Annabin Allah Muhammad (s.a.a.w)

Duniya kafin manzo.

n tayar da AnnaAbi Musa a.s a matsayin Annabi don ya shiryar da mutane zuwa ga ibadar Allah makadaici, sannan yana umurtarsu zuwa ga adalci don ya tseratar da su daga zaluncin fir'aunoni da dagutai. Sai ya zo musu da Attaura  wadda a cikinta akwai dukkan hukunce-hukucne a garesu.

  Bayan tafiyar Musa a.s zuwa ga Ubangijinsa, sai malamam yahudawa suka fara canza zancen Allah madaukaki. Suka cigaba da fassara maganar Allah da manufofinsu musamman akan abin da ya shafi maganar Annabin Allah Isa (a.s) wanda ya yi musu bushara da shi cewa annabi zai zo bayansa kuma sunansa Isa.

  Lokacin da Allah ya tayar da Annabi Isa (a.s) don tsarkake  zukatan mutane da dasa soyayya a tsakaninsu a karkashin inwar akida ta tauhidi, sannan ya yi bushara da Annabin da zai zo bayansa wanda sunansa Ahmad. Sai wasu daga cikin yahudawa suka shiga wani addini daban wanda aka canza kamar yadda suka yi wa addinin musa kafinsa. Don haka ba su bi wasiyyar manzonsu ba wato Isa a.s.

 Haka Dan Adam ya rayu a cikin kwazazzabai  a cikin matakan rayuwarsa. Don haka ne zalunci da barna suka sugabanci al'umma,

kuma mutane suka koma bautar Gumaka da shirka da Allah madauka, suka wayi gari suna rayuwa a cikin canfi da kirkire-kirkire.

 Yankin Larabawa a wancan lokaci ya kasance   karkashin  tsari na kabilanci ke shugabantarsu, suma sun kasance suna rayuwa a cikin duhun zalunci , dimuwa da yake-yake.

DA MAIALBARKA

Bayan duhun zalunci da bata da ya bai baye wannan yanki na larabawa da dukkan duniya baki daya, a shekara ta 570 bayan haihuwar Annabi Isa a.s. sai a ka haifi  Manzon tsira Muhammad (s.a.a.w)a shekarar da ake cewa shekarar giwa  bayan kusan wata daya da kawao harin da Abarhata ya yi wa Ka'aba.

Babansa (s.a.a.w) wato Abdullah ya kasance yana kasuwanci tsakanin Makka da sham, wata rana ya yi tafiya zuwa Sham domin kasuwanci kamar yadda ya saba sai ajali ya riske sa ya yi wafati a bisa hanya  don haka Manzo bai sami ganin mahaifinsa domin kuwa yana ciki ne ya yi wafati.

 Kamar yadda ya ksance a wancan zamani al'adar larabawa sukan kai 'ya'yansu ne kauye domin a shayar da su, domin su koyi jarunta da fasahar harshe. Shima manzo mai daraja an kai sa ne wajen wata mata mai suna Halimatus-sa'adiyya domin ta shayar da shi. Mijin Halima ya yi mata  ishara da  cewa ta shayar da shi wata kila albarkacinsa albarka ta mamaye gidansu kasancewarsa maraya. Haka kuwa aka yi sakamakon shayarwar da ta  yi masa albarka ta mamaye gidan na su. Haka karamomi Manzo kulum suke bayyana har Halima da mijinta  suka so manzo ya tsaya ya cigaba da rayuwa a gidansu.

Yayin da manzo maigirma ya cika shekara biyar sai aka maida shi zuwa ga mahaifiyarsa wat o Amina a.s. domin ta cigaba da renonsa kamar yadda ya kamata. Ta kasance ta kaisa wajen 'yan uwanta dake Madina don su ganshi, a bisa hanyarta ne fa ta dawowa Allah ya yi ikon nasa, sakamakon wata gajeruwar rishin lafiya ta yi wafati, aka rufe ta a wani wuri da ake cewa Abwa'a wanda yake tsakanin

Makka da Madina,  a wannan lokaci sai Ummu Aimana Baiwar Mahaifiyarsa ta maido da shi zuwa ga Kakansa Abdulmadallib.

