zuriyar Adam sai kawai yan kadan daga cikinsu.

Adam na neman taimako daga Allah

Kamar yadda muka fada a baya Allah ya ba Iblis damar rayuwa har zuwa ranar tashin kiyama, sannan ya samu dama akan mutanen da suka bi shi, sai kawai salihan bayi wadan da suka yi ayyukan kwarai, wadannan ba ya da iko akansu.

Adam A.s. da ya fahimci haka, shi ne yake cewa Allah kai ne kawai kake da iko akan bayinka, kai ne ka ba Iblis wannan dama kuma kai  ne kake da iko akan komi, Ya Allah ina neman tsarinka. Sai Allah ya ce wa Adam ka je duk wanda ya aikata mummuna daga zuriyarka yana da zunubi guda, idan kuma ya aikata mai kyau yana da lada goma. Sai Annabi Adam ya cigaba da cewa ya Ubangiji a kara. Sai Allah madaukaki ya ce to zan gafara ga bayinka ba tareda kulawa ba. Sai Adam a.s ya ce ya yi ya uabangiji.

Mantuwar Adam da kuskurensu.

Allah madaukaki ya zaunar da Adam da Hauwa'u a gidan Aljanna,sannan ya yi musu kashedi da Iblis cewa lallai su yi hankali da shi kuma abokin gabarsu ne kada ya fitar da su daga gidan Aljanna.Sannan Alllah ya hane su da kada su ci wata itaciya a gidan Aljanna amma suna iya cin kowace ban da ita. Amma sai Iblis ya zo musu da sura ta yaudara ya ce musu ai idan suka ci wannan itaciya to lallai zasu dawwama a gidan Aljanna. Adam da matarsa sun manta da kashedi da Allah ya yi musu na kada su yi kusa ma da itaciyar nan, kuma lallai kada  su yarda da yaudarar shedan domin, makiyinsu ne, don haka suka bi yaudarar Shaidan suka ci wannan itaciya. Sakamakon yadda Shaidan ya bayyana matsayin maikaunarsu kuma maitausaya musu.Domin ya nuna musu cewa idan suka ci wannan itaciya ai zasu iya komawa ma Mala'iku ko kuma su dawwama a rayuwa ba zasu mutu ba.

 Bayan kuwa Adam da Hauwa'u sun ci wannan Itaciya sai Allah madaukaki ya fitar da su daga gidan Aljanna, inda Adam ya sauka a wani wuri cikin India ita kuwa Ahuwa'u a jidda kamar yadda aka nuna cikin tarihi da ruwayoyi.

 Annabi Adam da Hauwa'u da sauran Mal'iku sun yi bakin ciki da fitar Adam daga Aljanna.

Gafarar ubangiji ga Adam da Hauwa'u:

Bayan saukar Adam da Ahauwa'u daga  gidan Aljanna sai Allah ya aika mala'ika zuwa ga gare su cewa ya gafarta musu, sannan ya aika musu da hemar gidan Aljanna domin su samu inda zasu zauna a cikin duniya.

Bayan nan Allah ya umurci Annabi Adam Adam da da'a zuwa gare shi sannan kada su yi shirka da shi, sannan Allah ya yi musu albishir da cewa duk wanda ya bi Allah daga cikin bayinsa zasu koma wancan gidan Aljanna mai ni'ima. Haka Dai Ada da  Hauwa'u suka cigaba da rayuwa a cikin duniya suna haihuwa har duniya ta cika da bil Adam.

 Ya 'yan uwa musulmi wannan kissa tana cike da abubuwan lura a ckin rayuwa ta yadda take nuna mana cewa mu yi  la'akari sosai a rayuwarmu, mu kaucewa sabon Allah, domin sakamakonsa ba mu san yadda zai kasance ba. Muna ga dai yadda shaidan ya kasance mai girma da daukaka amma laifi daya ya yi, ya fitar da shi daga rahmar Ubangiji har abada. Don haka dole ne mu yi hankali mu guji sabon Allah domin ba mu sani ba kada ya zama sakamakon tabewarmu wa 'iyazu billah. Alla ya kiyashe mu Amin.