') //-->
Wanda duk ya yi bitar ruwayoyi da hadisan da suka zo ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) ya kuma karanci tarihin rayuwarsu da alakarsu da Littafin Allah, ba zai sami muhimmanci da kulan da Ahlulbaiti (a.s) suke bayarwa fiye da wanda suke bai wa Littafin Allah, Mai Girma da Daukaka ba, ko a yanayin rayuwarsu ko cikin abin da suka ruwaito da maganganunsu ko cikin abin da suka yi wasiyya ko suka tarbiyyantar ko suka fuskantar da mabiyansu da almajiransu da daukacin 'ya'yan musulmi.
Imam Ja'afar Sadik (a.s.) ya ruwaito daga kakansa Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Ya ku mutane, lalle kuna gidan dako ne, kuma kuna kan tafiya, tafiyar kuwa tana sauri da ku, kun ko ga dare da yini da rana da wata suna tsufar da kowane sabon abu, suna kuwa kusanto da kowane manisanci suna kawo kowane abin alkawartawa, to ku tanadi shiri wa tafiyar nan mai tsawo".
Ya ce: sai Mikdad bn Aswad ya mike, ya ce: Ya Manzon Allah! Mene ne gidan dako?, sai yace masa:
"Gidan isarwa da yankewa, to idan fitinu kamar yankin dare mai duhu sun rikitar da al'amurra a kanku, na hore ku da Alkur'ani, domin shi, mai ceto ne abin karbawa ceto, mai jayayya abin gaskatawa. Duk wanda ya sanya shi gabansa zai ja-gorance shi zuwa aljanna, wanda ko ya sanya shi a bayansa zai iza shi zuwa wuta. Shi kuwa ja-gora ne mai shiryarwa zuwa mafi alherin
hanya. Kuma shi littafi ne wanda a cikinsa akwai rarrabewa da bayani da riba (ko karuwa) shi ne rarrabewa kuma ba kakaci ba ne, yana da baya da ciki. Bayansa hukumci ne, cikinsa kuwa ilmi ne, bayan nasa gwanin kyau ne da shi, cikin nasa kuwa zurfi ne da shi. Yana da taurari, bisa taurarinsa ma akwai wasu taurarin. Ba a iya kididdigar ababen ban mamakinsa, abubuwan ban sha'awarsa kuma ba sa tsufa. Akwai fitilun shiriya da hikima cikinsa, kuma mai shiryarwa ne zuwa ga masaniya ga wanda ya san sifa. To mai yawo ya yi yawo (cikin Alkur'ani) da ganinsa, kuma dubinsa ya riski sifar domin ya tsira daga halaka ya kuma kubuta daga tsanani. Domin kuwa tunani rayuwar zuciya mai gani ne, kamar yadda mai tafiya cikin duhu yake haskaka hanya da haske. To na hore ku da kubuta mai kyau da karancin dako[1] ".
Imam Sadik (a.s.) yana cewa:
"Mahaddacin Alkur'ani, mai aiki da shi yana tare da Mala'iku Marubuta, Masu daraja, Masu da'a ga Allah[2] ".
Imam Aliyu bn Husain (a.s.) yana cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Wanda Allah Ya ba shi Alkur'ani, sai ya ga cewa an bai wa wani mutum fiye da abin da aka ba shi, to hakika ya rena babban abu, ya kuma girmama karami[3] ".
Ya zo kuma daga wajen Imam Muhammadu Bakir (a.s.) cewa ya ce Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Ya ku jama'a makarata Alkur'ani! Ku ji tsoron Allah Mai Girma da Daukaka cikin abin da Ya dora muku na LittafinSa domin ni abin tambaye ne, ku ma abin tambaya ne. Ni za a tambaye ni kan isar da sako, ku kuma za a tambaye ku ne kan abin da aka dora muku na Littafin Allah da Sunnata[4] ".
Sannan kuma Imam Sadik (a.s.) yana cewa:
"Ya kamata mumini kada ya mutu har sai ya koyi Alkur'ani, ko kuwa ya
zama cikin koyonsa[5]
".
Imam Sadik (a.s.) kuma yana cewa:
"Alkur'ani alkawarin Allah ne da bayinSa, to hakika ya kamaci mutum musulmi ya yi dubi cikin alkawarinsa, ya kuma karanta ayoyi hamsin daga ciki a kullum[6] ".
Imam Sadik din dai yana cewa:
"Abubuwa uku za su kai kuka zuwa ga Allah Madau-kakin Sarki: masallacin da aka kaurace masa ba a salla a cikinsa, malamin da ke tsakanin jahilai da kuma Alkur'anin da aka rataye shi kura tana hawa kansa don ba a karanta shi[7] ".
