Iyalina

Wadda Ta Wallafa:MU'ASSASAR AL-BALAGH

Wanda Ya Fassara:MUHAMMAD AWWAL BAUCHI

Rayuwar dan'Adam takan fara ne daga lokacin da aka haife shi har zuwa lokacin da zai koma ga Mahaliccinsa, sai dai kawai rayuwar takan bi matakai ne har lokacin da za ta kure abin da aka diba mata a wannan duniya. To daga cikin irin wadannan matakai akwai lokacin samartaka, wanda yake da muhimmancin gaske cikin rayuwar dan'Adam.

A wannan lokacin ne ake sa ran dan'Adam ya fara sanin inda yake masa ciwo, don haka ne ma yake fara tunani kamar haka:

An haife ni cikin soyayyar mahaifiyata.....an haifi soyayya a kewaye da ni.....an haife ni cikin iyalina da kuma soyayya ga rayuwa ta.....ina iya tuna ranakun yarintata.....na kasance dan karamin yaro, ina wasa a kewayen gidanmu tare da 'yan'uwana kanana.....ban san mece ce rayuwa ba.....kuma mene ne nauyi ba.....face dai na samu an shirya min duk abin da nake bukata..... rayuwa ba ta kasance kome ba a gare ni in ban da wasa da kuma barci.....

Kai! Wani irin farin ciki ne yake rufe ni a duk lokacin da babana ya kawo min halawa a lokacin da ya dawo daga aiki.....ko kuma lokacin da mahaifiyarta ko kuma kakarta ta saya min riga ko kuma wani abin wasa don in yi wasa da shi.....

Ko kuma a lokuta da dama na kan tuna kalmo-min soyayya da kauna da kakana yake gaya min da kuma nuna min.....

Dukkan abin da nake bukatuwa da shi a kan samar da shi gare ni.....babana da mahaifiyata su kan samar min da shi ba tare da gori ko cutarwa ba.....face ma dai babban burinsu shi ne su wahala don nema min abin rayuwa da kuma jin dadina.....

Ina tuna irin soyayya da kuma kulawar da iyayena suke nuna min tare da sauran 'yan'uwana kanana......

An haife ni cikin iyalina, kuma a cikinsu ne na tashi, sannan kuma na girma tare da 'yan'uwana .....

Wadannan su ne iyalina: mahaifi da mahaifiyata, kakana namiji da kakata mace, 'yan'uwana, wadanda suka girme min da wadanda na girme musu......

Hakika wannan hikimar Ubangiji ne da Ya halicci mutum a matsayin halitta ma'abuciyar hadin gwiwa da 'yar'uwarta, da kuma gina rayuwa a karkashin so da tausasawa.....a karkashin so, girmamawa da kuma cudaddeniya.....kana kuma iyaye da 'ya'yansu su rayu cikin wannan madaukakiyar da'irar.....wato da'irar iyali.....da'irar so da kauna......

A wasu lokuta nakan zauna ni kadai ina tunanin makomar rayuwata......

To a halin yanzu wannan matsayin na yarinta ya wuce.....a halin yanzu zan fara wani sabon matsayi ne.....matsayin nauyi dangane da Ubangijina Wanda Ya arzurta ni da falaloli da kuma ni'imomi, kana kuma a kan kaina, iyalai da kuma al'ummata..... kai hatta ma a kan dukkan nau'in dan'Adam da kuma iyalinsa.....

A halin yanzu na zama mutum abin tambaya dangane da iyalansa.....hakika yanayina ya cika, haka kuma tunanina, amma duk da haka ina bukatuwa da nasihohin mahaifana.....ina bukatuwa da iliminsu da kuma ilmummukan sauran mutane.....don kuwa wani kogi ne da ke cike da ruwa da igiyar ruwa, dole ne in kama ingantaccen tafarkin da zai kai ni ga tudun tsira.

Kasantuwa ta memba a cikin iyalina yakan haifar min da wasu hakkoki a cikin al'umma da kuma tabbatar min da wasu ayyukana wajibi.....don kuwa rayuwa a duniyar iyali takan haifar da alakoki tsakanin mutanen cikinsa, tsakanin uwa da uba, tsakanin iyaye da 'ya'yayensu, tsakanin 'ya'yayen kansu, a matsayinsu na 'yau'uwan da ke raye cikin al'umma guda, ta 'yan'uwantaka, akida, gida, cin abinci da kuma tattaunawa take hada su waje guda. Hakanan kuma tafarki da 'yan'uwantaka ta hada su waje guda.

Kewayen Iyali

Kewayen iyali shi ne yanayin rayuwa da kuma alakokin da suke kewaye da ita da suka hada da soyayya, girmamawa, cudaddeniya, fahimtar juna, sadaukarwa, ciyarwa da kuma amfani da dukiya, tsari, kula da kai da kuma lokaci, kokari, nisantar saba doka, son kai.....kasala, rashin tsari, wasa da lokaci, yawan magana da musun da ba shi da amfani da dai sauransu.

Mai yiwuwa ne a samu dukkan wadannan halaye a cikin iyali.....masu kyaun cikinsu da marasa kyau..... dukkan wata dabi'a ko kuma hali yana da nasa tasirin cikin kafa iyali da kuma halayen mutanen cikinsa, kamar yadda a lokuta da dama yara sukan dauki siffofin iyayensu. To mai yiwuwa ne su dauki wasu siffofi na rayuwa, kamar yadda suke daukan wasu halaye da dabi'u daga wajen iyalansu, ta yarda za su zamanto sashi na rayuwarsu. To hakanan ne suke daukan kyawawa da kuma munanan halaye da siffofi daga wajen iyalinsu.

