Shahriyar Farhizkor

An haifi malami a garin   a garin Tehran a shekara ta 1343 H.S. Iya yensa sun kasance masu son addini, wannan ya taimaka masa wajen ba da himma wajen karatu kur'ani.

 malamin ya fara sauraren katun malamin nan wato Abdul Basit tun yana yaro  ya fara koyon muryarsa kamar dai yadda makaranta sukan yi, farkon koyon karatunsu wato kafin su kware suma su kirkiro samfari da launin karatu na su na kansu.

 Malamin tun yana yaro ya kan kamanta kansa kamar yana cikin gasar karatu kuma mutane suna sauraren sa,da haka ne ya yi ta himma da kokari yana tarbiyyntar da kansa akan karatun Kur'ani.

Malamin ya yi nasara wajen samun mataki na farko a wajen gasar karatu ta duniya da ta cikin gida a lokutta da dama.

 Malamin karkashin tarbiyar malaminsa Maulayi ya samu damar hardace kur'ani mai girma.

Malamin bayan gama karatunsa na gaba da firamare ya cigaba da karatu a Jamia inda ya yi karatu a fannin konfuta wato ya samu digri na farko a wajen.

  sannan malamin ya yi aure a shekara ta 1360 wanda a sakamakon haka ne ya samu yara guda biyu.

Daga cikin abubuwan da ba zai manta ba a rayuwarsa shi ne, shiga dakin ka aba da ya yi lokacin da ya je gasar karatu saudiyya a shekara ta 1366 wannan abu yana alfahri da shi a rayuwarsa.

malamin ya kasance yana gudanar da majalisoshi daban- daban a cikin Iran haka nan ma ya gudanar da irin wannann majlisin a lokacin yakin Iran Iraqi don kara wa sojojinsu kwarin guiwa.

 Malamin ya yi kira zuwa ga matasa da su maida hankalinsu akan kur' ani da hidma akansa. tare da yin hakan zamu iya warware matsalolin da suka dame mu.  

    Wannan shi ne takaitacen tarihin rayuwar malamin. Da fatan Allah ya kara yawaita irinsu din yi wa kur’ani hidima  amin.