Imam Sadik (a.s.) yana cewa:
"Lalle Alkur'ani rayayye ne ba matacce ba, kuma yana gudana kamar yadda dare da yini suke gudana, kuma kamar yadda rana da wata suke tafiya. Yana kuma tafe ne kan na karshenmu, kamar yadda yake tafe a kan na farkonmu".
Amirul Muminina (a.s) ya ce:
"Sannan Allah Ya saukar masa da Littafi, haske ne fitilunsa, ba su mutuwa, fitila ce da haskenta ba ya bishewa, kogi ne da ba a risko zurfinsa; tafarki ne wanda salonsa ba ya bacewa; haske ne wanda ba ya yin duhu, mai rarrabewa wanda karfin hujjarsa ba ya raguwa, bayani ne wanda ba a rusa ginshikinsa, waraka ce wadda ba a tsoron cuta a tare da ita, daukaka ce wacce ba a rinjayar masu taimakon ta; gaskiya ce wadda ba a tabar da masu taya ta. Shi ne taskar imani, kuma tsakiyar shi, shi ne mabubbugan ilmi da kogunan shi; shi ne koraman adalci da tabkunan shi; shi ne murhun Musulunci da ginin shi; shi ne kwazazzabon gaskiya da mafakarta; shi tekun ne da masu kwarfa ba sa iya kwarfe shi; idanuwar ruwa ne masu kwarfa ba su iya karar da shi; wuraren sha ne masu taho masa ba sa kafar da shi; masaukai ne da matafiya ba sa bacewa da hanyarsa, alamu ne wadanda matafiya ba sa makance masa; tsaunuka ne da wanda ya nufe su ba zai wuce su ba. Allah Ya sanya shi mai kashe kishin ruwan malamai; bazaar (mai rayawa) ga zukatan fukaha'u (masana ilmin fikihu); gwadabe mai tara hanyoyin mutanen kwarai; waraka wadda babu wata cuta bayanta; hasken da babu wani duhu tare da shi; igiya ce mai karfi; mafaka ce wadda kololuwarta karerriya ce; daukaka ga wanda ya jibince shi; aminci ga wanda ya shige shi; shiriya ga wanda ya yi koyi da shi; uzuri ga wanda ya yi riko da shi; hujja ga wanda ya yi magana da shi; shaida ga wanda ya yi amfani da shi wajen jayayya; nasara ga wanda ya kafa hujja da shi; mai daukar duk wanda dauke shi; abin hawa ga wanda ya yi aiki da shi; alama (aya) ce ga wanda ya sa lura; garkuwa ga wanda ya nemi kariya da shi; ilmi ga mai kiyayewa; abin fadi ga mai ruwaya; kuma hukumci ne ga mai hukumtawa[8] ".
Haka nan dai muke fahimtar kimar Alkur'ani da darajarsa a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da kuma tafarkinsu. Ita ce kuwa kima ta hakika wacce Alkur'ani ya yi furuci da ita, wahayi kuma ya siffanta shi da ita
"Hakika wannan Alkur'ani yana shiryarwa zuwa hanya da tafi daidai". (Surar Isra'i, 17: 9)
Alkur'ani shi ne hanyar rayuwar al'umma, mabubbu-gar ilmi da shiriya, taskar ma'arifa da wayewa, tafarkin fahimta da tunani, ma'aunin ci gaba da halaye na kwarai, shi ne doka ta ilmi wajen tsara rayuwar dan'Adamtaka, kuma shi ne ma'aji mai tattara al'adun rayuwar mutumtaka da dokokinta.
A cikin abin da ya gabata, mun ambaci yadda tafar-kin Ahlulbaiti (a.s) da mazhabarsu suka tabbatar mana da cewa Littafin Allah madawwami ne, ba jirkitarwar da ta same shi, shi ne kuma kundin dokokin Ubangiji dawwa-mammu, shi ne tushen shari'a, shi ne ma'auni mai hukumci kan ingancin ruwayoyi da hadisai, shi ne kuma hujja wajen tabbatar da kuskure ko dacewar kowane abu. Hadisi ya zo daga Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa:
"Idan wani hadisi ya zo muku daga gare ni, ku gwada shi da Littafin Allah, abin da ya dace da shi ku karba, abin da ya saba masa kuwa ku yi jifa da shi[9] ".