Hakika tafarkin tsira da kuma tsarkake kewayen iyali daga irin wadannan matsaloli, shi ne mu ba da gagarumar gudummawa wajen sana'anta kyawawan halaye da kuma nesantar munanan dabi'u. Don kuwa samar da mummunan yanayi ga iyali yakan bata dukkan al'umma gaba daya.....sannan kuma ya canza yanayin alheri da daukaka zuwa ga yanayin sharri da halaka......

Iyali wuri ne da muke hutawa daga gajiyar aikace-aikace da kuma matsalolin rayuwa......

Don kuwa samuwar yanayi mai kyau da ke cike da so, kauna da kuma girmamawa yakan mantar da mutum wahalhalun rayuwa da kuma rage masa damuwa da rashin tabbas din da yake damunsa.....

Hakika a duk lokacin da rayuwa ta canza ta zamanto cike take da damuwa da rashin tabbas, to takan haifar da mummunan yanayi ga mutum da kuma cutar da lafiya da kuma tunaninsa.

Ya Ya Zan Yi Mu'amala Da Mahaifina?

Dukkan wani abin da yake a wannan duniya, da suka hada da sama, tsirrai da kuma dabi'a duk suna tafiya ne a kan tsari da kuma doka.....to haka ita ma rayuwar 'yan'Adam, babu yadda za ta iya tafiya kamar yadda ya kamata, matukar dai babu wasu dokoki da kuma tsari.....don haka dukkan wani abu a wannan duniya tamu, cibiyoyi, kamfanoni, ofisoshin gwamnati, da dai sauransu, suna bukatu-wa da tsari......

Iyali wata cibiya ce mai muhimmanci daga cikin cibiyoyin rayuwa, don haka take bukatuwa ga dokoki da za su tsara da kuma tafiyar da rayuwa a cikinsa, bugu da kari kan alakoki tsakanin dangi. Hakan kuwa shi ne abin da shari'ar Musulunci ta tsara, yayin da ta tsara hakkoki da kuma wajibai. Sannan kuma kamar yadda muka sani ne cewa dukkan wata ma'aikata tana da hukumar gudanarwa da kuma shugaban da yake gudanar da ita da kuma tabbatar da doka a cikinta.....

To haka ma dabi'ar iyali take tabbatar da uba a matsayin mai shugabantar iyali kana kuma mai daukan nauyinsu. Haka Allah Ya so, Ya sanya mahaifi yana iko a kan 'ya'yansa kanana wadanda ba su balaga ba, ya kallafa masa ciyar da su da kuma basu tarbiyya, kamar yadda ya kallafa masa ciyar da matarsa da kuma daukan nauyin dukkan iyalinsa.

Don hakanauyin uba yafi na sauran iyalansa, don haka ne kuma Allah Madaukakin Sarki Ya umurci 'ya'yaye da su girmama iyayensu da kuma yi musu da'a matukar dai suna kan tafarkin kirki da tabbatar da musu da alherin duniya da na lahira......

Uba yakan ba da muhimmancin gaske wajen kula da 'ya'yayensa da kuma ba da kokari wajen tabbatar da mashalolinsu. Shi yana so ya gansu sun yi nasara a yayin karatunsu.....yana so ya ji jama'a suna yabonsu.. yana so ya gansu suna ba da kokari a ayyukan da suka sa a gabansu.....yana kuma son ya ga sun nesanci duk wani abin da zai zubar musu da mutumci da kuma cutar da su, ta yadda za su zamanto abin kyama a idon mutane.

A koda yaushe mahaifi yakan so ya ga 'ya'yansa sun kwaikwayi halayensa da kuma rayuwarsa, don haka yake ba da dukkan kokari da kuma kulawansa ga 'ya'yan ta yadda ba za su iya mayar masa da shi ba, hakanan shi ma kuma ba zai iya mayar da shi ba. A saboda haka ne yake jin zafin gaske a lokacin da ya ga 'ya'yansa suna rashin nasara a cikin rayuwarsu, ko kuma idan suka zama abin kyama da Allah wadai din al'umma, sannan kuma masu jawo wa iyayensu abin kunya da cutarwa a tsakanin al'umma.....

Alhali kuwa yakan kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali a duk lokacin da ya ga 'ya'yansa maza da mata sun cim ma nasara cikin rayuwarsu da kuma zama abin girmamawan al'umma, suna masu tabbatar masa da mutumci, kwanciyar hankali da farin ciki saboda kyawawan ayyukansu.....nasara cikin karatu.....cikin alaka tsakanin abokansu.....cikin alakarsu ta soyayya a tsakaninsu, a matsayinsu na 'yan'uwa ma'abuta hadin kai.....

Don haka za mu ganshi cikin bakin ciki da jin zafi a duk lokacin da ya gansu sun aikata wani aiki mummuna, ko kuma a lokacin da suke tattauna wasu matsaloli masu cutarwa ga iyalinsu a cikin gidan, ko kuma idan suka fadi a jarrabawarsu, ko kuma suna munana alakarsu da sauran abokan-su.....ko kuma a lokacin da suke aikata munanan ayyuka, irinsu almubazzaranci, shan taba, caca, cutar da sauran mutane da dai sauransu.

Hakika munanan ayyuka sukan zubar da mutumcin mutum, kuma yakan tabbatar wa mutane cewa ya taso ne daga mummunan gida, ta haka ne mummunan tasirinsa yakan koma ga iyaye.

