')
//-->
An haifi Husain a shekara ta 1334 H.S a garin Tehran wato babban birnin Iran. Iyayensa sun kasance masu son addini , wannan ne ya ba shi karfin guiwa wajen dagewa da karatu Kur’ani.
Sautin shehi malamin nan wato abdulbasit shi ne ya sa masa son karatun.Don haka ne tun a lokacin yarintarsa ya fara koyon muryar malamin. Tare da taimakon mahaifinsa kuwa sai ya nutsa a cikin al’amarin. Mahaifinsa shima makarancin kur,ani ne don haka ya cigaba da ba dansa tarbiyya da kwarin guiwa .Husain ya zama daya daga cikin jerin makaranta kwararru. Malamin kamar sauran makaranta ya kasance ya zabi ya yi koyi da yanayin karatun Abdulbasit da na manshawi. Amma daga karshe shima ya samar da yanayi nasa na kansa.malamin ya halarci gasar karatu wurare da dama kuma ya samu lambar yabo maigirma akan hakan.
Misali ya yi na uku a gsar karatu na duniya a maleziya. kuma ya yi na daya a gasar karatu ta duniya a Afrika ta kudu. Sannan ya halarci gasar karatu da dama a cikin gida waato Iran.
Malamin ya yi aure a shekara ta 1360 kuma yanzu yana da yara guda biyu.
Sannan haka nanan malamin ya kware wajen kiran salla tare da murya mai ban sha’awa.
Malamin ya halarci yakin Iran Iraq, sannan ya kasance yana gudar da majlisin karatu a filin dagar, domin karfafa sojojinsu.
Wannan shi ne takaitaccen tarihin malamin. Da fatan Allah ya ya yi masa sakayya akan hidimar da yake yi akan Kur’ani mai girma amin.