Bayan tabbatar wannan da soke dukkan raunanan maganganu na
barna, za mu gane cewa tafarkin musulun-ci na asali ya nuna wa musulmi da
ma'abuta ilmi da sani hanyar fahimtar Alkur'ani da tafsirinsa da mu'amala da
nassin Alkur'ani, ya kuma kayyade mana hanyar. Wannan batu na fahimtar
Alkur'ani da tafsirinsa da kuma tawilinsa, batu ne mai tushe, wanda kubutar
tunani a Musulunce da ingancin akida da shari'a da masaniyar Musulunci duk sun
dogara a kansa ne. Domin duk wani karkata ko takaita ko takaitawa wajen
fahimtar Alkur'ani da binciken taskar shari'a da akida da fitar da
hukumce-hukumcensa da riskar iliminsa da dokokinsa na zamanta-kewar al'umma da
na siyasa, tattalin arziki, tarbiyya, zartar da hukumci da dai sauransu, duk
suna kai wa ga karkata da rarrabar musulmi, da kuma yin tawaye ga tsarin asalin
addinin Musulunci da tsabtarsa.
Wajibi ne a farkon magana kan wannan batu mai tushe da muhimmanci, mu rarrabe
tsakanin tafsiri da tawili.
Tafsiri dai a wajen malaman lugga, shi ne: "Gano ma'anar lafazi da kuma fito da ita[10]".
Tawili kuwa shi ne: "Mai da dayan ma'anoni biyu da lafazi ke iya dauka ya zuwa dacewa da zahirin al'amari[11] ".
Ahmad Ridha ya ce: "Kalmar tafsiri an dauko ta ne daga kalmar "fassara" wacce aka ciro ta daga "assifru", shi ne kuwa fitarwa da bayyanarwa. Ana cewa "asfaras subhu" wato asubahi ya bayyana, ana kuma cewa "asfaratil mar'atu an wajhiha" wato mace ta fito da fuskarta, an yi amfani da kalmar "asfara" wajen fitowa.
Ko kuma ace kalmar tafsiri an dauko ta ne daga "fasara-yafsiru" kamar "daraba-yadribu" ko "nasara-yansuru" "fasara-yafsiru-fasran. Fasru tana nufin bayyana da fito da rufaffen abu. Mutum ya kan ce "fasartu" ga abu idan ya bayyana shi[12]".
Shaikh Tabrisi (Allah Ya daukaki mukaminsa) ya fadi cikin gabatarwar tafsirinsa mai daraja wato Majma'ul Bayan fi Tafsiril Kur'an cewa:
"Tafsiri shi ne fito da manufar lafazi mai rikitarwa, tawili kuwa shi ne maidowa da dayan ma'anoni biyu da lafazi ke iya dauka, ya zuwa ga dacewa da zahiri. Tafsiri shi ne bayani".
Abul Abbas Mubarrid ya ce: "Tafsiri da tawili da ma'ana duk daya suke. An ce 'fasru' shi ne fitowa da rufaffe, tawili kuwa shi ne karshen abu da makomarsa, da abin da al'amarinsa yake komawa gare shi...[13] ".
Hanyar Da Ake Bi Wajen Tafsirin Alkur'ani:
Yayin da tafsiri yake bayanin ma'anar kalmomin Alkur'ani da jumlolinsu da kuma fito da ma'anoni a sarari, sannan kuma sashen kalmomin Alkur'ani da jumlolinsa ana iya fassara su da tafsirin zahiri wanda mai yiyuwa ne ya kasance ya yi nisa da manufa ta hakika ga Alkur'ani, shi kuwa tawili shi ne aikin fito da ma'anar da ake nufi, hakan kuwa ta hanyar mayar da ma'anoni da ke ajiye cikin ayar - bayan jujjuya su tsakanin fuskoki biyu ko fiye[14] - ya zuwa ga makomarsa. Burin da muke so mu cimma a nan shi ne daidaiton tawili da tafsiri a matsayin sakamako. Shi ne kuwa fayyace ma'anonin Alkur'ani da bayanin abin da Allah Madaukakin Sarki Yake nufin bayaninsa ga bayinSa.
Duk wanda ya yi bitar littattafan tafsiri da tafarkin masu tafsiri, zai samu cewa akwai tazara mai fadi da ramuka masu hadari, wadanda sashin masu fassara suka fada, sai suka karkace daga manufar tafsiri domin hanyoyin tafsirin wadanda suka bi da bayanin tawilin da suka yi wa ayoyin Alkur'ani. Wani lokacin a samu sun dogara da raunanan ruwayoyi da aka sossoka, wani loton kuwa a samu sun bi son zuciya sai su tankwarar da Alkur'ani zuwa ra'ayoyin kungiyoyin da suke bi, da kuma son zuciyarsu kebantacciya. Sai ka ga suna kokarin sa ayoyin Alkur'ani su dace da abubuwan da suka auku a tarihi kuma danganta su ga wadansu daidai-kun mutanen da Alkur'anin ba su yake nufi ba. Kai sun ma nemi su sa ayoyin Alkur'ani su dace da girmama ra'ayoyinsu da karkatar su kebantattu.