To wannan shi ne yadda uba yake ji dangane da 'ya'yayensa ko da yake mai yiwuwa ne 'ya'yayen ba za su fahimci hakan ba, daga baya matsala ta faru kana kuma ta munana alakar da ke tsakanin 'ya'ya da iyayensu. Don haka fahimtar yara da yadda iyayensu suke ji dangane da su al'amari ne da zai magance da yawa daga cikin matsaloli da kuma haifar da ruhin fahimta da kuma soyayya tsakaninsu......da kuma sanya yaran su fahimci abubuwan da suke bata rayukan iyayensu don su nesance su.

Babu shakka gina iyali ma'abuciyar nasara shi ne gina kyawawan dabi'u da kuma sauran al'amurran duniya a lokaci guda, don kuwa nasara cikin wani al'amari ta kan samu da farko cikin kyawawan dabi'u kafin al'amurran duniya.....

Akwai wasu asasi na kyawawan alaka tsakanin iyaye da 'ya'yayensu wadanda suke tabbatar da nasara da kuma yardar Allah a tsakanin al'umma.....

Hakika bukatuwar iyali, iyaye da 'ya'yansu, ga soyayya da kuma girmamawa, yana a matsayin bukatuwar tsiro ne ga hasken rana.....kuma sakon Musulunci ya zo ne saboda soyayya da kuma girmamawa, sannan kuma a kan wannan asasi ne ya gina rayuwa.....

Rayuwar mutum takan girma da kuma cika ne ta hanyar so da kuma girmamawa.....sannan kuma ta hanyar kiyayya da kuma ha'inci, mutumcin mutum yakan zube da kuma mayar da shi abin kyama.

Don haka ne Manzon Allah (s.a.w.a.) ya bayyana cewa soyayya ita ce hakikanin Musulunci. An ruwaito daga gare shi (s.a.w.a) yana cewa: "......shin akwai wani abu a addini in banda soyayya".

A saboda wannan asasi, an kwadaitar da iyaye a kan son 'ya'yansu da kuma kula da su, hakanan su ma 'ya'yan an kwadaitar da su a kan so da kuma


yin da'a wa iyayensu, bugu da kari kan kyautata musu.....

Alkur'ani mai girma ya jaddada karamar dan'-Adam da kuma wajibcin girmama mutumcinsa, inda yake cewa:

"Kuma lalle ne Mun girmama 'yan'Adam, kuma Muka kauke su a cikin kasa da teku, kuma Muka arzurta su daga abubuwa masu dadi, kuma Muka fifita su a kan masu yawa daga wadanda Muka halitta, fifitawa". (Surar Isra, 17:70)

Sannan kuma a wani gurin ya kirayi 'ya'yaye zuwa ga so da kuma girmama iyayensu, cikin fadinSa Madaukakin Sarki cewa:

"......kada ka ce musu tir, kuma kada ka tsawace su......". (Surar Isra': 17:23)

".....kuma ka ce: Ya Ubangiji! Ka yi musu raha-ma, kamar yadda suka yi renona, ina karami".(Surar Isra', 17: 24)

".....kuma ka abuce su a duniya gwargwadon shari'a.......". (Surar Lukman, 31: 15)

A cikin wani hadisin na daban an kirayi 'ya'yaye zuwa ga so da kuma girmama iyayensu, sannan kuma ya bayyana hakan a matsayin ibada. Manzon

Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Kallon da ga iyayensa cikin soyayya, ibada ce".

Sannan kuma yana cewa: "Allah Zai yi rahama ga bawan da ke nuna tsananin kauna ga dansa"[1].

Hakika 'ya'yaye za su iya alaka da iyayensu yadda ya dace ne idan har suka fahimci falaloli da kuma gudummawar da iyayensu suka bayar wajen girma da kuma tarbiyyarsu, bugu da kari kan so da kaunar da suke nuna musu......

Alkur'ani mai girma yana tabbatar da wannan lamari ga dan'Adam yayin da yake tabbatar da alaka a kan asasin fahimtar falala. Allah Ta'ala Yana cewa:

".....(Muka ce masa) ka gode miNi da kuma mahaifanka biyu. Makoma kawai zuwa gare Ni kawai take". (Surar Lukman, 31:14)

Lalle godiya ga wanda ya kyautata wa mutum, yarda da girmansa da kuma mayar da mai kyau gare shi.....suna daga cikin halaye madaukaka. Alkur'ani mai girma yana tabbatar da hakan, cikin fadinSa Madaukakin Sarki cewa:

"Shin, kyautatawa na da wani sakamako? (A'aha) face kyautatawa". (Surar Rahman, 55:60)

A duk lokacin da wannan ka'ida ta - kyautatawa a matsayin sakamakon kyautatawa - ta samu wajen zama a zukatan 'ya'yaye, za su ji cewa lalle fa iyayensu suna bin su bashin girmamawa da kuma da'a hatta ma cikin abubuwan da su iyayen suka gaza ko kuma suka bata rai dominsa, don kuwa babban abin da ya sa su hakan shi ne kaunar da suke wa 'ya'yayen nasu. Ba wai sun yi hakan don rashin girmama 'ya'yan nasu ba ne ko kuma don takura masu, face dai uba yana gudanar da aikin da ya hau kansa dangane da 'ya'yansane.

Don haka ya zama dole ga 'ya'yaye su gabatar da wajibinsu na faranta wa iyayensu rai.....