AbdulMadallib kakan Manzo ya cigaba da rainonsa  cikin kula da tattashi na musamman har zuwa lokacin da Manzo ya kai dan shekara takwas, a wannan lokaci ne kuma kakansa mai kula da shi wanda yake matsayin uwa da uba ga manzo shima ya riga mu gian gaskiya. Daga nan ne fa Baffansa wato Abu dalib Mahaifin  Imam Ali a.s ya dauki nauyin kula da manzon tsira kamar yadda yake kula da'ya'yansa na cikinsa, harma an ce ya fi kula da manzo fiye da 'ya'yansa. Abudalib ya kara kula da  manzo sosai a lokaci da bahira wani malamin yahudawa ya gaya masa cewa lallai ka kula da  wannan yaro domin shi ne Annabin wannan al'umma kamar yadda a aka fada a cikin Attaura da injil.

  Lokacin da manzo ya kai  matsayin matashi dukkan mutanen Makka sun kasance sun aminta da shi saboda kasancewarsa mutum mai halaye nakwarai wanda ake so kowane mutum ya siffanta da su. Duk da kasancewarsa karamin yaro a tsakanin manya-manyan mutanen Makka amma sun kasance suna aminta da maganar da ya yi fiye da sauran mutane manyan-manyan makka. Manzo ya kasance tun wancan lokaci yana taimakon wadan da aka zalunta da raunana.

Alamomin Annabta:

Sayyida khadija ta kasance  mata ce mai girma da daukaka a cikin garin makka, ta samu labarin halayen kwarai na manzo s.a.a.w don haka ne ta bukaci da zai yarda ya zo su rika kasuwanci kamar yadda ta saba yi da sauran mutane, takan aika su zuwa Sham domin su yo mata fatauci. Sai kau manzo ya karba     neman da ta yi masa kuma ya tafi Sham domin kasuwanci. Kuma cikin yardar Ubangiji  a ka samu riba mai yawa  a wannan kasuwanci wadda ta rubanya wadda ake samu daga waninsa. Sayyida khaja ta ji dadin wannan al'amari kwarai da gaske, wanda daga karshe abin ya kai ta nemi manzo da ya zama mijinta kuma ya aminta da hakan. Lokacin  manzo maigirma da daukaka ya auri khadi ta kasance tana 'yar shekara arba'in kamar yadda tarihi ya nuna. Kuma Sayyida khadija ta haifar wa manzo 'ya'yaye da dama kuma maza da mata kamar haka:

Kasim, Ibarahim, Zainab Rukayya, Ummu kulthum, Abdullah da Fatima Azzahra a.s. wadda kuma ita kadai ce ta rayu kuma ta hanyarta ne zuriyar manzo ta yadu a duniya, wanda duk inda kaje a yau cikin duniya sai ka samu zuriyarta mai albarka.

 Bayan manzo ya yi aure  sai matsayinsa fa ya kara daukaka  acikin al'umma kamar yadda yake a al'ada idan mutum ya yi zaka ga ya shiga cikin hidimomin al'umma ba kamar yadda kafin ya yi aure ba.

 Manzo s.a.a.w ya kasance mutanene makka suna girmama sa duk da kasancewarsa matashi mai kananan shekaru a cikinsu, amma sukan yarda da maganarsa kuma ya kan shiga tsakanin mutane yayin wata rigima ko kace na ce tsakanin kabilun garin Makka. Daya daga cikin misalin shi ne lokacin da mutanen Makka zasu sake gina dakin Ka'aba sai kowace kabila tana so ace ita ce ta aza dutsin nan da ake kira da hajrul Aswad a wurinsa. Don haka sai kau rikici ya tashi a tsakaninsu akan hakan. Sai manzo mai girma da daukaka ya zo ya shiga tsakanisu don kada abin ya kai ga yaki domin wani abu ne mai sauki a wajensu a wannan lokaci.sai manzo ya umurcesu  da su kawo wani tufafi mai fadi ta yadda za'a iya aza dutsin a cikinsa, sai ya  umurci kowace kabila da ta kawo wakilinta ya kama gefen tufafin ta yadda zai kasance kowace kabila tana da hannu wajen sa shi wannan dutsi a wuri da ake bukata a maida shi. Haka kuwa aka yi da haka ne kuwa Manzo ya warware wannan matsala a tsakaninsu.

  Saboda amincewar da mutanen Makka suka yi wa  manzo shi ya sa  a wancan lokaci suke kiransa da Amin, wato wanda aka amince ma wa.