Misalin karkata cikin tawili shi ne fuskartar da ayoyin Alkur'ani da sashen masu falsafa da ilimin kalami suka yi bayan sun riga sun yi imani da tunani da mazhabobin kalami da falsafa sannan suka tankwara ma'anonin ayoyin zuwa wadannan mazhabobin.
Misali kuma shi ne cewa akwai abin da sashen marubuta da masu tafsiri ke yi na fuskantar da ayoyin Alkur'ani domin su dace da nazarce-nazarcensu na ilimin kimiyya da tunaninsu na tattalin arziki da zamantakewa da siyasa wadanda marubuta da amsu nazari suka bijiro da su suka kuma yadu a zamanin wadannan masu fassara. Suna bin fadar masu nazarce-nazarcen nan ba tare da akwai wata dangantaka ta hakika ko dacewa ta gaskiya ba. Haka nan muke samun yadda ake murda ayoyi zuwa son zuciya, ko ka ga mai tafsiri ya yarda da wasu ra'ayoyi sannan daga baya ya karkata ayoyin Alkur'ani zuwa ra'ayoyi da halaye da dama, tun da can da kuma ma yanzu.
Hakika masu tafsiri da yawa sun fada cikin wannan kuskuren, kuma daga mazhabobi daban-daban, na Ahlussunna ne ko na Shi'a ko kuma waninsu. Bayan sun yi wannan kuskuren sai su dora kawo hujjoji da dalilai don kare wadannan ra'ayoyi nasu.
Idan muka koma ga tafarkin Musulunci na asali wajen tafsiri za mu ga cewa ya yi watsi da wannan tafarki da muka fadi a baya da kuma tabbatar da asasai ingantattu na tafsiri.
Don kuwa tafsiri kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fadi, kuma tafarkin Ahlulbaiti (a.s) da duk wanda ya bi tafarkinsu ba tare da karkata ba da malaman tafsiri masu lizimta, yana da asasai da ginshikansa wadanda suke shiryar da mai tafsiri da mai bincike zuwa dacewa mayalwaciya.
Bari mu kawo bayanin da ya zo daga Manzon Allah (s.a.w.a.) da Imamai Masu shiryarwa (a.s.) da malaman al'umma kan batun sanya ginshikai wadanda ba su da wata karkata, domin tafsiri da tabbatar da ma'aunai da kuma dokoki masu kiyaye wannan ilmi mai daraja, domin shi ilmi ya ba da gudummawarsa tare da cikakkiyar kula da kubuta daga karkatarwa. Kuma domin wannan ilmi ya wadatar da duniyar dan'Adamtaka da ma'anoni da tunani da fahimce-fahimcen da za a iya riska da kuma hukumce-hukumce, ba tare da wata tawaya ko kirdado ko jidali ko bin ra'ayi ko kuma tankwara tafsirin domin ya bi son zuciya ba.
Allama Dabrisi ya ambata cewa: "Ya inganta daga Annabi (s.a.w.a), ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) cewa: "Tafsirin Alkur'ani ba ya halatta sai da asari (wato hadisi) ingantacce da kuma nassi bayyananne[15] ".
Lalle Ahlulbaiti (a.s) sun kasance suna bin wannan hanyar, suna kuma watsi da yi wa Alkur'ani tafsirin da ya yi nisa daga wadannan ginshikai guda biyu, wato:
Don haka ne ya wajaba cewa dole tafsirin ya lizimci wadannan ginshikai biyu, cikakkiyar lizimta. Sannan kuma wajibi ne kada mu gafala kan cewa hankali yana da fagensa na asasi da ja-goranci wajen fahimtar Alkur'ani da tafsirin ma'anoninsa da fuskantar da zahirinsa, bisa sharadin cewa shi hankali zai lizimci iyakokin Littafin Allah da Sunnan Ma'aiki (s.a.w.a.), ba zai kuma sabawa tsarinsu ba. Hakika Manzo Mai girma ya ba wa hankali fage fitacce wajen tafsirin Alkur'ani, inda ya ce:
"Alkur'ani mai saukin korawa ne, mai fuskoki da yawa; to ku dauki fassarar da ta fi kyau[16] ".
Har ila yau ya ce:
"Ku bayyana Alkur'ani kuma ku nemi kebantattun abubuwansa[17] ".