Haka nan kuma kamar yadda ake samun kulluwar alaka tsakanin iyaye da 'ya'yansu bisa asasin so da kuma girmamawa, haka kuma ake samun alaka ta abin duniya tsakaninsu.....don kuwa 'ya'yaye sukan dogara dungurungum a kan iyayensu a bangaren rayuwarsu ta duniya, hatta ma wajen kammala karatunsu da kuma shiga cikin jami'a. A daidai wannan lokaci yara sukan ji suna da alaka ta ruhi da kuma ta abin duniya a tsakaninsu da iyayensu.

Ko da yake a wasu lokuta wannan alaka ta kan yi tsami saboda matsalar abin duniya.....saboda gorin da wasu iyaye suke wa 'ya'yayen nasu, ko kuma saboda almubazzarancin da wasu yaran suke yi da kuma rashin lura da irin yanayin da iyayensu suke ciki, ko kuma saboda ci gaba da dogaro da iyaye da wasu yara suke yi duk kuwa da cewa suna da karfin yin aiki.....

Nauyin magance irin wannan matsala tana hannun dukkan bangarorin biyu ne.....nauyin kula da yanayin da iyaye suke ciki na abin duniya yana hannu yara ne, sai kuma nauyin kula da kuma kyautata dabi'a, kusanto da yara zuwa ga alheri dakuma nesantar gori da kuma cutar da su yana wuyan iyaye ne.

Babu shakka, jin 'yanci da kuma rashin dogaro ga iyaye hakki ne na 'ya'ya.....don kuwa dan'Adam shi yake cika yanayinsa da kuma girma lokacin balaga, lokacin da ya zama mukallafi. A lokacin da ya balaga ne yake samun 'yancin dogaro da kansa da barin dogaro da iyaye. To amma duk da haka zai saura yana bukatuwa da shiryarwa, nasiha da kuma shawara har lokacin da dan'Adamtakarsa ta cika cif kana kuma ya sami cikakkiyar ilimi na rayuwa, kamar yadda a wasu lokuta yakan ci gaba da bukatuwa da dogaro da kuma kula irin ta abin duniya da kuma zamantakewa daga iyaye har lokacin da ya samu daman dogaro da kansa......

Hakika kashe kudade kamar yadda ya kamata daga bangaren 'ya'yaye yana nuni da kamalar dan'Adamtakarsu, kubutar yanayinsu da kuma girmama kokarin iyayensu.

Shari'a bata tilasta wa iyaye ciyar da 'ya'yansu bayan isa shekarar balaga ba, to amma sai alaka irinta tausayawa da kuma kauna dake tsakani da kuma burin da suke da shi na ganin 'ya'yayen nasu sun yi nasara a rayuwa, yakan sa sukan ci gaba da ciyar da su har zuwa lokacin da suka kai karfin iya rike kansu......

Hakika alaka da kuma kula da iyaye alaka ce ta samuwa, dabi'a da ibada kuma abin tambaye ce gaba ga Allah Madaukakin Sarki, halittu da kuma al'umma gaba daya.

'Ya'yaye suna da wasu hakkoki a kan iyayensu, kamar yadda kuma iyaye suke da su a kan 'ya'yayensu. Hakkin iyaye yakan dada girma da kuma kara muhimmantuwa lokacin da suka tsufa ko kuma suka rasa karfin yin aiki da kuma kula da lamurransu.....don haka a irin wannan hali, muhim-mancin kyautatawa da kuma yi musu da'a yakan karu sosai.....

Sassauta magana, kalmomin girmamawa, murmushi da sake fuska yayin magana da iyaye, yakan sa mutum ya sami girma, daukaka da kuma yardar Allah Madaukakin Sarki. Ba ya daga cikin dabi'u na kwarai da kuma girmamawa, yaro ya dinga daga sauti da tsawa wa iyayensa, ko kuma nuna bacin ransa a fili a gare su da dai sauran nau'in rashin da'a a gabansu..... ".....kada ka ce musu tir, kuma kada ka tsawace su.." "kuma ka fada musu magana mai karimci".......

Dole mu san cewa komai irin girman soyayya da kuma kaunar da 'ya'yaye suka nuna wa iyayensu, to fa zuciyar iyaye tafi tasu buduwa a kan soyayya da kuma tausayawa gare su.

Fahimta Da Kuma Magance Matsalolin Iyali

Kamar yadda iyali ya zamanto matattaran so da kuma hadin guiwa, haka kuma cibiya ce ta tarbiyya da kuma koyarwa.....don kuwa fahimtar juna tsakanin iyaye da 'ya'yayensu lamari ne mai muhimmancin gaske a tsakaninsu, bugu da kari kan magance matsalolin da ka iya tasowa a tsakaninsu......

Don yaro shi ma yana da nasa tunani da kuma mahanga wacce ta kebanta da karatunsa, aiki, tafiye-tafiye, alakarsa da abokansa da dai sauransu. Ta haka ne yake samun haifar da wasu tunanunnuka da ra'ayoyi, don haka yana daga cikin hakkinsa a kan iyaye da kuma sauran 'yan'uwansa da su bude zukatansu da hankulansu don sauraran abin da ke cikin ransa da kuma ba da muhimmanci gare shi.....

Sannan kuma yana daga cikin hakkokin yaro ya gabatar da wadannan abubuwa ga iyayensa, ko kuma wasu 'yan'uwansa daga dangi don jin ra'ayoyi da kuma shawarwarinsu kan wannan bayani nasa don sanin abin yi.....

Lalle yana da muhimmancin gaske 'yan gida daya su dinga zama don tattauna matsalolin da ya shafi daya daga cikinsu, musamman ma 'ya'yaye, don kuwa hakan yakan haifar da girmama 'ya'yayen da kuma basu muhimmanci ga ra'ayoyi da kuma matsalolinsu, bugu da kari kan haifar da wani hali na kulawa da gobensu, dabi'u da kuma matsalolinsu.....

