Index

Mene ne Kur'ani

Kur'ani wahayin Ubangiji ne da ya sauko daga Allah a harshen AnnabinSa, akwai bayanin kome da kome a cikinsa shi ne Mu'ujiza madawwamiya wadda ta gagari bil Adama wajen karawa da ita a fasaha da azanci, abinda ya kunsa na daga hakika da sannai madaukaka, jirkita ko canji ko karkacewa ba sa shafar sa, Allah Ta'ala yana cewa: "Mu Mu ne Muka saukar da ambato kuma Mu gare shi lalle masu kariya ne". Surar Hijri: 9.

Alkur'anin da ke hannunmu wanda ke karanta shi a yau shi ne wanda aka saukar wa Annabi (S.A.W) duk kuma wanda ya yi da'awar sabanin wannan to shi mai kage ne, ko mai rikitarwa ko mai kuskure ne dukaninsu kuma ba a kan shiriya suke ba, domin shi Alkur'an zancen Allah ne wanda Karya ba ta zuwa masa ta gaba gare shi ko kuma ta bayansa. Surar Fusilat: 42.

Daga cikin dalilan da ke tabbatar da mu'ujizarsa akwai cewa duk yayin da zamani ya dada tsawo ilimi da fasaha kuma suka dada ci gaba shi yana nan daram a kan abubuwan da yake kaddamarwa da daukarkar manufa da abubuwan da ya kunsa na ra'ayoyi babu wani kuskure da ke bayyana daga cikinsa dangane da tabbatattun matsayi na ilimi kamar kuma yadda ba ya taba kunsar tawaya game da falsafa ta hakika da yakini sabanin littafan da malamai da manyan masanan falsafa kome matsayin da suka kai kuwa a fagen ilimi da kuma amfani da kwakwalwa da tunani. Domin duk yayin da bincike ya ci gaba to yakan bayyana a sarari cewa rarrauna ne ko sabo ne ko kuma kuskure hatta a gurin manyan masana falsafar kasar girka kamarsu Sakarot da­ Aplato da Arostatle wadanda kowa da kowa daga cikin wadanda suka zo daga bayansu suka yi musu shaida da cewa su ne iyayen ilimi da kuma amfani da kwakwalwa.

Kazalika mun yi imani da mutunta Alkur'ani mai girma da daukaka shi a magana da kuma a aiki. Bai halatta a najasta koda kalma guda a cikinsa wadda aka dauka cewa yanki ne daga cikinsa da kuma nufin cewa daga cikinsa take, Kamar kuma yadda bai halatta ba ga wanda ba shi da tsarki ya shafa kalmominsa ko harrufansa: "Babu mai shafa shi sai wadanda suke tsarkakakku". Surar Waki'a: 79.

Sawa'un sun kasance suna da babban kari ne kamar janaba ko haila ko jinin biki da makamantansu, ko kuma karamin kari koda ma barci ne kuwa sai dai bayan yin alwala ko kuma yin wannan a bisa asasin filla-fillan bayanan da ke cikin littafan fikihu.

Haka nan bai halatta a kona su ba, bai halatta wulakanta shi ba, koda ta wace fuska ne kuwa da yake sananne a tsakanin mutane kamar jefarwa, ko sanya masa kazanta, ko shurin sa da kafa, ko sanya shi a guri wulakantacce, Idan da wani zai wulakanta shi da gangan ko tozarta shi da aikata daya daga cikin wadannan abubuwan da muka ambata da makamantansu to shi ya shiga cikin masu karyata Addinin Musulunci da abubuwan tsarkakewarsa, kuma abin hukuntawa ne da ficewa daga Addini da kafircewa ga Ubangijin talikai.

Daga Littafin: Akidojin Imamiyya na MUZAFFAR