Alkur'ani mai girma ya bayyana irin rawar da hankali zai taka cikin tafsiri, ya kuma yaba wa ma'abota hankula masu fitar da hukumce-hukumce daga Alkur'ani, yayin da yake cewa:
"Da masu istinbadinsa daga cikinsu sun san shi". (Surar Nisa'i, 4: 83)
Alkur'ani ya yi suka ga wadanda suka bar tunani da lurar hankali cikin ayoyin Alkur'ani mai girma, da gano ma'anoninsa da abubuwa da ya kunsa, da cewa:
"Shin ba su lura da Alkur'ani ne, ko kuwa da kemare ne bisa zukata" (Surar Muhammadu, 47:24)
Daga nan za mu san cewa a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) tafsiri yana dogara ne da asasai uku:
Haka nan muke samun cewa tafsiri yana da asasai da dokoki, kuma abin da ya tafo na tafsirai wanda za a cewa ra'ayin mutum ya shige shi, ko kuwa an dauki wasu nazarce-nazarcen ilmi wadanda mai tafsirin ya yi zamani da su, ko ra'ayoyin falsafa da ilmin akida, ko abin da aka danganta shi da ruwayoyi raunana ko ma wadanda sanadinsu yashashshe ne, ko kuwa masu karo da ayoyin Alkur'anin da suke a sarari ko kuma sunna tabbatatta, ko kuwa tafsirin da mai tafsirin ya daidaita shi da ra'ayinsa da karkatarsa da kuma sauran irin wadannan, dukkansu ababan yarfarwa ne a tafarkin Ahlulbaiti (a.s) da kuma malamai da masu tafsiri wadanda suka bi shiriyarsu. Sau da yawa kuma ana samun cikin tafsiran musulmi, sunna da shi'a, ra'ayoyi da tafsirai wadanda ba su lizimci wannan hanyar ta Musulunci ba, wadanda kuma ba su bayyana ruhin Alkur'ani.
Don haka, ba wa irin wadannan tafsiran kima ba ya inganta, ba za mu kuma rike su mu yi aiki da su ba, sai dai wanda ya tabbatar wa kansa da ingancinsu.
Mai tafsiri kuwa ko wane ne shi, Alkur'ani hujja ce akansa, ba shi ne hujja a kansa ba. Kuma ba zai zamo hujja kan musulmi ba face da gwargwadon abin da ya dace da katari da abin da ya gano na hakika kawai.
Hakika hani ya zo daga wajen Imamai (a.s.) kan magana ba da wani ilimi ko hujja ba. An ruwaito Imam Bakir (a.s.) yana cewa:
"Abin da kuka san shi to ku fade shi, abin da kuwa ba ku sani ba to ku ce "Allah Shi Ya fi sani". Lalle mutum yana tuzgo aya daga Alkur'ani ya fadi cikin tuzgowar da ya yi, faduwar mai nisan fiye da tsakanin sama da kasa[18] ".
Imam Sadik (a.s.) ya ce:
"Ko wane abu ana komar da shi zuwa ga Littafin Allah da Sunna[19] ".
[1] Usul Kafi na Shaikh Kulayni juzu'i na 2 shafi na 598.
[2] Kamar na sama, shafi na 603.
[3] Kamar na sama, shafi na 605
[4] Kamar na sama, shafi na 606
[5] Usul Kafi na Shaikh Kulayni juzu'i na 2 shafi na 607.
[6] Kamar na sama, shafi na 609.
[7] Kamar na sama, shafi na 613.
[8] Nahjul Balagah, huduba ta 198.
[9] Majma'ul Bayan na Dabrisi, Mukaddima, juzu'i na 1, shafi na 13.
[10] Majma'ul Bahrain na Duraihi, kalmar fassara.
[11] Majma'ul Bayan na Dabrisi, Mukaddima, juzu'i na 1, shafi na 13.
[12] Ahmad Ridha cikin Mukaddimar Majma'ul Bayan, juzu'i na 1, shafi na 13.
[13] Gabatarwar Majma'ul Bayan juzu'i na 1 shafi na 13.
[14] Daga cikin misalin tawili, shi ne tawilin da ake yi wa wannan aya: "KujerarSa ta yalwaci sammai da kasa", anan ana yi wa kujera tawili da ilmi da mulki…da dai sauransu, ba wai kujera wacce ake zama a kanta ba kamar yadda aka sani.
[15] Gabatarwar Majma'ul Bayan na Tabrisi, juzu'i na 1, shafi na 13.
[16] Kamar na sama.
[17] Kamar na sama.
[18] Sahihul Kafi na Bahbudi, juzu'i na 1, shafi na 5.
[19] Kamar na sama, shafi na 11.