Sheikh Abdulbasit

An haifi sheikh Abdul basit shekara ta 1927 wani kauye mai suna Almazar’ia da ke cikin jihar Kana a kudacin Misra . An haifi malamin a wani wuri da ake kula ta musamman akan abin da shafi Kur’ani musamman hardarsa.Kakansa wato malam Abdussamad ya kasance mutunne mai son addini kuma mahardacin kur’ani, masanin ilmin Tajwid.Haka ma kakansa na wajen uwa mutum ne masanin Allah wato Jalil Abu Dawud wanda yake  ya shahara shima akan abin da ya  shafi batun kur’ani. Amma Babansa wato Abdussamad ya kasan malmin hardar Kur’ani.haka shima Dan uwansa wato Mahmud da Abdul hamid sun kasance suma suna karatun ko koyon hardar kur’ani a wata makaranta ta harda sai  aka kawo kanensu wato wato basit lokacin yana dan shekara 6.

 Kasancewar Abdulbasit yaro mai hazaka da himma wajen karatu sai malaminsu wato Sheik Amir ya ba shi kula ta musamman.

 Shehi malamin dakansa yana cewa lokacin da na kai shekara 10 na hardace Kur’ani kuma ya kasance yana gudana daga bakina  kamar  yadda ruwa ke gudana a cikin kogi. Ya cigaba da cewa Babana  ya kasance ma’aikaci a ma’aikatar sufuri. Sannan kakana ya ksance malami sai na nemi shawararsu da su nuna mani hanyar zan koyi karatun kur’ani sai suka umurce ni da in tafi a garin Danda da ke arewacin Misra  da na je na koyi ilimi Kur’ani a wajen Shehin malami Muhmmad salim . Amma kafin in tafi Danda sai muka sami labarin cewa ai malamin wato Muhammd Salim ya zo jiharmu domin ya kafa makarntar kur’ani don ya cigaba da koyar da shi a wajen. Don haka sai na shiga wannan makaranta na cigaba da karatu, inda na hardace wani littafi na kyon kira o’imai suna shadibiyya.

  Kasancewar Abdulbasit mai kwazo, malaminsa ya bashi kulawa ta musamman da nuna shi a wurare da dama, harma akan gayyace shi don gudanar da karatun kur’ani, a lokacin yana dan shekara 12.

Ziyararsa Haramin Sayyida Zainab

A shekara ta 1950 an gabatar da wani taron Maulidin manzo a haramin Sayyida Zainab dake misara. Sai Abdulbasit ya halarci tarn, sai kuwa aka nemi izini daga masu gudanar taron da sub a Abdulbasit dama don ya yi karatun Kur’ani in da manya-manyan malamai makaranta suka halarci taron don karatun kur’ani sai kuwa aka bashi dama da ya gudanar. Lokacin fara karatun ya haifar da wani yanayi na musamman a wajen inda ya kawatar da mahalar taron. An nemi izini ne da ya yi karatun na minti goma amma saboda kawatarwa da ya  yi sai da  kai awa daya yana yi.

Daga nan ne fa ya fara samun shahra a misra. Wanda daga nan aka nemi da ya  zo ya rika karatu a cikin Rediyo, wanda daga farko ya ki, amma dai da mutane suka nuna sha’awarsu da shaukinsu akan ya zo ya yi sai ya karba.Daga nan ne fa malamin ya sami wata irin daukaka in da kowane gida ka je zaka samu kaset  dinsa na  karatu.

    Don haka ne sai ya zabi day a dawo kusa da Kabarin Sayyida Zainab don ya zauna anan ya cigaba da rayuwarsa saboda albarkacinta ne ya samu daukaka..

Tafiye-tafiyensa

Malamin a shekara ta 1952 ya fara tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya don gabatar da karatun kur’ani maigirma. Malamin ya halarci kasashe da dama  acikin rayuwarsa don gabatar da wannan al’amarin.Har wani lokacima ba don ya yi karatu ake gayyatarsa ba, don kawai ya halarci tarurruka don ya kawatar da taron.Ya halarci wata gayyata da aka yi masa a Indinusiiya in da dubban mutane suka halarci taron har asuba suna tsaye suna saurraren karatunsa. Da irin wadan nan da dama acikin Duniya.

Wafatinsa

Malamin ya kamu da ciwon sikari in da  ya yi ta fama da jinya,wanda daga karshe likitocin misra suka ba shi shawara da ya tafi London don a yi masa magani . bayan ya je can ma abu ya gagara sai ya ce ma dansa wanda suka je tare su dawo gida domin yana jin cewa dai da wuya ya warke. Bayan dawowarsu kuwa ba da jimawa sai Allah ya yi wa malamin cikawa a 30-11-1988 in da rasuwarsa ta girgiza Al’ummar musulmin duniya.

  Wannan shi ne takaitaccen tarihin rayuwar malamin. Da fatan Allah ya kara haskaka kabaribsa da rahama amin.

Husain Ridha'iyan

An haifi Hausain  a garin Tehran babban birnin Iran a shekara ta  1334. sauraren

Karatunsa daga shehin malamin nan wato Abdulbasit ya sanya masa so da kaunar karatun Qur'ani. Musamman karataunsa na surar takwir da hashr, daga nan ne fa ya dukufa wajen karatun Qur'ani tare da kaancewar iyayensa masu son addini ya taimaka masa da ba shi kwarin guiwa wajen al'amarin. Sanannan tun yana dan shekara 12 ya fara koyon muryar malamin har yazuwa yanzu ma yana cigaba da kwai-kwayon muryar ta Abdulbasit, duk da cewa yanzu shima yana da nashi salon karatun.

 Ya samu lambar yabo wajen gasar karatu na duniya a wurare  dama .

Malamin a shekara ta 1360 ya yi aure wanda sakamakon haka ne ya samu yara guda biyu, wanda na farkon shima ya bi hanyar babansa, a yanzu shima yana daya daga cikin makaranta a kasar.

 Malamin bayan karatun kur'ani da yake gabatarwa a wurare da yawa, yakan koyar da fannoni dama na ilimin kur'ani.

 Malamin ya je wurare da dama a cikin duniya sakamakon gayyata da ake yi masa.

Kamar yadda yake cewa lokacin da ya je korea ta kudu da Canada mutane sun nuna shaukinsu da kaunarsu da karatun kur'ani.

  Shehin malamin  an fara sa karatunsa a cikin gidan talabijin na kasa wanda har yanzu kuma a gidajen talabijin na kasar da dama ana sa karatunsa.

    Malamin bayan karatu da Allah ya hore masa ya kware kuma a wajen kiran salla kasancewar muryar da Allah ya ba shi.

 Malamin ya halarci fagen fama yayin yakin Iran da Iraq kuma ya taka rawar gani sosai a wajen yakin.

 Wannan shi ne takaitaccen tarihin rayuwar malamin. Da fatan Allah madaukaki ya kara yawaita mana irinsu amin.