 Daga wannan lokaci ne fa almaomin annabta suka fara  bayyana ga manzo, sai fa ya fara yankewa daga mutane da rikice-rikicen kabilun makka, ya na tafiya a kogon hira inda yakan yi wata a wajen yana bautar Allah T.A.

Bayan manzo ya cika shekara arba'in a cikin rayuwarsa, sai Allah madaukaki ya aiko da Mala'ika Jabra'il da sako zuwa ga mazon a matsin Annabin Allah kuma mai shiryar da mutane zuwa ga hanyar Ubangiji. A lokacin ne fa aka saukar wa manzo da surar farko a cikin alkur'ani maigirma wato Suratul alak. Daga nan ne fa muhammad bin Abdullah s.a.a.w ya sake shiga cikin wata sabuwar rayuwa kuma mai wahalar gaske.

Manzo ya fara kiran mutanen Makka:

Manzo s.a.aw. ya fara da kiran matarsa kuma ta amasa da wannan kira da hannu biyu, sannan sai Imam Ali wanda shima a lokacin yana gidansa kuma  yana karamin yaro, a lokacin su ne farkon karbar kiran manzo a ciki tarihin musulunci. Sannan sai ya fara kiran wasu daga waje kuma suka amsa kamar su Abubakar da usmanu da dai sauran sahabbansa na farko, wanda a lokacin  yawan musulmi ya kai yawan mutum arab'in, sai manzo ya zabi gidan Arkam domin ya zama cibiyar da zai rika koyar da muminai kur'ani a wurin. A nan ya zama cibiya ta farko ta musulmi inda suke taruwa suna tattauna mtsalolinsu.

 Daga nan ne fa manzo ya cigaba da kira zuwa ga hanyar Allah, kuma ya fara shiga cikin mtsalolin mutanen makka wadan da  a da suke kiransa da Amin yanzu kuma ya koma sune suke gallaza mas da mabiyansa.

Wannan tsanani fa lokacin da ya yi kamari ya sa dole manzo ya bar garin makka in da ya yi Hijira zuwa garin Yahtrib wanda daga baya ake kiransa da suna Madinatur-rasul wato garin Manzo. Wanna kuwa ya faru ne bayan aiko manzo da shekar goma sha uku. Wato lokacin yana dan shekara 53 a cikin rayuwarsa.

 Bayan manzo fa ya yi hijira zuwa garin madina mutanen Madina kuma suka  karbi manzo da hannu biyu, wannan ne fa ya ba shi damar kafa hukuma a wannan gari a matsayin  cibiyar musulmi. Daga nan ne kuma ya cigaba da kiran mutane a tafarkin Allah wanda sakamkon hakane fa ya yi yakoki daban-daban da makiya Allah da addinin musulunci.

Yakokin manzo:

Bayan manzo ya koma Madina kamar yadda muka fada a baya ya yi yakoki da dama daya daga cikinsu kuwa  shine yakinsa da mutanen makka wan da aka yi sa a wani wuri da ake kira badar. A wannan wuri ne fa aka gabza yaki tsakanin musulmai da mushirikai inda galaba da rinjaye ya kasance a hannun musulmai, inda  suka rusa rundunar makiyya Allah.

 Sannn man zo ya halarci yakin uhd inda musulmi sakamakon kuskure da saba umurnin manzo da suka yi, suka sha wahala a hannun makiya addinin musulunci.

 Haka ma manzo ya halarci yakin khandak wanda shima galaba da nasara ta kasance a hannun muminai. Haka dai manzo ya cigaba da yakoki domin daukaka kalmar Allah T.A har inda ya kai zuwa ga  bude garin Makka wanda aka fi sani  da fathu Makkati inda garin Makka da ikon Ubangiji ya  komo a hannun musulmi.

  Da haka ne dai manzo ya samu damar yada addinin musulci a bangarori da dama na ksashen larabawa awannan lokaci.

Wafatin manzo s.a.a.w.

Bayan manzo ya yi hijira da shekara goma wato yana dan shekara 63 ne fa, bayan ya kafa hukuma da gwammanatin musuulunci sai Allah madaukaki ya karbi rayuwarsa zuwa ga rahamarsa, kuma ya  damka wannan amana a hannun musulmi. Sai dai abin tambaya  a nan shin Musulmi kau sun rike wannan amana maigirma ko kuwa?????????