Hakika tattaunawa da kuma jidali yana da wasu dabi'u nasa na daban da suka kebanta da shi kawai, kuma kiyaye su yana nuni da irin lafiya da kuma wayewar shi wannan mutum ne. Matukar dai aka kula da wadannan dabi'u, to ana iya fahimtar juna da kuma isa ga sakamako mai kyau da inganci.

A duk lokacin da aka samu jidali (kace-nace) da kuma tsayawa a kan ra'ayi ko da kuwa kuskure ne, ko aka samu nuna fushi, to da wuya a sami fahimtar juna ko kuma a isa zuwa ga natija da kuma yarda da ra'ayin da aka kawo.

Fahimtar juna kuwa tana bukatuwa da fayyacewa da kuma cikakken bayani kan lamarin da ake tattaunawa a kansa da kuma sauraron ra'ayin sauran mutane, bugu da kari kan yarda da ra'ayin wani matukar dai daidai ne da kuma sauka daga ra'ayi don cim ma maslahar da tafi dacewa. A duk lokacin da aka samar da yanayi mai kyau na fahimtar juna, to ana iya magance matsalar da ake fuskanta, ko kuma za a iya bayyanar da abin da yafi zama ingantacce. Dole ne kuma a bar duk wani abin da ba gaskiya ba ne kuma mai cutarwa.

Alaka Tare Da 'Yan' uwantaka

Hakika alaka ta 'yan'uwantaka da ke tsakanin 'ya'yaye tana tsayuwa ne a kan asasin dangantaka da akida da kuma rayuwa a karkashin inuwar iyaye da kuma gida guda.....don haka ne ta zamanto karfafaffiyar alaka. Hakan kuma yana nuni da fahimtar ma'anar 'yan'uwantaka da 'yan'uwan suka yi ne da kuma irin girman kyawawan dabi'un da suke da shi.

'Yan'uwa da suke raye a gida guda sun kasu kashi-kashi a bangaren shekaru da kuma jinsi (mata da maza), haka nan kuma a bangaren wayewa da kuma tunani.....sannan da kuma yanayin lafiya, iyawa da kuma kwarewa ta zati.

Lalle babu makawa rayuwa waje guda a matsayin dangi tana bukatarsu da su kasance abu guda.....hakan kuwa yakan samu ne kawai ta hanyar soyayya, sadaukarwa, gaisuwa, kyauta, girmama juna, taimakekkeniya, cin abinci waje guda da kuma fahimtar juna ta hanyar maganganun soyayya da kauna......bugu da kari kuma kan afuwa da kuma yafewa a duk lokacin da aka sami bulluwar wata matsala a tsakaninsu.....
Hakika aikin da ke tabbatar da soyayya da kuma hadin kai cikin harkokin yau da kullum tsakanin 'yan'uwa shi ne sallama da kuma gaisuwa..... gaisu-wa ita ce mabudin zukata; don kuwa tana nuni da so, girmamawa da alaka ta soyayya ne.....sannan kuma tana shafe abin da ke cikin zuciya na daga rashin fahimta, cutarwa da kuma rashin yarda.....

Babu shakka, yawaita gaisuwa tsakanin mutanen gida guda (iyali) yakan karfafa soyayya da kuma girmamawa. Don saboda muhimmancin da gaisuwa take da shi ne wajen alakar mutane, ya sa Manzon Allah (s.a.w.a.) yake kwadaitar da mu fara sallama da kuma yin gaisuwa; don ita hanya ce zuwa ga zuciya...kana kuma kalma ce da take shuka so da kauna a cikin zukata.

Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Ba za ku shiga aljanna ba har sai kun so junanku, ba za ku so juna ba har sai kun yi imani. Ashe ba zan shiryar da ku zuwa ga wani abin da idan kuka aikata shi za ku so juna ba, ku karfafa sallama a tsakaninku".

Sannan kuma Manzon Allah (s.a.w.a.) yana koyar da mu ladubban gaisuwa, inda yake cewa:

"Mafificinku shi ne wanda ya fara gaida (sallama) dan'uwansa".

Kwaryar abincin da iyaye da 'yan'uwa suka kewaye ta don ci daga cikinta, lalle ta kasance kwarya ce ta hadin kai da kuma tabbatarwa cikin rayuwa. Don kuwa a lokacin da suke cin abincin, za su dinga maganganu na soyayya a tsakaninsu, kai za su ma dinga tattauna matsalolin da suke fuskanta ta hanyar raha da kuma farin ciki.....

Lamarin ba wai kawai cin abinci ne ba, face dai musharaka ne cikin soyayya da kuma zumunta.....

Hadin guiwa da kuma taimakekkeniya tsakanin 'yan gida guda yana daga cikin muhimman abubuwan da suke tabbatar da sa'ada, haduwa da kuma jawo rahamar Ubangiji da kuma ta jama'a.....

Mai yiwuwa ne wasu daga cikin 'yan'uwa su kasance sun fi sauran ci gaba a bangaren karatu, don haka yana daga cikin hakkin dan'uwa a kan dan'uwansa da ya taimaka masa kan wasu darussansa ko kuma aikin da ya sa a gaba, da suka hada da zane, dinki, koyan ilimin komfuta da dai sauransu, ko kuma ya taimaka masa kan yadda zai magance matsaloli da wahalhalun da yake fuskanta......

Hakan yakan taimaka wa dan'uwa wajen tsaga tafarkin rayuwarsa, da kuma sanya shi ya zamanto cikin shirin taimaka ma dan'uwansa da ya taimake shi a wasu bangarori na daban.

Sannnan kuma mai yiwuwa ne daya daga cikin 'yan'uwa ya kasance ya sami damar samun aiki, da kuma kai wa ga wani matsayi, alhali kuwa dan'uwansa yana nan yana bukatuwa da taimakon kudi, to yana daga cikin hakkin 'yan'uwantaka da kuma kyautatawar da Allah Yake so, da ya taimaka wa 'yan'uwansa ya saukake musu wahalhalu da su da iyayensa, don su ma su yi tunanin taimaka masa a duk lokacin da ya bukaci taimakonsu...

Rayuwa cikin dangi da gida guda, rayuwa ce ta kauna, soyayya, sadaukarwa da kuma taimakekke-niya, kuma hakan yana tabbatuwa ne ta hanyar maganganu da kuma mu'amala mai kyau, kudi da kuma taimakekkeniya a sauran bangarori na rayuwa.....

Daya daga cikin hanyoyin guje wa matsaloli ita ce nesantar cutar da sauran mutane da kuma damunsu, musamman ma idan yana cikin halin bacin rai da damuwa saboda matsalolin da yake ciki.

Mai yiwuwa ne a samu wasu daga cikin yaran gida su kasance masu fushi da kunci rai ta yadda za su dinga samun matsala da sauran 'yan'uwansu, ko kuma hakan ya haifar da wani tunanin da bai dace ba dangane da su, ko kuma yana iya fada musu kalmomi masu zafi ko kuma ya aikata musu wani abu da zai sosa musu rai.....ko kuma mai yiwuwa ne sauran 'yan'uwan nasu su ma su mayar musu da martani da nuna musu irin wannan hali da suke nunawa. Ta haka sai a samu barkewar rikici a tsakanin 'yan'uwa da kuma dangi......

To a lokacin da irin wannan hali ya faru, dole a yi la'akari da irin halin da su wadannan 'yan'uwa na farko suke ciki, a kula da wannan matsala cikin kwanciyar hankali kana kuma cikin ruwan sanyi. Sannan daga baya, sai a tattauna wannan matsala da su gaba daya, ko kuma ta hanyar daya daga cikin iyaye, ko dan'uwa, ko aboki don kawo karshenta.....

Hakika afuwa, yafewa da kuma samun galaba a kan fushi, wani yanayi ne da ke nuni da karfin halin mai shi da kuma kubutarsa daga hassada, kiyayya da kuma bakin ciki. Alkur'ani mai girma ya yabi masu kame fushi da kuma yafewa mutane, kana kuma ya bayyana shi a matsayin kyautatawa da kuma tausayawa, Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:

"Wadanda suke ciyarwa a cikin sauki da tsanani, kuma suke masu hadiyewar fushi, kuma masu yafe wa mutane laifi. Kuma Allah Yana son masu kyautatawa". (Surar Al'Imrana, 3:134)

Haka nan ma kyauta takan tabbatar da soyayya da kuma fadada alaka tsakanin 'yan'uwa, don kuwa kyauta tana nuni da irin yadda mutum yake ji ne dangane da dan'uwansa. Kamar yadda kuma take nuni da kulawa, girmamawa da kuma rigegeniya cikin soyayya. Don haka ne ma Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ke cewa: "Ku yi kyauta, ku so junanku (soyayyarku ta karu)".

Don kyautar da ka yi da wani littafin da ya dace, misali, ko kuma abin sa hotuna, ko kuma agogo da dai sauransu ga 'yar'uwa ko kuma dan'uwanka ba makawa za ta bar wani tasiri a zuciyarsa/ta......

Dan'Adam halitta ce ma'abuciya magana, kuma ta hanyar maganar ce yake iya bayyanar da abin da yake damunsa. Sannan kuma tattaunawa irin ta iyali tana da nata tasirin. Don kuwa a lokacin da 'yan gida guda suka hadu suna tattaunawa ta soyayya, ko kuma kan wani lamari na wayewa, ko kuma na siyasa, ko kuma kan sha'anin da ya shafe gidan nasu, hakan yana taimakawa wajen dada musu wayewa da kuma masaniyya. Sannan kuma hakan zai sanya su kasance sun san matsalolin junansu da kuma damuwa da matsalolin al'ummar da suke cikinta. Bugu da kari kuma hakan zai magance musu zaman kadaitaka da kuma damuwa. Kamar yadda kuma wadannan maganganu zasu taimaka musu wajen hadin kai da kuma kusantar juna ta bangarori daban-daban na rayuwa a tsakaninsu.....

Don haka ka yi kokari ka fara tattaunawa da sauran 'yan'uwanka a yanayi na jama'a, ko kuma ka bijiro da tambayoyi kan wasu mas'aloli ga 'yan'uwanka da kuke zaune da su: mahaifiya da mahaifi..... don samar da yanayin da zai sa a fara tattaunawa irin ta iyali......

Sai dai kuma magana da kuma tattaunawa ma suna da nasu asasi da kuma ladubba, ba ya inganta mutum ka katse masu magana har sai ya gama maganar tasa, kada kuma ka mamaye magana ga kanka kawai, ka tantance maganganu da labaran da kake bayarwa kafin ka bayar da su. Don hakan yana bayyanar da girmanka da kuma maganar da kake fadi.

Tsari Cikin Iyali

Iyali cibiya ce daga cikin cibiyoyin zamantake-wa, don haka rayuwa cikinta yana bukatuwa da tsari, don tsara ayyuka da kuma alakokin mutanen da suke cikinta. Ita cibiya ce da ke da ayyuka daban-daban, da suka hada da na tarbiyya, tattalin arziki, zamantakewa, tsarin gudanar da mulki da dai sauransu.

Babu shakka tsari cikin iyali yana da nasa tasirin mai girman gaske wajen tsara rayuwa a cikinsa. Daga cikin tsare-tsaren iyali akwai ikon iya rayuwa a cikinsa, hakan yana da tasiri ta bangare mai kyau da mara kyau, sannan kuma gudanar da hakan yana kan iyaye ne.....

Don kuwa a duk lokacin da aka sami kulawa da kuma gudanar da sha'anin iyali kamar yadda ya dace, misali kyakkyawan yanayin gudanar da kudade, tarbiyyar yara da kuma shiryar da su, amfani da lokaci, tsara lokutan barci, farkawa da kuma cin abinci, magance matsaloli da dai sauransu, to ana iya samar da kyakkyawan tsari a cikin iyali. Kuma hakan zai tabbatar da tasirinsa cikin rayuwar mutanen wannan iyali, sannan kuma ya tafiyar da rayuwar iyalin kamar yadda ya dace.

Samar da kasafin kudi ga iyali, zai tsara irin kashe kudin da iyalin za su dinga yi gwargwadon karfin iyalin, ba tare da almubazzaranci ba. Hakika matsalar samar da kasafin kudi, matsala ce mai girman gaske da zata taimaki iyalai gudanar da rayuwa kamar yadda ya dace. Kuma kasafin kudin zai tsara yanayin kashe kudaden iyali gwargwadon bukatun iyalin, da suka hada da abinci, tufafi, ilimi, ajiye wani sashi na abubuwan bukata saboda bacin rana da dai sauransu.

To amma fa takurawa iyali ta hanyar hana su abubuwan bukatuwansu na yau da kullum duk kuwa da kasantuwan akwai daman yin hakan babban kuskure ne kuma tauye musu hakki ne, kamar yadda kuma almubazzaranci da kuma kashe kudi a abubuwan da ba su dace ba yake cutar da yanayin iyali. Mai yiwuwa ma ya kai ga matsayin haramci, idan har abin ya yi yawa ko kuma ya zama almubazzarancin.....

Sannan kuma za mu kara ganin munin hakan ne da kuma yin nadama, a lokacin da muka ga muna bukatar wadannan abubuwa da muka riga muka lalata su kana kuma ba mu da halin samunsu ko kuma sai mun koma muna rokon wadansu, to hakan zai sanya mu cikin jin kunya da kuma yarda da fifikon wasu a kanmu. A wasu lokuta mukan gagara samun kudaden da muke bukata, don haka sai mu shiga cikin damuwa da kuma nadama da dai sauransu.....

Hakika Alkur'ani mai girma ya sanya mana ka'ida mai kyau wacce za ta tabbatar mana da kasafin kudin da ya dace, cikin fadinSa cewa:

" Kuma kada ka sanya hannunka kuntacce zuwa ga wuyanka, kuma kada ka shimfida shi dukkan shimfidawa, har ka zama abin zargi, wanda ake yankewa[2] ". (Surar Isra', 17: 29)

Mai yiwuwa ne a wannan hali (na kuruciya) da muke ciki, wani daga cikinmu ya gagara fahimtar kimar kudi da kuma muhimmancinsa, to amma kuwa ba makawa za mu yi nadama bayan mun yi wasa da kuma lalata abin da ke hannunmu. Hakika iyayen da suke matse hannuwansu da kuma hana iyalansu amfani da kudade da kuma biya musu bukatunsu na wajibi, hakan wasa ne da kuma tauye hakkokin iyalansu. A irin wannan hali abin da ya hau kan 'ya'yaye shi ne kokari wajen fahimtar da su lamarin cikin ladabi.....sannan a duk lokacin da suke bukatuwa da kudi, kuma iyayen nasu suka ki taimaka musu, to babu makawa su nemi wani aikin da zai magance musu wannan matsala.....

Neman aikin yi mataki ne mai kyaun gaske da ke nuni da fahimta da kuma wayewar mutum da kuma karfinsa wajen gudanar da ayyukan da suka shafe shi. Koma dai mene ne ba ya kamata matsalar kudi ta kasance matsalar da za ta raba iyaye da 'ya'yayensu.

Daga muhimman matsaloli cikin matsalar tsarin iyali ita ce matsalar tsara lokaci.....don kuwa da yawa daga cikin iyalai ba sa ba da muhimmanci ga wannan lamari.....

Don haka ake samun kasala da gajiyawa daga wasu daga cikin iyalan.....misali sai ka ga ba sa tashi da wuri da safe sai bayan rana ta fito, ko kuma a yi ta bata lokaci da tadi da maganganu, ko kuma kallon talibijin.....hakan kuwa yakan cutar da yanayin karatun yaran gidan, ko kuma ruhin kokari da kuma aiki. Hakika wannan dabi'a ce wacce ba ta da kyau, dole ne a guje mata.....

Samuwar tsarin da ya dace a cikin iyali ya dogara ta bangarori da dama kan yadda ake amfani da lokaci, kamar yin barci da wuri, tashi da wuri, amfani da lokaci wajen karatu da bincike, ayyukan hannu, zane-zane da dinke-dinke, koyon aiki da wasu na'urori da dai sauransu......

Hakika kula da aiki da kuma kokari wajen gujewa kasala ya kan tarbiyyantar da yara koyon wannan kyakkyawar dabi'a, ta yadda su ma za su koyi wannan siffa ta kokari da kuma aiki tukuru.

Alakar Iyali Da Sauran Mutane

Iyali a yanayinsa na zamantakewa sashi ne na al'umma, kana kuma al'umma a dabi'arta ta kumshi iyalai ne da kuma mutane daban-daban.....sannan kuma alaka ta zamantakewa lamari ne mai muhimmanci gaske cikin rayuwar iyali. Don kuwa dole ne mutanen wani gida su kasance suna da alaka da sauran iyalai, musamman ma dangi, makusanta da kuma makwabta.

Don haka ingantacciyar iyali ma'abuciyar nasara ita ce wacce take da alakoki na abokantaka da sanayya da sauran iyalai. Kuma dole ne ya kasance akwai alaka ta soyayya da kuma yarda a tsakanin iyalanmu.

Hakika ziyarar juna da kuma kasancewa cikin bukukuwan farin ciki, kamar ranar salla, daren watan Ramalana, aure, nasara a jarrabawa, ko kuma na bakin ciki, ko kuma yayin faruwar wata matsala, ko kuma lokacin rashin lafiya, wajibi ne da ke nuna irin ingantaccen matsayin iyali. Hakan kuwa aiki ne da Allah Madaukakin Sarki Yake sonsa kuma Yake ba da sakamako saboda shi.....
Don kuwa sa da zumunta yana daga cikin ayyukan da Alkur'ani mai girma ya koyar da shi, kana kuma dokokin Musulunci sun bayyana yanke zumunta a matsayin babban zunubi. Don haka sa da zumunta yana daga cikin mafifitan ayyuka.....

Baya da haka kuma sa da zumunci yakan kore bala'i, kara arziki, samar da soyayya da kuma hadin kai tsakanin al'umma, yakan sanya mayar da abu mai kyau da kuma tsayawa a gefen iyali a duk lokacin da take cikin wata matsala, kamar yadda kuma zai sanya kasancewa tare da iyalin cikin lokutan farin ciki ko kuma bakin ciki.....

Hakan kuwa ita ce rayuwar al'umma.....soyayya da taimakekkeniya, kasacewa da jiki da ruhi yayin farin ciki ko bakin ciki.....

Hakika duk iyalin da take raye ita kadai ba tare da sanya kanta cikin al'umma ba, ita ce iyali maras nasara a al'ummance. Babu wani bambanci kan hakan, shin wannan kadaitaka saboda ji-ji da kai ne na dukiya ko kuma na mukami da kuma son doruwa a kan sauran mutane, ko kuma saboda dabi'ar kin mutane.....

Dukkan wadannan munanan siffofi sukan zubar da mutumcin wannan iyali, da kuma tarbiyyantar da yara marasa nasara a idon al'umma da kuma samun
girmamawarsu. Lalle babu wani mutum da ya wadatu daga taimakon sauran al'umma cikin 'yan'Adam.

Sannan kuma ba ya kamata ga iyalin 'yan'uwa ko kuma kawunnai da goggoni da dai sauransu su kirkiro gaba da kiyayya a tsakaninsu saboda faruwar wata matsala, face dai dole ne su yi aiki wajen ganin an kawo karshenta da kuma magance ta ta hanyoyin da suka dace.

Daga cikin hanyoyin da suke magance irin wadannan matsaloli akwai ziyarce-ziyarce, afuwa da mance sababin matsalar, kira zuwa ga cin abinci tare, tafiye-tafiye na iyali gaba daya, aike da wasidu da kuma katuttukan gaisuwa da kuma sadar da gaisuwa ta hanyar tarho idan har tsakanin iyalan akwai nisa da dai sauransu. Don haka dole mu fahimci rayuwar al'umma a matsayin rayuwa ce ta cude-ni-in-cude-ka. Alkur'ani mai girma ya bayyana haka cikin fadin Allah Madaukakin sarki cewa:

"Ya ku mutane! Lalle ne Mu, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangogi da kabiloli domin ku san juna. Lalle mafificinku daraja a wurin Allah shi ne wanda yake mafificinku a takawa......" (Surar Hujurat, 49: 13)

" Kuma ku taimaki juna a kan aikin kwarai da takawa. Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zalunci....."(Surar Ma'ida, 5: 2)

"Kuma ma'abuta zumunta, sashensu ne waliyyan sashe a cikin Littafin Allah" (Surar Anfal, 8: 75)

Sannan kuma Manzon Allah (s.a.w.a.) ya bayyana sakon Musulunci a matsayin so na gaskiya, inda ya ke cewa:

"Shin akwai wani abu a addini in ban da soyayya"...kana kuma mafi alherin mutane shi ne wanda yafi kowa kyautatawa ga iyalinsa, kamar yadda yazo cikin fadinsa (s.a.w.a) cewa: "Mafi alheri daga cikinku shi ne wanda ya fi kyautatawa ga iyalinsa, kuma ni ne na fi ku kyautatawa ga iyalaina".

Da haka ne muke iya fahimtar cewa iyalai su ne suke gina mutumcin 'ya'yayensu kana kuma 'ya'yayen nasu suna kamanta mutumcin iyayen nasu ne. Sannan kuma kyakkyawar iyali tana haifar da 'ya'yaye na kwarai.

Allah ya sa mu dace amin.


[1] Usul al-Kafi na Kulaini, shafi na 50.

[2] Wato kada ka zama marowaci a zarge ka, kuma kada ka zama almubazzari ka rasa mutane, su yanke daga gare ka.